Ku Taimake Wasu Su Yi Zaman Da Ya Cancanci Bautar Jehovah
“Ba mu fasa yi muku addu’a ba, muna roƙo . . . ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari.”—KOLOSIYAWA 1:9, 10.
1, 2. Menene musamman zai kawo farin ciki da gamsuwa?
“MUNA zama a wata gona a wani ayari. Ta wajen rayuwa mai sauƙi, muna da ƙarin lokaci mu yi wa mutane bishara. Mun samu albarkar taimakon mutane da yawa su keɓe rayuwarsu ga Jehovah.”—Ma’aurata, masu hidima ta cikakken lokaci a Afirka ta Kudu.
2 Ba za ka yarda da cewa taimakon wasu yana kawo farin ciki ba? Wasu ko yaushe suna ƙoƙari su taimaki masu ciwo, waɗanda aka hana su abubuwa, ko kuma sun kaɗaita—suna samun gamsuwa a yin hakan. Kiristoci na gaskiya suna da tabbacin cewa gaya wa wasu game da Jehovah Allah da Yesu Kristi shi ne taimako mafi girma da za su bayar. Wannan ne kaɗai zai sa wasu su amince da fansa da Yesu ya yi, su gina dangantaka mai kyau da Allah, su kuma shiga layin samun rai madawwami.—Ayyukan Manzanni 3:19-21; 13:48.
3. Ga wane irin taimako ne muke bukatar mu mai da hankali?
3 Amma, me za a ce game da taimaka wa waɗanda sun riga suna bauta wa Allah, da suke bin “Hanya”? (Ayyukan Manzanni 19:9) Marmarinka game da su babu shakka yana da girma, amma mai yiwuwa ba ka gan yadda za ka ƙara ko ci gaba da ba da taimako ba. Ko kuma yanayinka mai yiwuwa yana rage taimako da za ka ba su, da haka yana rage gamsuwa da za ka samu. (Ayyukan Manzanni 20:35) Game da fannoni biyun nan, za mu iya koyo daga littafin Kolosiyawa.
4. (a) A waɗanne yanayi ne Bulus ya rubuta wa Kolosiyawa? (b) Ta yaya ya shafe Abafaras?
4 Lokacin da manzo Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci a Kolosi, yana Roma inda aka tsare shi cikin gida, amma mutane za su iya ziyartarsa. Yadda za ka yi tsammani, Bulus ya yi amfani da ɗan ’yanci da yake da shi ya yi wa’azi game da Mulkin Allah. (Ayyukan Manzanni 28:16-31) Kiristoci masu bi za su iya ziyartar Bulus, wataƙila an tsare wasu ma tare da shi a wasu lokatai. (Kolosiyawa 1:7, 8; 4:10) Wani Abafaras ne mai bishara da himma daga birnin Kolosi a Firijiya, a ƙasar gabas da yake ƙasar Afisus a Asiya Ƙarama (Turkiya ta zamani). An yi amfani da Abafaras wajen kafa ikilisiya a Kolosi, ya yi aiki tuƙuru don ikilisiyoyi da ke kusa da Lawudikiya da na Hirafolis. (Kolosiyawa 4:12, 13) Me ya sa Abafaras ya yi tafiya zuwa wajen Bulus a Roma, me za mu koya daga amsar da Bulus ya bayar?
Taimako Mai Amfani ga Kolosiyawa
5. Me ya sa Bulus ya rubuta abin da ya rubuta wa Kolosiyawa?
5 Domin ya yi magana da Bulus game da yanayi cikin ikilisiyar Kolosi, Abafaras ya yi tafiya mai wuya zuwa Roma. Ya ba da labarin bangaskiya, ƙauna, da ƙoƙarce-ƙoƙarcen wa’azin bishara na waɗannan Kiristoci. (Kolosiyawa 1:4-8) Duk da haka, dole ya faɗa damuwarsa game da munanan rinjaya da ke so ya ɓata ruhaniya ta Kolosiyawa. Bulus ya rubuta wasiƙa da aka hure da ta ƙaryata wasu ra’ayoyi da malaman ƙarya ke yaɗawa. Ya mai da hankali musamman a kan matsayi da ya kamata Yesu Kristi ya ɗauka.a Taimakonsa ya tsaya ne a nanata muhimmiyar gaskiyar Littafi Mai Tsarki kawai? Ta yaya zai taimaki Kolosiyawa, kuma waɗanne darussa za mu koya game da taimaka wa wasu?
6. Menene Bulus ya nanata cikin wasiƙarsa ga Kolosiyawa?
6 Da farko a wasiƙarsa, Bulus ya ba da fahimi na irin taimako da wataƙila ba za mu lura da shi ba. Hanyar ba da taimako mai amfani ne daga nesa, Bulus da Abafaras suna nisa da Kolosi. Bulus ya tabbatar: “Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa’ad da muke muku addu’a.” Hakika, waɗannan addu’o’i na musamman ne don Kiristoci a Kolosi. Bulus ya daɗa: “Shi ya sa tun ran da muka ji labarin, ba mu fasa yi muku addu’a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu.”—Kolosiyawa 1:3, 9.
7, 8. Addu’o’i ta kanmu da ta ikilisiya sau da yawa tana ƙunsan wane al’amari ne?
7 Mun san cewa Jehovah mai “amsa addu’o’i” ne, saboda haka za mu gaskata cewa a shirye yake ya amsa addu’o’i da muke yi daidai da nufinsa. (Zabura 65:2; 86:6; Karin Magana 15:8, 29; 1 Yahaya 5:14) Amma, in ya zo ga yi wa wasu addu’a, yaya addu’o’inmu suke?
8 Sau da yawa za mu iya tunani mu yi addu’a game da ‘ ’yan’uwanmu a duniya duka.’ (1 Bitrus 5:9) Ko kuma mu yi wa Jehovah addu’a game da Kiristoci da kuma wasu a yanki inda bala’i ko tsautsayi ya faɗa musu. Lokacin da almajirai na ƙarni na farko da suke wani waje suka ji game da yunwa a Yahudiya, sun yi addu’o’i da yawa domin ’yan’uwansu kafin ma su aika musu kayan agaji. (Ayyukan Manzanni 11:27-30) A kwanakinmu, sau da yawa ana addu’o’i game da ’yan’uwanci duka ko game da rukunin ’yan’uwa a taron Kirista, inda mutane da yawa suna bukatar fahimta don su iya cewa “Amin.”—1 Korantiyawa 14:16.
Ka Yi Addu’a Game da Takamaiman Abu
9, 10. (a) Waɗanne misalai suka nuna cewa yi wa wasu takamaiman mutane addu’a daidai ne? (b) Ta yaya Bulus ya zama takamaiman wanda za a yi masa addu’a?
9 Amma, Littafi Mai Tsarki ya yi mana tanadin misalan takamaiman addu’o’i da aka yi game da wasu, an ambata sunan mutanen. Ka yi la’akari da furci da Yesu ya yi da ke rubuce a Luka 22:31, 32. Manzanni 11 masu aminci ne suka kewaye shi. Dukansu za su bukaci taimakon Allah a lokatai masu wuya da ke gaba, Yesu ya yi musu addu’a. (Yahaya 17:9-14) Har ila, Yesu ya mai da hankali ga Bitrus, ya yi addu’a na musamman game da wannan almajiri. Wasu misalai: Elisha ya yi addu’a Allah ya taimaki wani mutum musamman, bawansa. (2 Sarakuna 6:15-17) Manzo Yahaya ya yi addu’a Gayus ya yi zaman lafiya a jiki da kuma ruhaniya. (3 Yahaya 1, 2) A wasu addu’o’i kuma an mai da hankali ga wani rukuni takamaimai.—Ayuba 42:7, 8; Luka 6:28; Ayyukan Manzanni 7:60; 1 Timoti 2:1, 2.
10 Wasiƙu da Bulus ya rubuta ya bayyana batun takamanmun addu’o’i. Ya ce a yi masa addu’a ko kuma dominsa da abokan tarayyarsa. Kolosiyawa 4:2, 3 suka ce: “Ku lazamci yin addu’a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah, mu ma ku yi mana addu’a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanar da asirin Almasihu, wanda saboda shi ne nake a ɗaure.” Ka bincika waɗannan misalan su ma: Romawa 15:30; 1 Tasalonikawa 5:25; 2 Tasalonikawa 3:1; Ibraniyawa 13:18.
11. Lokacin da yake Roma, domin su wanene Abafaras ya yi addu’a?
11 Wannan haka yake game da abokin tarayyar Bulus a Roma. “Abafaras wanda ke ɗaya daga cikinku, . . . yana gaishe ku, kullum yana yi muku addu’a da himma.” (Kolosiyawa 4:12) Kalmar nan “himma” tana iya nufin “mazakuta,” yadda mai wasan motsa jiki yake yi a wasanni na dā. Abafaras yana yin addu’a da himma don kawai game da masu bi na duniya duka ko kuma game da masu bauta ta gaskiya a dukan Asiya Ƙarama ce? Bulus ya nuna cewa Abafaras yana addu’a musamman game da waɗanda suke Kolosi. Abafaras ya san yanayinsu. Ba mu san sunan dukansu ba, ba mu kuma san matsaloli da suke fuskanta ba, amma mu ƙaga abin da yake damunsu. Wataƙila Linas saurayi yana fama da rinjayar falsafa, kuma mai yiwuwa Rufas yana bukatar ƙarfi ya tsayayya wa ayyukansa na dā na addinin Yahudawa domin kada su rinjayi hankalinsa. Da yake mijinta ba mai bi ba ne, mai yiwuwa Barsisa tana bukatar jimiri da hikima ta yi renon yaranta cikin Ubangiji, kuma wataƙila Asinkiritas wanda yake ciwon ajali, na bukatar ƙarin ta’aziyya? Hakika, Abafaras ya san waɗanda suke ikilisiyarsa, ya yi addu’a da himma game da su domin shi da Bulus suna so irin waɗannan da suka ba da kansu su yi zaman da ya cancanci bautar Jehovah.
12. Ta yaya za mu iya ambatar takamanmun abubuwa cikin addu’o’i na kanmu?
12 Ka ga tafarki dominmu—hanyar da za mu taimake wasu? Yadda aka lura, addu’o’i ga jama’a a taron Kirista sau da yawa ba a roƙon takamaiman abu, domin jama’an sun bambanta. Amma addu’o’i na kanmu ko na iyalinmu sukan zama takamaimai. A wasu lokatai muna iya gaya wa Allah ya ja-goranci kuma ya albarkaci dukan masu kula masu ziyara ko makiyaya na ruhaniya, shin wasu lokatai bai kamata mu ambata suna ba? Alal misali, me ya sa ba za ka ambata cikin addu’a sunan mai kula da da’ira da ke ziyarar ikilisiyarku ko mai tafiyar da nazari na Nazarin Littafi na Ikilisiya taku ba? Filibiyawa 2:25-28 da 1 Timoti 5:23 sun nuna yadda Bulus ya ambaci Timoti da Abafaroditas da ya nuna damuwa game da lafiyarsu. Za mu iya nuna irin damuwar nan ga masu rashin lafiya da muka san sunansu?
13. Wane irin yanayi ne sun dace mu saka cikin addu’o’i na kanmu?
13 Hakika, dole mu guje sa baki a batutuwan wasu, amma daidai ne addu’o’inmu su nuna ƙauna ta gaske ga waɗanda muka sani kuma mun damu da su. (1 Timoti 5:13; 1 Bitrus 4:15) Mai yiwuwa wani ɗan’uwa ya yi rashin aikinsa, ga shi ba mu iya nema masa wani ba. Har ila yau, za mu iya ambata sunansa mu nace kan matsalarsa cikin addu’o’inmu. (Zabura 37:25; Karin Magana 10:3) Shin mun san wata ’yar’uwa da ta tsufa, ba ta da miji da kuma yara domin ta ƙuduri aniyyar ta auri “mai bin Ubangiji”? (1 Korantiyawa 7:39) A cikin addu’o’inku, me ya sa ba za ku gaya wa Jehovah ya albarkace ta ya taimake ta ta ci gaba da aminci cikin hidimarta ba? A wani misali, mai yiwuwa dattawa biyu sun yi wa ɗan’uwa da ya yi kuskure gargaɗi. Me ya sa kowanne cikinsu ba zai ambata sunan ɗan’uwan ba a wasu lokatai cikin addu’arsa?
14. Ta yaya takamanman addu’o’i ya shafi taimakon wasu?
14 Akwai yanayi da yawa da za ka ambata cikin addu’a na kanka mutane da ka sani suna bukatar taimakon Jehovah, ta’aziyya, hikima, da ruhu mai tsarki, ko amfani da za su kawo. Saboda nisan wuri ko wasu yanayi, ba za ka san abin da za ka aika ko kuma taimako da za ka bayar ba. Amma kada ka manta ka yi wa ’yan’uwanka maza da mata addu’a. Ka san cewa suna son su yi zaman da ya cancanci bautar Jehovah, duk da haka mai yiwuwa da gaske suna bukatar taimako don su ci gaba da yin hakan da daɗewa. Taimako na musamman shi ne addu’o’inka.—Zabura 18:2; 20:1, 2; 34:15; 46:1; 121:1-3.
Ka Yi Ƙoƙari Ka Ƙarfafa Wasu
15. Me ya sa ya kamata mu kasance da marmari ga sashe na ƙarshe na Kolosiyawa?
15 Addu’a da aka yi da himma, takamaimiya ba ita ce hanyar taimakon wasu kaɗai ba, musamman waɗanda suke kusa da kai da waɗanda ka ke ƙauna. Littafin Kolosiyawa ya bayyana wannan sarai. Masana da yawa sun ce bayan da Bulus ya yi tanadin ja-gora na addini da gargaɗi masu amfani, ya daɗa gaisuwa na kansa. (Kolosiyawa 4:7-18) Akasarin haka, mun gane cewa wannan sashen littafi na ƙarshe yana ɗauke da gargaɗi da ya kamata mu mai da hankali a kai, akwai ƙarin abin da za a koya daga wannan sashen.
16, 17. Me za mu ce game da ’yan’uwa da aka ambata su a Kolosiyawa 4:10, 11?
16 Bulus ya rubuta: “Aristarkus, abokin ɗaurina, na gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi. Yasuwa kuma da ake kira Yustus na gaishe ku. Wato cikin abokan aikina ga Mulkin Allah waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya.”—Kolosiyawa 4:10, 11.
17 Bulus a wajen ya nuna wasu ’yan’uwa da sun cancanta a lura da su musamman. Ya ce suna cikin waɗanda aka yi musu kaciya, daga cikin Yahudawa. Akwai Yahudawa da yawa da aka yi musu kaciya a Roma, wasu yanzu Kiristoci ne. Duk da haka, waɗanda Bulus ya ambata sun taimake shi. Wataƙila, sun yi tarayya da Kiristoci da su na Al’ummai ne, kuma da farin ciki sun bi Bulus a yi wa na Al’ummai wa’azi.—Romawa 11:13; Galatiyawa 1:16; 2:11-14.
18. Ta yaya Bulus ya yaba wa wasu da ke tare da shi?
18 Ka lura da furcin Bulus: “Sun kuwa sanyaya mini zuciya.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Ya yi amfani da kalmar Helenanci da ta bayyana sau ɗaya cikin Littafi Mai Tsarki. Masu fassara da yawa sun fassara ta “ta’aziyya.” Amma, akwai wata kalmar Helenanci (pa·ra·ka·le’o) da aka fi fassara ta “ta’aziyya.” Bulus ya yi amfani da wannan a wani waje cikin wannan wasiƙar amma ba a Kolosiyawa 4:11 ba ne.—Matiyu 5:4; Ayyukan Manzanni 4:36; 9:31; 2 Korantiyawa 1:4; Kolosiyawa 2:2; 4:8.
19, 20. (a) Menene ma’anar furci da Bulus ya yi amfani da shi wa ’yan’uwa da suke taimakonsa a Roma? (b) A waɗanne hanyoyi ne ƙila waɗannan ’yan’uwa suka taimaki Bulus?
19 Waɗanda Bulus ya ambata sunansu sun aikata fiye da ta’aziyya ta baki. Kalmar Helenanci da aka fassara ‘sanyaya zuciya’ a Kolosiyawa 4:11 wasu lokatai ana amfani da ita a littattafai na duniya cewa magani da ke sauƙaƙa wahala ne. New Life Version ya ce: “Su mataimaka ne gare ni!” Today’s English Version ya yi amfani da furci nan: “Sun zama da taimako mai girma gare ni.” Menene waɗannan ’yan’uwa Kirista kusa da Bulus suka yi su taimake shi?
20 Bulus zai iya samun baƙi, amma akwai abubuwa da yawa da ba zai iya yi ba, irin su sayen abubuwa da yake bukata—abinci da kuma sutura don lokacin sanyi. Ta yaya zai samu littattafai na nazari ko kuma ya sayi kayayyakin rubutu? (2 Timoti 4:13) Ba ka yi tunani ba cewa waɗannan ’yan’uwa sun taimaki Bulus da bukatunsa, suna yin abubuwa kamarsu cefane da yin wasu aiki? Zai so ya bincika kuma ya ƙarfafa wata ikilisiya. Da yake an ɗaure shi ba zai iya hakan ba, saboda haka ƙila waɗannan ’yan’uwa sun yi wa Bulus ziyara, suna ɗaukan saƙo, su kuma mayar masa da rahoto. Lalle wannan na sanyaya zuciya!
21, 22. (a) Me ya sa za mu yi marmarin kalmomi da ke Kolosiyawa 4:11? (b) Waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin amfani da misalin waɗanda suke tare da Bulus?
21 Abin da Bulus ya rubuta game da ‘sanyaya masa zuciya’ ya sa mun fahimci yadda za mu taimake wasu. Mai yiwuwa suna zaman da ya cancanci bautar Jehovah game da mizanan ɗabi’a, halartar taron Kirista, da sa hannu cikin aikin wa’azi. Saboda haka, sun cancanci mu yi musu godiya. Amma, za mu iya ‘sanyaya zuciya’ kamar yadda waɗanda suke tare da Bulus suka yi?
22 Idan ka san ’yar’uwa da take biyayya da 1 Korantiyawa 7:37 amma yanzu tana rashin iyali da ke kusa da ita, za ka iya haɗa ta a wasu ayyuka na iyali, wataƙila ka gayyace ta cin abinci ko wani ɗan shakatawa da abokane ko dangi? Me zai hana gaya ma ta ku yi tafiya tare da iyalinka zuwa babban taro ko hutu? Ko ka gaya ma ta ta bi ku cefane lokacin da ya fi kyau. Haka ma za a yi wa gwauro da gwauruwa, ko wataƙila waɗanda yanzu ba sa iya tuƙa mota. Za ka iya jin labaransu ko ka koyi daga iliminsu na yin abubuwa irinsu zaɓan ’ya’yan itace masu kyau ko zaɓan kayan yara. (Littafin Firistoci 19:32; Karin Magana 16:31) Sakamakon shi ne za ku zama abokai na kurkusa. Da haka za su kasance a sake su gaya maka ka taimake su idan suna bukatar wasu magani daga kantin magani, ko wani waje. ’Yan’uwa da suke tare da Bulus a Roma sun ba shi taimako mai amfani, na ban ƙarfafa, yadda naka zai iya zama. Lokacin can da yanzu ƙarin albarka ne a ƙarfafa gamin ƙauna, kuma mu ƙuduri aniyya mu bauta wa Jehovah tare cikin aminci.
23. Zai yi kyau kowannenmu ya ba da lokacin yin menene?
23 Kowannenmu zai iya tunani a kan yanayi da aka ambata cikin wannan talifi. Misalai masu sauƙi ne, amma wannan zai tunatar mana da takamaiman yanayi da za mu fi ‘sanyaya zuciyar’ ’yan’uwanmu maza da mata. Ba a nufin mu gina halayen waɗanda suke gabatar da zaman lafiyar mutane ba. ’Yan’uwa da aka ambata a Kolosiyawa 4:10, 11 wannan ba burinsu ba ne. Su ‘abokan aiki ne ga Mulkin Allah.’ Taimako da suka bayar game da wannan ne. Bari ya zama hakan a gare mu.
24. Menene ainihin dalilin yin addu’a domin wasu kuma mu biɗi mu sanyaya wa wasu zuciya?
24 Muna ambata sunan wasu cikin addu’a na kanmu kuma muna ƙoƙari mu sanyaya musu zuciya domin wannan: Mun gaskata cewa ’yan’uwanmu maza da mata suna so su “yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, [su]na faranta masa ta kowane fanni.” (Kolosiyawa 1:10) Wannan gaskiya na da alaƙa da wani abu da Bulus ya ambata lokacin da yake rubutu game da addu’ar Abafaras domin Kolosiyawa, ‘suna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.’ (Kolosiyawa 4:12) Yaya mu kanmu za mu cim ma wannan? Bari mu gani.
[Hasiya]
a Dubi Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafofi 490-491, da “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial,” shafofi 226-228, Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.
Ka Lura Kuwa?
• Yaya za mu fi kasancewa da taimako cikin addu’o’i na kanmu?
• A wane azanci ne wasu Kiristoci suka ‘sanyaya zuciya’ wa Bulus?
• A waɗanne irin yanayi ne za mu zama masu ‘sanyaya zuciya’?
• Me ya sa muke addu’a domin wasu kuma mu biɗi mu sanyaya zuciyar ’yan’uwanmu maza da mata?
[Hoto a shafi na 10]
Za ka iya haɗa wani Kirista cikin fita yawo na iyalinka?
[Inda aka Dauko]
Green Chimney’s Farm ne suka bayar