Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 6/15 pp. 25-29
  • ‘Ruhu Mai Tsarki ne Ya Motsa Su’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ruhu Mai Tsarki ne Ya Motsa Su’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TA YAYA ‘RUHU MAI-TSARKI YA MOTSA SU?’
  • DALILAI NA GASKATA CEWA LITTAFI MAI TSARKI DAGA ALLAH NE
  • ABUBUWAN DA SUKA SA MUTANE DA YAWA SUKA BA DA GASKIYA
  • “MAGANARKA FITILLA CE GA SAWAYENA”
  • Littafi Mai Tsarki Sako Ne Daga Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Hikima Cikin “Maganar Allah”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Koya Mana Game da Mawallafinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 6/15 pp. 25-29

‘Ruhu Mai Tsarki ne Ya Motsa Su’

“Ba a taɓa kawo kowane annabci bisa ga nufin mutum ba: amma mutane suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” —2 BIT. 1:21.

ABUBUWAN DA ZA KA YI TUNANI A KAI

Ta yaya ne Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya sa marubutan Littafi Mai Tsarki su san abin da za su rubuta?

Waɗanne dalilai ne suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki hurare ne daga wurin Allah?

Mene ne za mu iya yi kullum don mu nuna cewa muna godiya da aka ba mu Littafi Mai Tsarki?

1. Me ya sa muke bukatar Littafi Mai Tsarki?

MUTANE da yawa a duniya suna yin waɗannan tambayoyin: Daga ina muka fito? Me ya sa muka zo duniya? Mene ne zai faru da mu a nan gaba? Mene ne yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu? Me ya sa duniya ta lalace haka? Da ba mu da Littafi Mai Tsarki, ba za mu san amsoshin waɗannan tambayoyin ba. Da a ce ba mu da Littafi Mai Tsarki, da za mu riƙa yin amfani da fahiminmu ne kawai don amsa tambayoyinmu. Kuma da a ce muna yin amfani da fahiminmu ne kawai, da ba za mu ji kamar yadda marubucin zabura ya ji game da “shari’a ta Ubangiji” ba.—Karanta Zabura 19:7.

2. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da daraja Littafi Mai Tsarki?

2 Abin baƙin ciki ne cewa mutane da yawa ba sa son koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai kamar yadda suke yi sa’ad da suka fara koya game da Allah. (Gwada Ru’ya ta Yohanna 2:4.) Sun daina faranta wa Jehobah rai. (Isha. 30:21) Bai kamata mu ƙyale hakan ya faru mana ba. Ya kamata mu ci gaba da daraja Littafi Mai Tsarki da kuma koyarwarsa. Littafi Mai Tsarki baiwa ne mai tamani daga Mahaliccinmu mai ƙauna. (Yaƙ. 1:17) Mene ne zai taimaka mana mu yi ƙaunar “maganar Allah” sosai? Ya kamata mu yi tunani a kan yadda aka yi amfani da mazaje don rubuta Littafi Mai Tsarki. Kuma ya kamata mu yi tunani a kan wasu dalilai da suka sa muka gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. Yin haka zai taimaka mana mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma mu yi amfani da darasin da muka koya.—Ibran. 4:12.

TA YAYA ‘RUHU MAI-TSARKI YA MOTSA SU?’

3. Ta yaya aka “motsa” marubutan Littafi Mai Tsarki da ruhu mai tsarki?

3 Mazaje 40 da Allah ya motsa su da “Ruhu Mai-tsarki” sun rubuta Littafi Mai Tsarki cikin shekaru 1,610. Sun soma rubutun daga shekara ta 1513 kafin zamanin Yesu zuwa shekara ta 98 a zamanin Yesu. (Karanta 2 Bitrus 1:20, 21.) Sa’ad da muka karanta cewa ‘Ruhu Mai-tsarki ne ya motsa’ marubutan Littafi Mai Tsarki, hakan yana nufin cewa Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya gaya wa marubutan abin da za su rubuta da kuma yi musu ja-gora. Saboda haka, sun rubuta abin da Allah yake so ba ra’ayinsu ba. A wasu lokatai, waɗannan annabawa da marubuta ba su fahimci abin da suka annabta ko kuma rubuta ba. (Dan. 12:8, 9) Mun amince sosai cewa “kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne. Babu ra’ayin ’yan Adam a ciki.—2 Tim. 3:16.

4-6. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa marubutan Littafi Mai Tsarki su san abin da za su rubuta? Ka ba da misali.

4 Amma ta yaya Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya bayyana wa marubutan Littafi Mai Tsarki abin da za su rubuta? Shin an faɗar musu abin da za su rubuta ne dalla-dalla, ko kuwa an taƙaita musu abin da za su rubuta ne? Ka yi la’akari da yadda shugaban aiki yake rubuta wasiƙa. Sa’ad da yake son ya rubuta wasiƙar dalla-dalla, zai iya rubutawa da kansa ko kuma ya faɗa wa sakatarensa abin da zai rubuta. Sai sakataren ya rubuta wasiƙar kuma shugaban aikin ya sa hannu a wasiƙar. A wasu lokatai kuma, zai taƙaita masa abin da zai rubuta kawai, sai sakataren ya yi amfani da kalmominsa don rubuta wasiƙar. Bayan haka, shugaban aikin zai iya sake duba wasiƙar ko sakataren ya yi kuskure, idan ya yi hakan, sai ya nuna masa gyaran da zai yi. A ƙarshe, sai shugaban aikin ya sa hannu a wasiƙar. Kuma duk mutumin da aka aika wa wasiƙar zai san cewa shugaban aikin ne ya aiko da wasiƙar.

5 Hakazalika, Allah ne da kansa ya rubuta wasu sashe na Littafi Mai Tsarki. (Fit. 31:18) Sa’ad da Jehobah yake son a yi rubutu dalla-dalla, ya gaya wa marubutan kalmomin da za su rubuta. Alal misali, a littafin Fitowa 34:27, Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Ka rubuta waɗannan zantattuka: gama bisa ga azancin waɗannan zantattuka na yi alkawari tare da kai da Isra’ila kuma.’ Hakazalika, Jehobah ya gaya wa annabi Irmiya: ‘Ka rubuta dukan zancen da na yi maka a cikin wani littafi.’—Irm. 30:2.

6 Amma a yawancin lokatai, Allah bai gaya wa marubutan Littafi Mai Tsarki kalmomin da za su rubuta dalla-dalla ba. Maimakon haka, Allah ya saka abin da yake son su rubuta a cikin zuciyarsu, sai ya ƙyale su su rubuta su da kalmominsu. Littafin Mai-Wa’azi 12:10 ya ce: “Abin da Mai-wa’azi ya nema ke nan, ya sami magana masu-daɗin ji, da abin da aka rubuta daidai, kalmomin gaskiya ke nan.” Luka kuma ya ‘bi diddigin abubuwa duka daidai, ya rubuta bi da bi.’ (Luk 1:3) Allah ya yi amfani da ruhunsa don tabbatar cewa ’yan Adam ajizai ba su canja saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba.

7. Me ya sa yadda Jehobah ya ƙyale ’yan Adam su rubuta Kalmarsa abin hikima ne sosai?

7 Yadda Jehobah ya yi amfani da mutane don rubuta Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yana da hikima sosai. Mun fahimci kalmomin da suka rubuta sosai kuma mun fahimci yadda suke ji. Ka yi la’akari da wannan. Da a ce Jehobah ya yi amfani da mala’iku don rubuta Littafi Mai Tsarki fa? Da za su iya bayyana yadda ’yan Adam suke ji? Kamar jin tsoro da yin baƙin ciki da kuma yin sanyin gwiwa? Kalmar Allah tana motsa mu domin Jehobah ya ƙyale mutane su yi amfani da kalmominsu don su rubuta Littafi Mai Tsarki.

DALILAI NA GASKATA CEWA LITTAFI MAI TSARKI DAGA ALLAH NE

8. Me ya sa za mu iya cewa Littafi Mai Tsarki ya fita dabam da sauran littattafan addinai?

8 Muna da dalilai da yawa da za su sa mu gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. Ba za a iya haɗa Littafi Mai Tsarki da littattafan wasu addinai ba domin yana sa mu san Allah na gaskiya. Alal misali, littattafan addinin Hindu sun faɗi labarin bukukuwansu da ilimin falsafarsu da ƙagensu da kuma ɗabi’arsu. Littattafan addinin Buddhawa sun bayyana dokokin da ya kamata sufaye da mata masu-zaman zuhudu su bi. Sun kuma Bayyana koyarwar Buddhawa da kuma koyarwa game da Buddha. Buddha bai ce shi Allah ba ne, bai yi kalami da yawa game da Allah ba. Littattafan addinin Confucian ya yi magana game da abubuwan da suka faru a zamanin dā da ɗabi’a da tsafi da kuma waƙoƙi. Littafin da Musulmai suke amfani da shi ya koyar cewa Allah makaɗaici ne, ya san abin da zai faru a nan gaba kuma ya ƙaddara dukan abubuwan da za su faru, amma bai faɗa sunan Allah Jehobah ba. A cikin Littafi Mai Tsarki, sunan nan ya bayyana sau da yawa.

9, 10. Mene ne za mu iya koya game da Allah a cikin Littafi Mai Tsarki?

9 Littattafan addinai da yawa ba sa koyar da abubuwa da yawa game da Allah. Amma Littafi Mai Tsarki yana taimaka mana mu san Jehobah Allah da kuma dukan abin da yake yi. Yana kuma taimaka mana mu fahimci halayen Allah. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa shi Allah ne mai shari’a da hikima da kuma iko sosai. Ya kuma koyar mana ce shi Allah ne mai ƙauna. (Karanta Yohanna 3:16; 1 Yohanna 4:19.) Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (A. M. 10:34, 35) An fassara Littafi Mai Tsarki zuwa harsuna da yawa. Hakan ya nuna cewa Allah ba mai-tara ba ne. An fassara rabin Littafi Mai Tsarki ko kuma gabaki ɗaya zuwa harsuna 2,400. Saboda haka, kusan kowa a duniya zai iya karanta Littafi Mai Tsarki a nasa yaren.

10 Yesu ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.” (Yoh. 5:17) “Tun fil’azal [Jehobah] ne Allah har abada.” Saboda haka, ka yi la’akari da dukan abin da Jehobah ya cim ma. (Zab. 90:2) Littafi Mai Tsarki ne kaɗai ya gaya mana abin da Allah ya yi a dā, da abin da yake yi yanzu da kuma abin da zai yi a nan gaba. Littafi Mai Tsarki ya kuma gaya mana abin da yake so da abin da ba ya so, kuma ya gaya mana abin da za mu yi don mu kusace shi. (Yaƙ. 4:8) Bai kamata mu ƙyale biɗe-biɗe na rayuwa su hana mu bauta wa Jehobah ba.

11. Wace shawara mai kyau ce Littafi Mai Tsarki take ba mu?

11 Hikimar da ke Littafi Mai Tsarki ta nuna mana cewa littafi ne daga wurin Allah. Manzo Bulus ya rubuta: “Wanene ya gane nufin Ubangiji, da zai koya masa?” (1 Kor. 2:16) Ayar ta yi daidai da abin da annabi Ishaya ya tambayi mutane na zamaninsa: “Wanene ya gwada ruhun Ubangiji, wanene kuwa ya zama mai-ba shi shawara har ya koya masa?” (Isha. 40:13) Amsar ita ce babu kowa. Shi ya sa muke samun sakamako mai kyau idan mun bi shawarar Littafi Mai Tsarki game da yin aiki tuƙuru da aure da yara da nishaɗi da yin gaskiya da ɗabi’a da kuma abokan da muka zaɓa. Ba za mu taɓa samun shawara marar kyau daga Littafi Mai Tsarki ba. Amma, shawarar da ’yan Adam suke bayarwa ba ta yawan yin nasara. (Irm. 10:23) Sukan yi gwara ga shawararsu idan sun gano cewa bai yi daidai ba. Littafi Mai Tsarki ya ce ‘tunanin ’yan Adam banza’ ne.—Zab. 94:11.

12. Yaya mutane suka yi ƙoƙari su halaka Littafi Mai Tsarki?

12 Tarihi ya kuma sa mu gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. A shekaru da yawa da suka shige, mutane sun yi ƙoƙari su halaka Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 168 kafin zamanin Yesu, sarkin ƙasar Siriya mai suna, Antiochus na Huɗu ya ba da umurni cewa a tattara littattafan Doka kuma a ƙona su. A shekara ta 303 kafin zamanin Yesu, sarkin ƙasar Roma Diocletian ya ba da umurni cewa a halaka wuraren taro na Kirista kuma a ƙone Nassosinsu. An ci gaba da wannan halakar har kusan shekara goma. Bayan ƙarni na 11, paparuma sun yi ƙoƙari su hana a riƙa fassara Littafi Mai Tsarki domin ba sa son mutane su samu ilimi na Littafi Mai Tsarki. Duk da ƙoƙarin da Shaiɗan da kuma mabiyansa suka yi, ba su iya halaka Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya ba. Jehobah bai ƙyale ’yan Adam su halaka kyautar da ya ba mutane ba.

ABUBUWAN DA SUKA SA MUTANE DA YAWA SUKA BA DA GASKIYA

13. Waɗanne dalilai ne za su sa mu gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga Allah ne?

13 Akwai wasu dalilai kuma da suka sa mu gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. Littafi Mai Tsarki bai da saɓani a cikinsa, ya jitu da kimiyya, annabce-annabcensa daidai ne, kuma marubutan sa suna da gaskiya. Littafi Mai Tsarki yana kuma da iko ya gyara rayuwar mutane, abin da ya faɗa game da nan gaba gaskiya ne kuma ya ba da amsa mai kyau ga tambayoyin da aka yi a sakin layi na 1. Ka yi la’akari da abin da ya taimaki wasu su gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga Allah ne.

14-16. (a) Mene ne ya sa wasu mutane uku suka gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne? (b) Me za ka so ka faɗa sa’ad da kake wa’azi don mutane su gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne?

14 Anwara wani Musulmi ya yi girma a wata ƙasa a Gabas ta Tsakiya. Sa’ad da yake zama a Kudancin Amirka, sai Shaidun Jehobah suka ziyarce shi. Anwar ya ce: “A lokacin ba na son Kiristoci saboda miyagun abubuwa da suka yi a dā. Amma na amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni domin ina son koyon sabon abu.” Ba da daɗewa ba, sai Anwar ya koma ƙasarsu kuma bai ga Shaidu kuma ba. Bayan ’yan shekaru, sai ya koma ƙasar Turai kuma ya sake soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Sai ya ce: “Na gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga Allah ne domin annabce-annabcensa sun cika, tana da jigo guda, ba ta ƙaryata kanta kuma bayin Jehobah suna ƙaunar juna.” Sai Anwar ya yi baftisma a shekara ta 1998.

15 Asha ’yar shekara 16 ce, kuma iyayenta ’yan addinin Hindu ne. Ta ce: “A dā ina addu’a sa’ad da nake wurin bauta ko kuma nake da matsaloli kawai. Amma ba na tuna da Allah sa’ad da ba ni da matsaloli.” Amma wata rana, sai Shaidun Jehobah suka yi wa Asha wa’azi kuma sai ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Kuma sai ta zama aminiyar Allah. Mene ne ya tabbatar mata cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki? Ta ce: “Na samu amsoshin dukan tambayoyin da na yi a cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma Littafi Mai Tsarki ya sa na kasance da imani ba tare da na je haikalin ’yan Hindu ba ko kuma na bauta wa gumaka.”

16 Iyayen Paula ’yan cocin Katolika ne. Amma sa’ad da ta yi girma, ba ta tabbata cewa Allah ya wanzu da gaske ba. Akwai wani abu da ya faru. Ta ce: “Na ga wani abokina da ya daɗe ba mu haɗu ba. Kuma a lokacin, ana yayin barin sumar kai ya yi girma sosai da kuma shan ƙwaya. Amma, ya fita dabam. Ya haske sumarsa, ya yi gyaran fuska kuma yanzu yana farin ciki. Sai na tambaye shi dalilin hakan da kuma inda ya je. Ya gaya mini cewa yana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, sai ya yi mini wa’azi bayan haka.” Yadda Littafi Mai Tsarki ya sa wannan mutumin ya yi gyara a rayuwarsa ta sa Paula ta so Littafi Mai Tsarki kuma ta soma amince cewa Allah ne ya hure shi.

“MAGANARKA FITILLA CE GA SAWAYENA”

17. Wane sakamako za ka samu idan kana karanta da kuma yin bimbini a kan Kalmar Allah?

17 Littafi Mai Tsarki baiwa ne mai kyau da Jehobah ya ba mu ta wajen ruhunsa mai tsarki. Idan kana jin daɗin karanta shi kullum, za ka yi ƙaunar Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. (Zab. 1:1, 2) Ka riƙa yin addu’a cewa Allah ya ba ka ruhunsa a duk lokacin da kake son ka karanta Littafi Mai Tsarki domin ka fahimci abin da za ka karanta. (Luk 11:13) Maganar Allah ce ke cikin Littafi Mai Tsarki. Idan ka yi bimbini a kan abin da ka karanta, za ka riƙa tunani kamar Allah.

18. Me ya sa kake son ka ci gaba da koyo daga Littafi Mai Tsarki?

18 Yayin da kake daɗa koyon gaskiya ta Littafi Mai Tsarki, ka yi amfani da abin da ka koya. (Karanta Zabura 119:105.) Za a iya kwatanta karanta Littafi Mai Tsarki da kallon madubi. Idan ka ga cewa kana bukatar yin gyara, kada ka yi jinkirin yin hakan. (Yaƙ. 1:23-25) Kalmar Allah tana kama da takobi. Za ka iya yin amfani da ita don kāre abin da ka gaskata. Za ka kuma iya yin amfani da shi don cire koyarwar ƙarya daga zukatan mutane. (Afis. 6:17) Yayin da kake yin amfani da shi, ka yi godiya cewa “Ruhu Mai-tsarki” ne ya motsa marubutan Littafi Mai Tsarki.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

[Bayanin da ke shafi na 29]

Ka karanta Littafi Mai Tsarki kullum, kuma za ka yi ƙaunar Allah sosai

[Hoto a shafi na 26]

Mutumin da akwai sa hannunsa a wasiƙa ne ya rubuta wasiƙar

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba