Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 pp. 3-7
  • Matasa, Ku Bar Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Ku Bar Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Bar Kalmar Allah ta Yi Muku Ja-gora a Cikin Iyali
  • Bin Ja-gorar Kalmar Allah Sa’ad da Kuke Amfani da Kuɗi
  • Ku Bari Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora Sa’ad da Kuka Kaɗaita
  • Ku Faranta Zuciyar Jehobah
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Iyaye Da Yara, Ku Tattauna Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yana da Muhimmanci a Kafa Dokoki a Gida?
    Tambayoyin Matasa
  • Ka Yi Koyi Da Jehovah Yayin Da Kake Renon Yaranka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 pp. 3-7

Matasa, Ku Bar Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora

“Ka sami hikima, ka sami fahimi.”—MIS. 4:5.

1, 2. (a) Mene ne ya taimaki manzo Bulus ya jimre wa famar da ya yi? (b) Yaya za ku samu hikima da fahimi?

“NI DA na ke nufi in aika nagarta, ga mugunta gareni.” Ka san wanda ya furta waɗannan kalaman kuwa? Manzo Bulus ne. Ko da yake Bulus yana ƙaunar Jehobah, amma da akwai lokacin da ya yi gwagwarmaya don ya yi abin da ya dace. Yaya ya ji game da wannan famar da ya yi? Ya rubuta: “Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi!” (Rom. 7:21-24) Ka fahimci yadda Bulus ya ji kuwa? Yana yi maka wuya ka yi abin da ya dace a wani lokaci? Hakan yana sa ka baƙin ciki, kamar Bulus? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa. Bulus ya yi nasara wajen bi da ƙalubale da ya fuskanta, kai ma za ka iya yin hakan.

2 Bulus ya yi nasara domin ya bar “sahihiyan kalmomi” su yi masa ja-gora. (2 Tim. 1:13, 14) A sakamako, ya samu hikima da fahimi da yake bukata don ya jimre wa ƙalubale kuma ya tsai da shawarwari masu kyau. Jehobah Allah zai iya taimaka maka ka samu hikima da fahimi. (Mis. 4:5) Ya yi tanadin shawara mafi kyau a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (Karanta 2 Timotawus 3:16, 17.) Ku yi la’akari da yadda za ku iya amfana daga ƙa’idodin da ke cikin Nassosi sa’ad da kuke sha’ani da iyayenku, sa’ad da kuke tsai da shawara game da yadda za ku kashe kuɗi, da kuma sa’ad da kuka kaɗaita.

Ku Bar Kalmar Allah ta Yi Muku Ja-gora a Cikin Iyali

3, 4. Me ya sa zai iya yi muku wuya ku yi biyayya ga dokokin iyayenku, amma me ya sa iyaye suke kafa dokoki?

3 Yana yi muku wuya ku bi dokokin iyayenku ne? Me ya sa za ku ji hakan? Dalili ɗaya zai iya zama cewa kuna son a ɗan ba ku ’yanci. Hakan daidai ne. Yana nuna cewa kuna yin girma. Amma, sa’ad da kuke gida, wajibi ne ku yi biyayya ga iyayenku.—Afis. 6:1-3.

4 Fahimtar dalilin da ya sa iyayenku suka kafa dokoki da bukatu zai sa ya kasance muku da sauƙi ku bi su. Hakika, a wani lokaci za ku iya ji kamar Briellea ’yar shekara 18, wadda ta ce game da iyayenta: “Sun mance gabaki ɗaya ƙalubalen da waɗanda suke tsarata suke fuskanta. Ba sa son na faɗi ra’ayi ta, na tsai da shawara, ko kuma na yi girma.” Kamar Brielle, kuna iya jin cewa iyayenku suna hana ku ’yanci da kuke gani ya kamata su ba ku. Amma, ainihi dalilin da ya sa iyayenku suke kafa dokoki shi ne don sun damu da ku. Ƙari ga haka, iyaye Kiristoci sun san cewa za su ba da lissafi ga Jehobah game da yadda suka kula da ku.—1 Tim. 5:8.

5. Ta yaya za ku iya amfana ta wajen yin biyayya ga iyayenku?

5 Hakika, yin biyayya ga dokokin iyayenku yana kama da biyan bashin da kuka ci a banki, idan kuna saurin biyan bashinku, bankin zai riƙa ba ku rance. Haka nan ma, iyayenku suna bukata ku daraja su da kuma yi musu biyayya. (Karanta Misalai 1:8.) Idan kuna biyayya sosai, iyayenku za su daɗa ba ku ’yanci. (Luk 16:10) Hakika, idan kun ci gaba da taka dokokin, kada ku yi mamaki cewa iyayenku za su rage ko kuma su daina ba ku ’yanci.

6. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa matasa su yi biyayya?

6 Hanya ɗaya da iyaye za su iya taimaka wa yaransu su yi biyayya ga dokokin da suka kafa ita ce ta misali. Ya kamata biyayyarsu da yardan rai ga abin da Jehobah yake bukata ya nuna cewa dokokin Allah suna da kyau. Hakan zai taimaka wa matasa su fahimci cewa yana da kyau su yi biyayya ga dokoki da iyayensu suka kafa. (1 Yoh. 5:3) Ƙari ga hakan, Littafi Mai Tsarki ya ambata yanayi da yawa da Jehobah ya ba bayinsa zarafi su furta ra’ayinsu game da wasu batutuwa. (Far. 18:22-32; 1 Sar. 22:19-22) Shin da akwai lokacin da ya kamata iyaye su ba yaransu damar yin magana a kan batutuwa dabam dabam?

7, 8. (a) Wane ƙalubale ne wasu matasa suke fuskanta? (b) Fahimtar mene ne zai iya taimaka muku ku amfana daga horo?

7 Matasa suna iya fuskantar ƙalubalen bi da abin da suke ɗauka a matsayin zargi da bai dace ba daga iyayensu. A wani lokaci, za ku ji kamar wani matashi mai suna Craig, wanda ya ce, “Mahaifiyata tana kama da ɗan sandan ciki, a koyaushe tana neman wurare da na yi kuskure.”

8 A wasu yanayi, mukan ji cewa ana yi mana sūka sa’ad da aka yi mana gyara da horo. Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa yana da wuya a amince da horo, ko da a lokacin da ya dace ne. (Ibran. 12:11) Mene ne zai iya taimaka muku ku amfana daga horon da aka yi muku? Muhimmiyar abu da ya kamata ku tuna shi ne cewa wataƙila ƙauna ce ta motsa iyayenku su yi muku gargaɗi. (Mis. 3:12) Suna son su taimaka muku ku guji koyon halaye marasa kyau kuma ku koyi halaye masu kyau. Wataƙila iyayenku sun fahimci cewa idan ba su yi muku gyara ba, sun tsane ku ne! (Karanta Misalai 13:24.) Ku kuma fahimci cewa yin kurakurai hanyar koyo ne. Saboda haka, sa’ad da aka yi muku gyara, ku nemi muhimmiyar abu da ke cikin abin da aka faɗa. ‘Cinikin hikima ya fi cinikin azurfa kyau, ribarta kuma ta fi sahihiyar zinariya.’—Mis. 3:13, 14.

9. Maimakon su riƙa tunani game da abin da suke gani rashin adalci ne, mene ne matasa za su iya yi?

9 Amma, iyaye suna yin kurakurai. (Yaƙ. 3:2) Sa’ad da suke muku horo, suna iya yin magana da garaje. (Mis. 12:18) Mene ne zai iya sa iyayenku su aikata hakan? Wataƙila suna fuskantar matsi, ko kuma sun ɗauki kurakuranku a matsayin kasawa a gare su. Maimakon ku ci gaba da yin tunani a kan abin da kuke gani rashin adalci ne, ku nuna godiya don yadda suke son su taimaka muku. Amincewa da horo zai taimaka muku sosai sa’ad da kuka zama manya.

10. Ta yaya za ku iya bi da dokoki da gyara na iyayenku da kyau?

10 Za ku so ya yi muku sauƙi ku amince da kuma amfana daga dokoki da horon iyayenku ne? Idan haka ne, kuna bukatan ku kyautata yadda kuke tattaunawa da su. Yaya za ku iya yin hakan? Mataki na farko shi ne ku saurara. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane mutum ya yi hanzarin ji, ya yi jinkirin yin magana, ya yi jinkirin yin fushi.” (Yaƙ. 1:19) Maimakon ku yi saurin ba da hujja a kan abin da kuka yi, ku yi ƙoƙari ku kame kanku kuma ku saurari abin da iyayenku za su faɗa. Ku mai da hankali ga abin da aka faɗa, ba yadda aka faɗe shi ba. Sa’an nan ku nuna musu cewa kun fahimci abin da suka faɗa ta wajen amincewa da kuskurenku cikin ladabi. Yin hakan zai tabbatar musu cewa kun ji abin da suka faɗa. Idan kuna so ku ba da bayani game da furcinku ko kuma ayyukanku kuma fa? A yawancin yanayi, ya fi kyau “ku yi la’akari da furcinku” sai bayan kun yi abin da iyayinku suke so. (Mis. 10:19, NW) Muddin iyayenku sun ga cewa kun saurare su, za su fi kasancewa a shirye su saurare ku ma. Bi da al’amarin haka yana nuna cewa Kalmar Allah tana muku ja-gora.

Bin Ja-gorar Kalmar Allah Sa’ad da Kuke Amfani da Kuɗi

11, 12. (a) Mene ne Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu yi game da kuɗi, kuma me ya sa? (b) Ta yaya iyayenku za su taimaka muku ku yi amfani da kuɗi da kyau?

11 Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Kuɗi] kāriya ce.” Amma wannan ayar ta nuna cewa hikima ta fi kuɗi tamani. (M. Wa. 7:12) Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu daraja kuɗi, amma kada mu so shi. Me ya sa za mu guji son kuɗi? Ka yi la’akari da wannan kwatancin: Wuƙa mai kaifi tana da muhimmanci ga mai dafa abinci. Duk da haka, wannan wuƙar za ta iya yanka hannun wanda bai iya amfani da ita ba ko kuwa wanda bai mai da hankali ba. Idan aka yi amfani da kuɗi yadda ya kamata, zai iya zama da amfani. Amma, waɗanda “suna so su zama mawadata” sau da yawa suna ɓata abutarsu, dangantaka na iyalinsu, har da dangantakarsu da Allah. Saboda haka, sukan “hudu kansu da baƙinciki mai-yawa.”—Karanta 1 Timotawus 6:9, 10.

12 Ta yaya za ku koyi yin amfani da kuɗi da kyau? Ku nemi shawara wajen iyayenku a kan yadda za ku yi amfani da kuɗinku. Sulemanu ya rubuta: “Domin mai-hikima shi ji, shi ƙaru da ilimi: mai-fahimi kuma shi kai ga ingantattun shawarwari.” (Mis. 1:5) Wata matashiya mai suna Anna ta nemi shawara mai kyau daga wajen iyayenta. Ta ce, “Babana ya koya mini yadda zan yi amfani da kuɗi, kuma ya nuna mini yadda yake da muhimmanci na tsara yadda nake amfani da kuɗin iyalin.” Mamar Anna ma ta koya mata darussa masu amfani. “Ta nuna mini amfanin taya abubuwa a wurare dabam dabam kafin na saya,” in ji Anna. Ta yaya Anna ta amfana? Ta ba da amsa: “Yanzu ina iya yin amfani da kuɗina da kyau. Ina mai da hankali ga yadda nake kashe kuɗi, kuma ina da ’yanci da kwanciyar hankali da ake samu don guje wa cin bashi da bai dace ba.”

13. Ta yaya za ku hori kanku sa’ad da ya zo ga batun kashe kuɗi?

13 Kuna iya tara wa kanku bashi idan kuna sayan kaya bisa motsin rai ko kuma kuna kashe kuɗi don ku burge abokanku. Mene ne zai taimaka muku ku guji waɗannan tarkuna? Idan ya zo ga kashe kuɗi, dole ne ku koya ku hori kanku. Haka ne wata matashiya Ellena take yi. “Sa’ad da na fita tare da abokai na,” in ji ta, “Ina shiryawa tun da wuri kuma na yi lissafin iyakar kuɗin da zan kashe. . . . Kuma na ga hikimar zuwa yin sayayya tare da abokaina waɗanda suke mai da hankali da kuɗinsu kuma waɗanda za su ƙarfafa ni na taya abubuwa a wurare dabam dabam ba kawai na saya a wuri na farko da na taya ba.”

14. Me ya sa ya kamata ku mai da hankali game da “ruɗin dukiya”?

14 Samun kuɗi da yin amfani da shi da kyau abubuwa ne masu muhimmanci a rayuwa. Amma, Yesu ya ce “masu-ladabi a ruhu” ne za su yi farin ciki na gaske. (Mat. 5:3) Ya yi gargaɗi cewa abubuwa kamar su “ruɗin dukiya,” suna iya raba hankalin mutum daga abubuwa na ruhaniya. (Mar. 4:19) Saboda haka, yana da muhimmanci ku ƙyale Kalmar Allah ta yi muku ja-gora kuma ku kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi!

Ku Bari Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora Sa’ad da Kuka Kaɗaita

15. A wane lokaci ne za a fi gwada amincinku ga Allah?

15 A wane lokaci ne kuke tunani cewa za a fi gwada amincinku ga Allah, sa’ad da kuke tare da mutane ko kuma sa’ad da kuka kaɗaita? Hakika, sa’ad da kuke a makaranta ko wajen aiki kun fi kasancewa a faɗake ga kome da zai ɓata dangantakarku da Allah. Amma sa’ad da ba ku a faɗake ne za ku fi faɗa wa hari da za a kai ga mizananku na ɗabi’a.

16. Me ya sa za ku so ku yi biyayya ga Jehobah har a lokacin da kuka kaɗaita?

16 Me ya sa za ku so ku yi biyayya ga Jehobah ko a lokacin da kuka kaɗaita? Ku tuna wannan: Kuna iya ɓata wa Jehobah rai ko kuma ku sa shi farin ciki. (Far. 6:5, 6; Mis. 27:11) Abubuwan da kuke yi suna shafan Jehobah domin “yana kula da ku.” (1 Bit. 5:7) Yana son ku saurare shi don ku amfani kanku. (Isha. 48:17, 18) Wasu bayin Jehobah a Isra’ila ta dā sun ɓata masa rai, yayin da suka ƙi bin gargaɗinsa. (Zab. 78:40, 41) A wani ɓangare kuma, Jehobah yana ƙaunar annabi Daniyel sosai, gama wani mala’ika ya kira shi “mutum ƙaunatacce ƙwarai.” (Dan. 10:11) Me ya sa? Daniyel ya kasance da aminci ga Allah ba a lokacin da yake tare da mutane kawai ba amma sa’ad da ya kaɗaita.—Karanta Daniyel 6:10.

17. Waɗanne tambayoyi ne za ku yi wa kanku sa’ad da kuke zaɓan nishaɗi?

17 Don ku kasance da aminci ga Allah sa’ad da kuka kaɗaita, dole ne ku koyar da ‘hankulanku . . . garin rabewar nagarta da mugunta,’ kuma ku koyar da waɗannan hankulan “bisa ga aikaceya” ta wajen yin abin da kuka sani daidai ne. (Ibran. 5:14) Alal misali, sa’ad da kuke zaɓar waƙar da za ku saurara da bidiyon da za ku kalla, ko kuma dandalin Intane da za ku yi bincike, ga abin da zai taimaka muku ku zaɓa abin da ke daidai kuma ku guji abu marar kyau. Ku yi wa kanku waɗannan tambayoyi: ‘Wannan abin da na zaɓa zai ƙarfafa ni na yi juyayi ko kuma zai sa ni na yi farin ciki sa’ad da wani yake cikin “masifa”?’ (Mis. 17:5) ‘Zai taimaka mini na ‘ƙaunaci nagarta’ ko kuma zai sa ya yi mini wuya na “ƙi mugunta”?’ (Amos 5:15) Abin da kuke yi sa’ad da kuka kaɗaita zai nuna abubuwa da kuka fi ɗauka da tamani.—Luk 6:45.

18. Mene ne ya kamata ku yi idan kuna abu marar kyau a ɓoye, kuma me ya sa?

18 Mene ne ya kamata ku yi idan kuna yin abin da kun san ba shi da kyau a ɓoye? Ku tuna, “wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba: Amma dukan wanda ya faɗe su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.” (Mis. 28:13) Ba zai yi kyau ba mu ci gaba da mummunan tafarki kuma mu riƙa “ɓata zuciyar Ruhu Mai-tsarki na Allah.” (Afis. 4:30) Kuna da hakki a gaban Allah da iyayenku, da kuma kanku ku yi ikirarin zunubanku. Game da wannan “dattiɓan ikilisiya” suna iya taimaka muku sosai. Almajiri Yaƙub ya ce: “Su yi addu’a a bisansa [mai zunubi], suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji: addu’ar bangaskiya kuwa za ta ceci mai-ciwo, Ubangiji kuwa za ya tashe shi; idan kuma ya yi zunubai, za a gafarta masa.” (Yaƙ. 5:14, 15) Hakika, hakan yana iya sa ku ji kunya da kuma wataƙila wasu sakamako da ba su da daɗi. Amma, idan kuna da gaba gaɗi ku nemi taimako, za ku guji wasu lahani kuma ku samu sauƙi da ake samu don kasancewa da lamiri mai kyau.—Zab. 32:1-5.

Ku Faranta Zuciyar Jehobah

19, 20. Mene ne Jehobah yake son ku samu, kuma mene ne dole ne ku yi?

19 Jehobah “Allah ne mai [farin ciki]” kuma yana son ku yi farin ciki. (1 Tim. 1:11) Yana damuwa da ku sosai. Ko idan ba wani da yake lura da ƙoƙarin da kuke yi don ku yi abin da yake da kyau, shi yana lura da hakan. Babu abin da yake a ɓoye a idanun Jehobah. Yana kallo ba don ya nemi laifi ba, amma don ya tallafa wa ƙoƙarce-ƙoƙarcenku na yin abu mai kyau. “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.”—2 Laba. 16:9.

20 Saboda haka, ku bar Kalmar Allah ta yi muku ja-gora, kuma ku yi amfani da shawararta. Ta hakan za ku samu hikima da fahimi da kuke bukata don ku sha kan matsaloli masu wuya kuma ku tsai da shawarwari masu wuya a rayuwa. Ba za ku faranta zuciyar iyayenku da na Jehobah kaɗai ba, amma za ku more rayuwa na farin ciki.

[Hasiya]

a An canja sunayen.

Yaya Za Ka Amsa?

• Mene ne matasa za su iya yi don su jimre da kuma amfana daga dokoki da kuma gyara da iyayensu suke musu?

• Me ya sa yake da muhimmanci ku kasance da daidaitaccen ra’ayi game da kuɗi?

• Ta yaya za ku kasance da aminci ga Jehobah sa’ad da kuka kaɗaita?

[Hoton da ke shafi na 6]

Za ku kasance da aminci ga Allah sa’ad da kuka kaɗaita?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba