Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 1/1 pp. 11-16
  • Ku Dage Kuna Cikakku Masu Haƙƙaƙewa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Dage Kuna Cikakku Masu Haƙƙaƙewa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Ƙoƙari Ku “Dage Kuna Cikakku”
  • Ka Yi Addu’a don Haƙƙaƙewa
  • Ku Taimake Wasu Su Yi Zaman Da Ya Cancanci Bautar Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Taimaka wa Matasa da Gargaɗi a Kan Lokaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Abin da Kake Sa Zuciya a Kai Zai Tabbata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • In “Kun San Wadannan Abubuwa, Za Ku Zama Masu Albarka Idan Kun Yi Su”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 1/1 pp. 11-16

Ku Dage Kuna Cikakku Masu Haƙƙaƙewa

“Kullum yana yi muku addu’a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.”—KOLOSIYAWA 4:12.

1, 2. (a) Waɗanda suke a waje sun lura da menene game da Kiristoci na farko? (b) Yaya littafin Kolosiyawa ya nuna damuwa mai kyau?

MABIYAN Yesu suna damuwa sosai da ’yan’uwansu masu bi. Tertullian (marubuci na ƙarni biyu da uku A.Z.) ya faɗi game da alheri da suka yi wa marayu, matalauta, da tsofaffi. Waɗannan ayyuka na ƙauna ya burge marasa bi har wasu suka ce game da Kiristoci, ‘Duba yadda suke ƙaunar juna.’

2 Littafin Kolosiyawa ya nuna damuwa mai kyau da manzo Bulus da abokin tarayyarsa Abafaras suke da shi ga ’yan’uwa maza da mata a Kolosi. Bulus ya rubuta musu: Abafaras “kullum yana yi muku addu’a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.” A shekara ta 2001, jigon shekara na Shaidun Jehovah shi ne waɗannan kalmomi na Kolosiyawa 4:12: “Ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.”

3. Game da waɗanne abubuwa biyu Abafaras ya yi addu’a?

3 Za ku ga cewa addu’o’in Abafaras game da ƙaunatattunsa yana da fannoni biyu: (1) su dage “[su]na cikakku” kuma na (2) su dage “masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.” Wannan labari an saka cikin Nassosi don amfaninmu ne. Saboda haka ka tambayi kanka, ‘Me nake bukata na yi don in dage cikakke kuma haƙƙaƙe cikin dukan nufin Allah? Yayin da nake haka, menene zai zama sakamakon wannan?’ Bari mu gani.

Ku Yi Ƙoƙari Ku “Dage Kuna Cikakku”

4. A wane azanci Kolosiyawa suke bukatar su zama “cikakku”?

4 Abafaras ya damu ƙwarai ’yan’uwansa na ruhaniya maza da mata a Kolosi su ‘dage suna cikakku.’ Kalmar da Bulus ya yi amfani da ita, a nan “cikakku,” zai iya nufin kamiltattu, dattako, ko manyanta. (Matiyu 19:21; Ibraniyawa 5:14; Yakubu 1:4, 25) Wataƙila ka san cewa zama Mashaidi na Jehovah da ya yi baftisma ba ya nufin cewa mutumin Kirista ne da ya yi dattako. Bulus ya rubuta wa Afisawa da ke da zama a yammacin Kolosi, cewa makiyaya da masu koyarwa su yi ƙoƙarin taimaka wa duka su “riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu.” A wani waje Bulus ya aririce Kiristoci ‘wajen hankali su yi dattako.’—Afisawa 4:8-13, tafiyar tsutsa tamu ce; 1 Korantiyawa 14:20.

5. Ta yaya za mu sa zama cikakku makasudi na musamman?

5 Idan wasu a Kolosi har ila ba su yi dattako ba, ko ba su manyanta a ruhaniya ba, wannan ya kamata ya zama makasudinsu. Bai kamata ya zama hakan a yau ba? Ko mun yi baftisma shekaru da yawa da suka shige ko a baya bayan nan muka yi, shin mun yi dattako sosai wajen hankalinmu da ra’ayoyinmu? Muna bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kafin mu tsai da shawarwari? Shin batutuwa game da Allah da abubuwa na ikilisiya suna ɗaukar matsayi mafi girma a rayuwarmu kuwa, maimakon ya faru kurum? Ba za mu iya kwatanta a nan dukan hanyoyi da za mu iya nuna irin girman nan na zama cikakku ba, amma ka yi la’akari da misalai biyu.

6. A wane fasali ne wani zai iya ya yi girma zuwa zama kamilcacce, yadda Jehovah yake?

6 Misali na ɗaya: A ce mun yi girma a inda ake nuna halin sonkai na ƙabilanci, kishin ƙasa, ko yanki. Yanzu mun san cewa Allah ba ya tara domin haka bai kamata mu mu yi ba. (Ayyukan Manzanni 10:14, 15, 34, 35) A cikin ikilisiyarmu ko a da’irar, akwai waɗanda suka fito daga wurare dabam dabam, haka muke a gare su. Duk da haka, yaya muke mugun tunani a ciki ko yin shakkar irin mutanen nan? Muna da halin ‘ɓacin rai’ muna saurin mummunar tunanin idan wani daga tsakanin irin mutanen nan ya yi kuskure ko ya yi mana wani ɗan laifi? Ka tambayi kanka, ‘Ina bukata in yi girma ne wajen kasancewa da ra’ayin Allah wanda ba ya tara?’

7. Zama cikakken Kirista zai ƙunshi ɗaukar wasu yaya?

7 Misali na biyu: In ji Filibiyawa 2:3, kada mu yi “kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali’u, kowa na mai da ɗan’uwansa ya fi.” Yaya muke yi a wannan batu? Kowanne mutum yana da kumamanci da kuma ƙarfi. Idan a dā muna saurin lura da kumamancin wasu, shin mun yi gyara, mun daina tsammanin sun zama kusan ‘cikakku’? (Yakubu 3:2) Yanzu, fiye da dā, muna iya gani—mu nemi—hanyoyi da wasu sun fi mu? ‘Lalle wannan ’yar’uwa ta fi ni haƙuri.’ ‘Wannan mutum ya fi nuna bangaskiya mai ƙarfi.’ ‘Gaskiya, ya fi ni iya koyarwa da kyau.’ ‘Ta fi ni sauƙin hali.’ Wataƙila wasu Kolosiyawa suna bukatar su yi girma a wannan fanni. Haka muke?

8, 9. (a) A wane azanci ne Abafaras ya yi addu’a Kolosiyawa su “dage” suna cikakku? (b) ‘Dage cikakku’ yana nufin menene game da gaba?

8 Abafaras ya yi addu’a Kolosiyawa su ‘dage cikakku.’ A bayyane yake sarai, Abafaras yana wa Allah addu’a cewa yawan yadda Kolosiyawa suke Kiristoci cikakku, da sun manyanta, da dattako, za su “dage,” ko su ci gaba da yin hakan.

9 Ba za mu aza cewa kowanne da ya zama Kirista, ko wanda ya manyanta ma, zai ci gaba hakan. Yesu ya ce wani mala’ika ɗan Allah “bai zauna kan gaskiya ba.” (Yahaya 8:44) Bulus ya tunasar wa Korantiyawa game da wasu dā waɗanda suka bauta wa Jehovah amma sun kasa. Ya gargaɗi ’yan’uwa shafaffu: “Wanda ke tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi.” (1 Korantiyawa 10:12) Wannan ya daɗa sa ƙarfi ga addu’ar cewa Kolosiyawa su ‘dage suna cikakku.’ Muddin sun zama cikakku, sun yi dattako, suna bukatar su nace, kada su ja baya, su gaji, ko su zakuɗa. (Ibraniyawa 2:1; 3:12; 6:6; 10:39; 12:25) Da haka za su zama “cikakku” a rana da za a bincika su da kuma amincewa na ƙarshe.—2 Korantiyawa 5:10; 1 Bitrus 2:12.

10, 11. (a) Abafaras ya kafa mana wane gurbi a yin addu’a? (b) Daidai da abin da Abafaras ya yi, wace shawara za ka so ka tsai da ita?

10 Mun riga mun tattauna muhimmancin ambata sunan wasu cikin addu’a, muna gaya wa Jehovah ainihi ya taimake su, ya yi musu ta’aziya, ya albarkace su, ya kuma ba su ruhu mai tsarki. Addu’o’in da Abafaras ya yi wa Kolosiyawa irin waɗannan ne. Za mu iya—hakika, ya kamata—cikin waɗannan kalmomi mu sami shawara mai kyau game da abin da muke gaya wa Jehovah cikin addu’a game da kanmu. Babu wata tantama, ya kamata mu biɗi taimakon Jehovah a yin haka don kowannen mu ya ‘dage muna cikakku.’ Kana yin hakan?

11 Me ya sa ba za ka ambata yanayinka cikin addu’a ba? Ka gaya wa Allah yadda ka kai game da zama ‘cikakke,’ da dattako, wanda ya manyanta. Ka roƙe shi ya taimake ka gane wurare inda kana tukuna ka kai girma a ruhaniya. (Zabura 17:3; 139:23, 24) Babu shakka, kana da fannonin nan. Maimakon ka yi sanyin jiki game da wannan, ka bayyana wa Allah dalla-dalla cikin addu’a, ya taimake ka ka manyanta. Ka yi haka fiye da sau ɗaya. Hakika, me ya sa ba za ka shawarta cewa wannan mako mai zuwa za ka yi addu’a mai tsawo kaɗan don ka ‘dage kana cikakke.’ Ka shirya ka yi haka sosai yayin da ka ke bincika jigon shekarar. Lokacin da ka ke addu’a, ka mai da hankali ga abubuwa da za su sa ka ja da baya, ka gaji, ko zakuɗa daga hidimar Allah da yadda za ka guje yin haka.—Afisawa 6:11, 13, 14, 18.

Ka Yi Addu’a don Haƙƙaƙewa

12. Me ya sa Kolosiyawa musamman suke bukatar “haƙƙaƙewa”?

12 Abafaras ya yi addu’a don wani abu da yake da muhimmanci idan Allah zai amince da tsayawan Kolosiyawa. Yana da muhimmanci ma a gare mu. Menene wannan? Ya yi addu’a cewa su dage “masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.” An kewaye su da koyarwar ƙarya da ussan ilimi mai lahani, wasu suna yaudara daga bauta na gaskiya. Alal misali, an matsa musu su yi bikin wasu ranaku na musamman da yin azumi ko biki, yadda ake bukatar haka a lokacin a bautar Yahudawa. Malaman ƙarya sun mai da hankali a kan mala’iku, waɗannan ruhohi masu ƙarfi suna idar da Dokar Musa. Ka ƙaga kasancewa cikin irin matsin nan! Akwai mutane da yawa da suka rikice da ra’ayoyi da suka saɓa wa juna.—Galatiyawa 3:19; Kolosiyawa 2:8, 16-18.

13. Gane wane abu ne zai taimake Kolosiyawa, yaya hakkan zai iya taimakonmu?

13 Bulus ya ba da tabbaci ta wajen nanata matsayin Yesu Almasihu. “Da ya ke kun yi na’am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya gare shi, kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku.” Hakika, akwai bukata (ga Kolosiyawa da mu kuma) don cikakken haƙƙaƙewa game da matsayin Kristi cikin nufin Allah da kuma cikin rayuwarmu. Bulus ya yi bayani: “A cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar allahntaka ke tabbata. A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko.”—Kolosiyawa 2:6-10.

14. Me ya sa sa zuciya aba ce da take da muhimmanci ga waɗanda suke cikin Kolosi?

14 Kolosiyawan Kiristoci ne da ruhu ya shafe su. Sa zuciyarsu dabam ce, rayuwa a sama, kuma suna da kowane dalili su sa zuciyarsu ya yi haske. (Kolosiyawa 1:5) “Nufin Allah” ne su kasance masu haƙƙaƙewa game da tabbacin sa zuciyarsu. Ya kamata kowanne cikinsu ya yi shakkar wannan sa zuciyar? Ko kaɗan! Wannan zai zama dabam ne a yau ga dukan waɗanda suke da zaton da Allah ya bayar na rayuwa cikin aljanna ta duniya? A’a! Wannan sa zuciya bangaren “nufin Allah” ne. Ka yi la’akari da waɗannan tambayoyi: Idan kana ƙoƙari ka kasance cikin “ƙasaitaccen taro” waɗanda za su tsira a “matsananciyar wahala,” sa zuciyarka tabbacacciya ce? (Wahayin Yahaya 7:9, 14) Yana cikin “haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah” da ka ke yi?

15. Bulus ya tsara waɗanne abubuwa ne da sun haɗa da sa zuciya?

15 Ta wajen “sa zuciya” ba ma nufin muradi da ba a ganewa, ko kuma wasiƙar jaki. Za mu gane wannan daga abubuwa da Bulus ya gabatar wa Romawa a farko. A cikin wannan tsari, kowanne abu da aka ambata na haɗe da ko kuma yana kai ga wani. Ka mai da hankali ga inda Bulus ya saka “sa zuciya” a ba da tabbacinsa: “Muna taƙama da shan wuyarmu, da ya ke mun sani shan wuya ke sa jimiri, jimiri kuma ke sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma ke sa sa zuciya, ita sa zuciyan nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙauna tasa a zukatanmu, ta Ruhu Mai Tsarki.”—Romawa 5:3-5.

16. Yayin da ka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki, wace sa zuciya ka samu?

16 Lokacin da Shaidun Jehovah da farko suka gaya maka saƙon Littafi Mai Tsarki, wata gaskiya mai yiwuwa ta kwashe maka hankali, irinsu yanayin matattu ko tashin matattu. Ga mutane da yawa, abin da suka fahimta da farko a Littafi Mai Tsarki shi ne cewa rayuwa cikin aljanna ta duniya za ta yiwu. Ka tuna lokacin da ka ji wannan koyarwa da farko. Lalle sa zuciya ne mai girma—ciwo da tsufa ba za su ƙara kasancewa ba, za ka rayu ka more riban aikinka, salama za ta kasance tare da dabbobi! (Mai Hadishi 9:5, 10; Ishaya 65:17-25; Yahaya 5:28, 29; Wahayin Yahaya 21:3, 4) Ka samu sa zuciya mai ban al’ajabi!

17, 18. (a) Ta yaya tsari da Bulus ya gabatar ga Romawa ya kai ga sa zuciya? (b) Wane irin sa zuciya ne ake nufi a Romawa 5:4, 5, kana da irin wannan?

17 Da shigewar lokaci, wataƙila za ka fuskanci adawa ko tsanani. (Matiyu 10:34-39; 24:9) Har ma a baya bayan nan, Shaidu a ƙasashe dabam dabam an ci ganimar gidajensu ko kuma an tilasta su su zama ’yan gudun hijira. Wasu an doke su, an kwace littattafansu na Littafi Mai Tsarki, ko kuma yaɗa labaran ƙarya game da su. Ko wane irin tsanani da ƙila ka fuskanta, yadda Romawa 5:3 ta ce, za ka iya taƙama da shan wuya, zai kawo sakamako mai kyau. Yadda Bulus ya rubuta, shan wuya zai sa ka jimiri. Jimiri kuma ke sa ingataccen hali. Ka san kana yin abin da ke daidai, kana yin nufin Allah, saboda haka ka tabbata cewa ya amince da kai. A kalmomin Bulus, ka gane ma’anar kasancewa cikin “ingataccen hali.” Da yake ci gaba Bulus ya rubuta cewa “ingataccen hali kuma [ke sa] sa zuciya.” Wannan zai iya zama da wuya. Me ya sa Bulus ya haɗa “sa zuciya” cikin jerin? Ba ka da sa zuciya tun da daɗewa, lokacin da ka ji bisharar da farko?

18 A bayane yake, Bulus a nan ba ya nufin yadda muka ji dā game da sa zuciyar kamilcaccen rai. Abin da yake nufi ya wuci wannan; yana da zurfi, ya fi motsawa. Yayin da mun jimre cikin aminci kuma ta haka muka gane cewa Allah ya amince da mu, wannan yana da amfani sosai na ƙara kuma na ƙarfafa sa zuciyarmu da muke da ita a farko. Sa zuciyar da muke da ita yanzu za ta ƙara zama tabbacacciya, ya fi ƙarfi, ya zama na zuciyarmu. Wannan sa zuciya mai zurfi zai ƙara haskakawa. Tana cika rayuwarmu, kowanne bangaren jikinmu. “Ita sa zuciyan nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙauna tasa a zukatanmu, ta Ruhu Mai Tsarki.”

19. Yaya ya kamata sa zuciyarka ta kasance cikin addu’arka ta kullum?

19 Abafaras ya yi addu’a da himma ’yan’uwansa maza da mata a Kolosi su kasance waɗanda abin da ke gaba ke taɓa su kuma huɗubantar da su, su kasance “masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.” Hakanan, bari kowannenmu mu kusaci Allah kullum game da sa zuciya tamu. Cikin addu’arka, ka haɗa sa zuciyarka ta sabuwar duniya. Ka gaya wa Jehovah yadda ka ke marmarinta, da cikakken tabbaci cewa za ta zo. Ka yi masa addu’a ya taimake ka ka zurfafa kuma faɗaɗa tabbacinka. Yadda Abafaras ya yi addu’a don Kolosiyawa su zama “masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah,” ka yi hakan. Ka yi shi a kai a kai.

20. Idan kalilan suka juya daga hanya ta Kirista, me ya sa wannan ba zai zama dalilin sanyin jiki ba?

20 Kada hankalinka ya janye ko ka yi sanyin jiki don ba duka ba ne suka dage suna cikakku kuma masu haƙƙaƙewa. Mai yiwuwa wasu za su fāɗi, su juya baya, ko fid da zuciya. Wannan ya faru tsakanin waɗanda suka fi kusa da Yesu, manzanninsa. Amma lokacin da Yahuza ya zama mai cin amana, sauran manzannin sun rage hanzari ko sun daina aikin ne? Sam sam! Bitrus ya yi amfani da Zabura 109:8 ya nuna cewa wani zai ɗauki matsayin Yahuza. Aka zaɓi wani, amintattun Allah suka ci gaba da aikinsu na wa’azi da ƙwazo. (Ayyukan Manzanni 1:15-26) Sun ƙuduri anniyar su dage suna cikakku masu haƙƙaƙewa.

21, 22. A wane azanci ne za a lura da dagewarku cikakku, masu haƙƙaƙewa?

21 Za ka tabbata cewa za a lura da dage cikakku da kuma haƙƙaƙewa a dukkan nufin Allah da ku ke yi. Za a lura da shi a kuma nuna godiya. Wanene zai lura?

22 ’Yan’uwanka maza da mata, waɗanda suka san ka kuma suna ƙaunarka za su lura. Ko ma yawanci ba su furta ba, sakamakon zai zama kamar abin da muka karanta a 1 Tasalonikawa 1:2-6: “Kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku cikin addu’armu, ba ma fasa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da faman da kuke yi domin ƙauna, da kuma sa zuciyarku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu. Domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, har ma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. . . . kuka zama masu koyi da mu, da kuma da Ubangiji.” Amintattun Kiristoci da sun kewaye ku za su ji hakanan yayin da sun lura cewa “kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.”—Kolosiyawa 1:23.

23. Me ya kamata ya zama ƙudurinka, baɗi?

23 Babu shakka, Ubanku na samaniya zai lura kuma zai yi farin ciki. Ka tabbata da wannan. Me ya sa? Domin kuna dagewa cikakku, masu haƙƙaƙewa “cikin dukkan nufin Allah.” Bulus ya rubuta yana ƙarfafa Kolosiyawa game da zamansu ‘da ya cancanci bautar Ubangiji, suna faranta masa.’ (Kolosiyawa 1:10) Hakika, yana yiwuwa mutane ajizai su faranta masa rai sosai. ’Yan’uwanka Kolosiyawa maza da mata sun yi hakan. Kiristoci da sun kewaye ka yanzu suna yin haka. Kai ma za ka iya yin haka! Saboda haka, a wannan shekara mai zuwa, bari addu’arka ta kowacce rana da ayyukanka na kullum su nuna ka ƙuduri anniyar ‘kana cikakke, mai haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.’

Za Ka Iya Tuna?

• Menene ka ‘dage kana cikakke’ ya ƙunsa?

• Waɗanne abubuwa game da kanka ya kamata ka haɗa cikin addu’a?

• Yadda aka shawarta a Romawa 5:4, 5, wane irin sa zuciya ka ke so ka samu?

• Nazarinmu ya motsa ka ka kasance da wane makasudi a baɗi?

[Hoto a shafi na 12]

Abafaras ya yi addu’a ’yan’uwansa su kasance Kiristoci da sun manyanta, da haƙƙaƙewa game da Kristi da sa zuciyarsu

[Hotuna a shafi na 15]

Wasu miliyoyi suna da sa zuciyar da ka ke da shi da kuma haƙƙaƙewa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba