Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 6/15 pp. 30-31
  • Masu Hikima Suna Biɗan “Ingantattun Shawarwari”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Masu Hikima Suna Biɗan “Ingantattun Shawarwari”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TA YAYA ZA MU SAMU “INGANTATTUN SHAWARWARI”?
  • KA YI TUNANIN ABIN DA ZAI FARU NAN GABA KUMA KA YI SHIRI
  • Hikima Tana Kira da Babban Murya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Matasa, Ku Bar Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 6/15 pp. 30-31

Masu Hikima Suna Biɗan “Ingantattun Shawarwari”

An kwatanta rayuwa da yin tafiya da jirgin ruwa. Amma, hikimar ’yan Adam ba ta yawan taimaka wa mutane a rayuwa. Mutane da yawa sun fuskanci haɗari a rayuwa. (Zab. 107:23, 27) Me ya sa ya dace a kwatanta matsaloli na rayuwa da yin tafiya mai haɗari a cikin jirgin ruwa?

A zamanin dā, ana bukatar fahimi sosai don a yi tafiya cikin teku. Aiki ne da ake koya daga wurin waɗanda suka daɗe suna tuƙa jirgin ruwa. (A. M. 27:9-11) A zane-zane da yawa na zamanin dā, an zana matuƙin jirgin ruwa da girma sosai fiye da sauran mutanen da suke cikin jirgin, kuma hakan ya nuna cewa aikin matuƙin yana da muhimmanci sosai. Masu tafiya da jirgin ruwa suna koyo game da taurari da iska da kuma wasu abubuwa da za su taimaka musu su gane wani yanayi kafin su soma tafiya a cikin teku. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa wasu masu aiki a jirgin ruwa suna da “wayo.”—Ezek. 27:8.

Bi da matsalolin rayuwa a yau yana da wuya sosai kamar yin tafiya a cikin teku a zamanin dā. Mene ne zai iya taimaka mana?

TA YAYA ZA MU SAMU “INGANTATTUN SHAWARWARI”?

Ka yi la’akari da wannan gaskiyar Littafi Mai Tsarki da ta daɗa nuna cewa rayuwa tana kama da yin tafiya a cikin jirgin ruwa: ‘Mai-hikima shi ji, shi ƙaru da ilimi: mai-fahimi kuma shi kai ga ingantattun shawarwari.’ (Mis. 1:5, 6) Za a iya yin amfani da furuci na Ibrananci da aka fassara “ingantattun shawarwari” don a kwatanta ayyukan matuƙin jirgin ruwa na zamanin dā. Yana nufin yin amfani da hikima don yin ja-gora.

Ko da hakan yana bukatar yin ƙoƙari sosai, muna iya samun “ingantattun shawarwari” kuma mu koya yadda za mu yi nasara a rayuwa. Kamar yadda littafin Misalai ya nuna, muna bukatar mu biɗi “hikima” da “koyarwa” da kuma “fahimi.” (Mis. 1:2-6; 2:1-9) Kuma wajibi ne mu nemi ja-gorar Allah, domin ko miyagu sun san yadda ake ba da shawarwari don su ruɗi mutane.—Mis. 12:5.

Saboda haka, yana da muhimmanci sosai mu zama masu nazarin Kalmar Allah da ƙwazo. Ta irin wannan nazarin, za mu koya abubuwa masu tamani game da Jehobah da kuma Yesu Kristi wanda ya fi yin koyi da Jehobah. (Yoh. 14:9) Muna samun shawarwari masu kyau a tarurrukan Kirista. Ƙari ga hakan, muna iya koyan abubuwa daga wurin wasu mutane, har da iyayenmu.—Mis. 23:22.

KA YI TUNANIN ABIN DA ZAI FARU NAN GABA KUMA KA YI SHIRI

“Ingantattun shawarwari” suna da muhimmanci sosai sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Rashin sanin matakin da za mu ɗauka sa’ad da muke cikin yanayi mai wuya yana iya raunana mu, kuma hakan zai kawo mugun sakamako.—Yaƙ. 1:5, 6.

Ana kuma yin amfani da furucin nan “ingantattun shawarwari” idan ana yin magana game da yaƙi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ana bukatar shawara ta hikima [“dabara mai kyau,” in ji fassarar Revised English Bible] cikin yaƙinka: cikin taron masu-shawara kuma akwai nasara.”—Mis. 20:18; 24:6.

Kamar mai tsara yadda za a yi yaƙi, ya kamata mu yi tunani kuma mu yi shiri don kawar da abubuwan da za su ɓata dangantakarmu da Jehobah. (Mis. 22:3) Alal misali, wataƙila za ka tsai da shawara ko za karɓi sabon aiki ko kuma ƙarin girma a wurin aiki. Za ka yi la’akari da albashin da lokacin tafiya zuwa wurin aiki da dawowa da kuma wasu abubuwa. Amma, da akwai wasu abubuwa da za ka ƙara yin tunani a kai: Shin wannan aikin ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? Ta yaya canje-canje a tsarin aikin zai shafi hidimata ga Jehobah?—Luk 14:28-30.

Wata Mashaidiyar Jehobah mai suna Loretta ta samu aiki mai kyau a wani kamfanin abinci. Sa’ad da suke son su kai kamfanin zuwa wani wuri, an ba Loretta matsayi mai kyau a sabon wurin. Darektocin suka gaya mata: “Wannan zarafi ne mai girma da ba za ki taɓa samu kuma ba. Mun riga mun gano cewa akwai Majami’ar Mulki a wurin.” Amma, Loretta tana son ta sauƙaƙa salon rayuwarta don ta bauta wa Mahaliccin sosai. Ta ga cewa sabon aikin ba zai ba ta lokacin yin ayyuka na Kirista ba. Saboda haka, ta yi murabus ko da yake darektan ya gaya mata a ɓoye cewa ita kaɗai ce suke son ta ci gaba da yin aiki a kamfanin. Loretta, wadda ta yi shekara 20 yanzu tana hidimar majagaba na kullum tana da tabbaci cewa ta samu sakamako mai kyau don ta yi shirin da ya jitu da “ingantattun shawarwari,” wato, shawara da ke cikin Kalmar Allah. Ta ƙarfafa dangantakarta da Jehobah kuma ta samu gatan taimaka wa mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah.

Ana bukatar “ingantattun shawarwari” sosai a cikin iyali. Renon yara abu ne da ke ɗaukan lokaci, kuma zaɓin da iyaye suka yi game da yadda za su taimaka wa iyalinsu su kasance da dangantaka na kud da kud da Jehobah da kuma yadda za su samu abubuwan biyan bukatun iyalinsu suna shafan rayuwar dukan waɗanda suke cikin iyalin a nan gaba. (Mis. 22:6) Alal misali, iyaye suna iya tambayar kansu: ‘Ta wurin taɗin da muke yi da kuma misalinmu, muna koya wa yaranmu su kusaci Jehobah domin su jimre da matsalolin rayuwa a lokacin da suka yi girma? Salon rayuwarmu yana taimaka musu su fahimci yadda za su kasance da wadar zuciya don su sauƙaƙa rayuwarsu kuma su mai da hankali ga hidimarsu na Kirista?’—1 Tim. 6:6-10, 18, 19.

Yin nasara bai dangana ga biɗan abin duniya da kuma ayyukanta da mutane suke ɗaukan da muhimmanci ba. Sarki Sulemanu ya fahimci hakan. Jehobah ya hure shi ya rubuta: “Waɗanda ke tsoron Allah za su zama lafiya, masu-ibada ke nan.” (M. Wa. 8:12) Hakan ya nuna hikimar biɗan “ingantattun shawarwari” da suka jitu da Kalmar Allah.—2 Tim. 3:16, 17.

[Hoto a shafi na 30]

Don a nuna cewa aikin matuƙan jirgin ruwa yana da muhimmanci sosai, ana yawan zana su su fi sauran masu aiki a cikin jirgin girma

[Inda Aka Ɗauko]

Su concessione del Ministero per i Beni e le Attività Culturali. An haramta a sake buga ko kuma a kofa wannan hoton a kowacce hanya.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba