Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 9/1 p. 3
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Aka Kira Yesu Dan Allah?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Allah da Kuma Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 9/1 p. 3

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Kolossiyawa 1:16 ta ce game da Ɗan Allah “dukan abu ta wurinsa an halitta su, dominsa kuma.” A wane azanci ne aka halicci dukan abu ‘domin’ Ɗan Allah, Yesu?

Jehovah ya yi amfani da Ɗansa makaɗaici gwanin aiki wajen halittar dukan abu, wato, dukan abu ban da Yesu kansa. (Misalai 8:27-30; Yohanna 1:3) Daidai, Ɗan yana jin daɗin waɗannan ayyukan, a wannan azanci kuwa “dominsa” ne.

Mun sani cewa iyaye suna tsammanin farin ciki, kuma sau da yawa suna samu, daga abin da suka haifa—’ya’yansu. Da haka, misalai na Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “ɗan da [ubansa] ya ke jin daɗinsa.” (Misalai 3:12; 29:17) Hakanan ma, Jehovah Allah ya ji daɗin Isra’ila lokacin da mutanensa suke da aminci. (Zabura 44:3; 119:108; 147:11) Yana jin daɗin amincin amintattunsa zuwa lokacinmu.—Misalai 12:22; Ibraniyawa 10:38.

Da haka, ya dace da Allah zai so abokin aikinsa Yesu ya ji daɗin ayyukansa. Hakika, Misalai 8:31 ta ce Ɗan ‘yana farin ciki cikin wuraren zama na duniyarsa, daularsa tana wurin ’yan Adam.’ A wannan azanci ne Kolossiyawa 1:16 ta ce: “Dukan abu ta wurinsa an halitta su, dominsa kuma.” (Tafiyar tsutsa tamu ce).

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba