Alheri Yana Kawar da Fushi
WASU shaidu biyu ma’aurata da ke ƙasar Holan masu suna George da Manon suna son su yi wa wata tsohuwa mai suna Rie wa’azi game da Mulkin Allah, amma tsohuwar ba ta da fara’a. An gaya musu cewa ta yi rashin magidanta biyu da kuma ɗanta kuma tana ciwon sanyin ƙashi mai tsanani. Ko da yake ta saurare su sa’ad da suke mata wa’azi, amma ba ta yi fara’a ba.
Amma, George ya gaya wa Manon cewa su kai wa matar kwandon furanni domin yana ganin ta kaɗaita kuma tana baƙin ciki. Rie ta yi farin ciki sosai sa’ad da suka yi hakan. Amma, lokacin da suka kai ziyarar bai dace mata ba, sai suka sa ranar da za su sake komawa. Sa’ad da George da Manon suka koma a ranar da suka shirya, ba su tarar da matar a gida ba. Ko da yake sun ci gaba da koma wurinta a lokatai dabam-dabam, amma ba su same ta ba. Har suka soma tunani cewa ba ta son su tattauna da ita.
Wata rana, George ta same Rie a gida. Sai ta ba shi haƙuri kuma ta bayyana cewa an kwantar da ita a asibiti ne shi ya sa ba sa ganinta. Ta ce: “Kun san abin da ya faru bayan kuka tafi? Na soma karanta Littafi Mai Tsarki!” Sai ya tattauna da ita kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita.
Yayin da take nazarin Littafi Mai Tsarki sai ta daina baƙin ciki kuma ta soma farin ciki. Ko da yake ba ta iya fita waje, amma nan da nan ta soma yi wa waɗanda suke ziyararta wa’azi. Rashin lafiya bai ƙyale ta ta halarci tarurrukan ikilisiya a kai a kai, duk da haka tana farin ciki sa’ad da ’yan’uwa suka kai mata ziyara. A ranar da ta kai shekara 82, ta halarci taron da’ira kuma aka yi mata baftisma don ta nuna ta keɓe kanta ga Allah.
Bayan ’yan watanni da ta rasu, sai aka ga waƙar da ta rubuta. A cikin waƙar, ta kwatanta baƙin cikin kaɗaici sa’ad da mutum ya yi tsufa kuma ta nanata muhimmanci nuna alheri. Manon ta ce: “Karanta wannan waƙar ya taɓa zuciyata sosai, kuma ina farin ciki sosai cewa Jehobah ya taimaka mana mu yi mata alheri.”
Hakika, misalin da Jehobah ya nuna mana ya motsa mu mu riƙa nuna irin wannan ƙauna da alheri. (Afis. 5:1, 2) Hidimarmu za ta ba da amfani idan muna nuna kanmu ‘masu-hidimar Allah ta yin kirki.’—2 Kor. 6:4, 6.