Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kr babi na 17 pp. 182-191
  • Yadda Ake Koyar da Masu Hidimar Mulkin

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Ake Koyar da Masu Hidimar Mulkin
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ina Faɗin Waɗannan Magana Yadda Uba Ya Koya Mani”
  • Yadda Ake Koyar da ’Yan’uwa Su Zama Masu Bishara
  • Yadda Ake Koyar da ’Yan’uwa Maza Su Yi Ayyuka na Musamman
  • Makarantu na Ƙungiyar Jehobah—Tabbaci Ne Cewa Jehobah Yana Ƙaunarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Shin Kana Koyon Dukan Abin da Za Ka Iya Koya Daga Wurin Jehobah?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Wace Makaranta Ce Aka Shirya don Majagaba?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Ku Nemi Ilimi Daga Wurin Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Mulkin Allah Yana Sarauta!
kr babi na 17 pp. 182-191

BABI NA 17

Yadda Ake Koyar da Masu Hidimar Mulkin

MANUFAR WANNAN BABIN

Yadda makarantu na ƙungiyar Jehobah suke shirya masu hidimar Mulkin su yi hidimarsu da kyau

1-3. Ta yaya Yesu ya yaɗa bishara, kuma waɗanne tambayoyi za mu yi?

YESU ya yi wa’azi a Galili har tsawon shekaru biyu. (Karanta Matta 9:35-38.) Ya je birane da ƙauyuka da dama, yana koyarwa a cikin majami’u kuma yana wa’azin bishara game da Mulkin Allah. A duk inda Yesu ya yi wa’azi, jama’a sun bi shi. Yesu ya lura cewa “girbi hakika yana da yawa,” amma ana bukatar ƙarin ma’aikata.

2 Yesu ya yi shiri don a yi wannan wa’azin sosai. Ta yaya ya yi hakan? Ta wajen aika manzanni 12 “su yi wa’azin mulkin Allah.” (Luk 9:1, 2) Wataƙila manzannin sun yi tunani a kan yadda za su iya cika aikin. Amma kafin Yesu ya ce su soma aikin, ya koyar da su kamar yadda Ubansa na sama ya koyar da shi.

3 Hakan zai sa mu yi wasu tambayoyi kamar: Mene ne Uban ya koya wa Yesu? Mene ne Yesu ya koya wa manzanninsa? Kuma ta yaya Yesu, Sarkin Mulkin Allah yake koyar da mabiyansa a yau don su cika hidimarsu?

“Ina Faɗin Waɗannan Magana Yadda Uba Ya Koya Mani”

4. A yaushe ne Jehobah ya koyar da Yesu, kuma a ina ya yi masa koyarwar?

4 Yesu ya bayyana sarai cewa Ubansa ne ya koyar da shi. A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, ya ce: “Ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.” (Yoh. 8:28) A yaushe ne aka koyar da Yesu, kuma a ina? Babu shakka, an soma koyar da Ɗan fari na Allah nan da nan bayan an halicce shi. (Kol. 1:15) Ɗan ya yi shekaru da yawa a sama yana saurara da kuma lura da abin da Mai Koyarwa Mai Girma yake yi. (Isha. 30:20) A sakamakon haka, Ɗan ya koyi halaye da ayyuka da kuma nufin Ubansa sosai.

5. Wane umurni ne Uban ya ba Ɗansa game da hidimar da zai yi a duniya?

5 Da sannu-sannu, Jehobah ya koya wa Ɗansa yadda zai yi hidima a duniya. Ka yi la’akari da wani annabci da ya bayyana dangantakar da ke tsakanin Mai Koyarwa Mafi Girma da kuma Ɗansa na fari. (Karanta Ishaya 50:4, 5.) Annabcin ya ce Jehobah yakan tayar da Ɗansa “safiya kan safiya.” Wannan annabcin ya misalta Jehobah da malamin da ke tayar da ɗalibinsa daga barci kowace safiya don ya koyar da shi. Wani littafin bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar dai Jehobah . . . ya sa shi a makaranta, ya koya masa yadda zai yi wa’azi da kuma abin da zai yi wa’azi a kai.” A wannan “makarantar” da ke sama, Jehobah ya koya wa Ɗansa ‘abin da zai faɗa da maganar da zai yi.’ (Yoh. 12:49) Uban ya kuma ba Ɗansa umurni a kan yadda zai koyar da mutane.a Sa’ad da Yesu yake duniya, ya bi umurnin da Ubansa ya ba shi ta wajen cika hidimarsa kuma ya koyar da mabiyansa su cika hidimarsu.

6, 7. (a) Mene ne Yesu ya koya wa manzanninsa, kuma mene ne hakan ya shirya su su yi? (b) Wace koyarwa ce Yesu ya tabbata cewa mabiyansa suna mora a yau?

6 Mene ne Yesu ya koya wa manzanninsa kamar yadda aka ambata ɗazu? Littafin Matta sura 10 ta ce Yesu ya ba su takamaiman umurni game da yadda za su yi wa’azi kuma hakan ya haɗa da umurni game da: inda za su yi wa’azi (ayoyi na 5 da 6), abin da za su yi wa’azi a kai (aya ta 7), muhimmancin dogara ga Jehobah (ayoyi na 9 da 10), yadda za su gabatar da wa’azinsu (ayoyi na 11-13), yadda za su bi da mutanen da ba su saurare su ba (ayoyi na 14 da 15), da kuma abin da za su yi sa’ad da aka tsananta musu (ayoyi na 16-23).b Wannan koyarwar da Yesu ya yi wa manzanninsa kai tsaye ta taimaka musu su yi ja-gora a yin wa’azi a ƙarni na farko.

7 A yau kuma fa? Yesu Kristi wanda shi ne Sarkin Mulkin Allah, ya ba mabiyansa aiki mafi girma, wato yin bishara “ta mulki . . . ga dukan al’ummai.” (Mat. 24:14) Shin Sarkin ya koya mana yadda za mu yi wannan aikin? Ƙwarai kuwa! Sarkin ya tabbata cewa an koya wa mabiyansa yadda za su yi wa’azi ga mutane da kuma yadda za su gudanar da ayyuka na musamman a cikin ikilisiya. Ya cim ma dukan waɗannan abubuwan daga sama.

Yadda Ake Koyar da ’Yan’uwa Su Zama Masu Bishara

8, 9. (a) Mene ne ainihin manufar Makarantar Hidima ta Allah? (b) Ta yaya Makarantar Hidima ta Allah ta taimaka maka ka ƙware a hidima sosai?

8 Ƙungiyar Jehobah ta daɗe tana yin amfani da manyan taro da kuma taron ikilisiya, kamar Taron Hidima don koya wa bayin Allah yadda za su yi wa’azi. Amma daga shekara ta 1940 zuwa 1949, ’yan’uwa masu ja-gora a hedkwata sun soma yin amfani da makarantu dabam-dabam don a koyar masu wa’azi.

9 Makarantar Hidima ta Allah. Kamar yadda muka tattauna a babin da ya gabata, an soma makarantar nan ne a shekara ta 1943. Shin an kafa wannan makarantar ne don kawai a koya wa ’yan’uwa yin jawabai masu ƙayatarwa a taron ikilisiya? A’a. Ainihin manufar makarantar a dā da kuma yanzu ita ce koyar da bayin Allah su yi amfani da furucinsu wajen yabon Jehobah sa’ad da suke yin wa’azi. (Zab. 150:6) Makarantar tana koyar da dukan ’yan’uwa maza da mata don su kyautata yadda suke yin wa’azin Mulkin.

10, 11. Su waye ne za su iya zuwa Makarantar Gilead yanzu, kuma mene ne manufar makarantar?

10 Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. An soma makarantar a ranar 1 ga Fabrairu, 1943. An kafa makarantar ne asali don a koyar da majagaba da kuma wasu masu hidima ta cikakken lokaci don su yi wa’azi a ƙasashen waje. Amma daga watan Oktoba na 2011, waɗanda ake gayyata zuwa makarantar su ne: ’Yan’uwan da ke hidimar majagaba ta musamman da masu kula masu ziyara da matansu da masu hidima a Bethel da kuma masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su halarci makarantar ba tukun.

11 Mene ne manufar Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead? Wani ɗan’uwa da ya daɗe yana koyarwa a makarantar ya ce: “Ana so ne a ƙarfafa bangaskiyar ɗaliban ta wajen nazarin Kalmar Allah sosai kuma a taimaka musu su kasance da halayen da za su taimaka musu su shawo kan ƙalubalen da za su fuskanta a hidimarsu. Wani dalili na musamman kuma da ya sa aka kafa makarantar shi ne don a taimaka wa ɗaliban su yi marmarin yin wa’azi.”—Afis. 4:11.

12, 13. Ta yaya makarantar Gilead ta taimaka a yin wa’azi a faɗin duniya? Ka ba da misali.

12 Ta yaya Makarantar Gilead ta taimaka wajen yin wa’azi a faɗin duniya? Tun shekara ta 1943, ɗalibai sama da 8,500 sun sauke karatu daga makarantar,c kuma sun yi wa’azi a sama da ƙasashe 170 a faɗin duniya. Masu wa’azi a ƙasashen waje sun yi amfani da koyarwar da aka yi musu ta wajen yin hidima da ƙwazo kuma sun koya wa wasu su yi hakan. A yawancin lokatai, ’yan’uwan ne suke ja-gora a yin wa’azi a yankunan da babu isashen masu shela ko kuma babu gaba ɗaya.

13 Ka yi la’akari da abin da ya faru a ƙasar Japan, inda aka daina yin wa’azi a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. Kafin watan Satumba na shekara ta 1949, masu shela da ke ƙasar baki ɗaya ba su kai goma ba. Amma a ƙarshen wannan shekarar, sai aka tura ’yan’uwa guda 13 da suka sauke karatu a Makarantar Gilead don su yi wa’azi a ƙasar Japan. Daga baya, aka daɗa tura wasu. Da farko, ’yan’uwan sun mai da hankali ga manyan birane, amma daga baya, sai suka koma wasu ƙananan birane. ’Yan’uwan sun ƙarfafa ɗalibansu da kuma wasu ’yan’uwa su soma hidimar majagaba. Shin sun sami sakamako mai kyau ne? Hakika! A yau, akwai masu shelar Mulki fiye da 216,000 a ƙasar Japan, kuma kusan kashi 40 cikin ɗari na masu shela majagaba ne!d

14. Wane tabbaci ne makarantun ƙungiyar Jehobah suke ba da? (Ka kuma duba akwatin nan “Makarantun Koyar da Masu Hidimar Mulki,” a shafi na 188.)

14 Wasu makarantu na ƙungiyar Jehobah. Makarantar Hidima ta Majagaba da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata da kuma Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure sun taimaka wa waɗanda suka halarta su kyautata dangantakarsu da Jehobah kuma su yi ja-gora a wa’azi.e Dukan waɗannan makarantun sun ba da tabbaci cewa Sarkinmu ya koyar da mabiyansa sosai domin su cika hidimarsu.—2 Tim. 4:5.

Yadda Ake Koyar da ’Yan’uwa Maza Su Yi Ayyuka na Musamman

15. A waɗanne hanyoyi ne ya kamata maza masu hakki a ƙungiyar Jehobah su yi koyi da Yesu?

15 Annabcin Ishaya da muka ambata ɗazu ya ce Allah ya koyar da Yesu. A wannan “makarantar” da ke sama, Ɗan ya koyi ‘abin da zai faɗa, domin ya iya ƙarfafa marar ƙarfi.’ (Isha. 50:4, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya yi amfani da wannan koyarwar sa’ad da yake duniya ta wajen taimaka wa dukan waɗanda suke ‘wahala da masu-nauyin kaya’ su sami kwanciyar rai. (Mat. 11:28-30) Ya kamata maza masu hakki a ƙungiyar Jehobah ma su yi koyi da Yesu ta wajen taimaka wa ’yan’uwansu maza da mata su sami kwanciyar rai. Domin a cim ma wannan burin, an kafa makarantu don a taimaka wa ’yan’uwa maza su ƙware sosai wajen yi wa ’yan’uwansu hidima.

16, 17. Mene ne manufar Makarantar Hidima ta Mulki? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

16 Makarantar Hidima ta Mulki. An soma aji na farko na wannan makarantar a ranar 9 ga Maris, 1959, a birnin South Lansing, a jihar New York. An gayyaci masu kula masu ziyara da kuma bayin ikilisiya (an kira su shugabannin ikilisiya daga baya) su halarci makarantar na tsawon wata ɗaya. Daga baya, an fassara abin da ake tattaunawa a ajin daga Turanci zuwa wasu harsuna, kuma an soma koyar da ’yan’uwa maza daga dukan faɗin duniya.f

Ɗan’uwa Lloyd Barry yana koyarwa a Makarantar Hidima ta Mulki a shekara ta 1970 a ƙasar Japan

Ɗan’uwa Lloyd Barry yana koyarwa a Makarantar Hidima ta Mulki a shekara ta 1970 a ƙasar Japan

17 Littafin nan 1962 Yearbook of Jehovah’s Witnesses ya yi wannan furucin game da manufar Makarantar Hidima ta Mulki: “A wannan duniyar da mutane suke a taƙure, ya wajaba masu kula a cikin ikilisiyar Shaidun Jehobah su zama mazajen da suka tsara salon rayuwarsu daidai wa daida domin su kula da kowa a cikin ikilisiya sosai. Bai kamata kuma su yi watsi da iyalansu domin suna so su kula da ikilisiya ba, amma ya kamata su kasance da sanin yakamata. Babban gata ne bayin ikilisiya a dukan duniya su halarci wannan Makarantar Hidima ta Mulki domin su koyi abubuwan da za su taimake su su cika hakkinsu bisa ga umurnin Littafi Mai Tsarki.”—1 Tim. 3:1-7; Tit. 1:5-9.

18. Ta yaya dukan bayin Allah suke amfana daga Makarantar Hidima ta Mulki?

18 Dukan bayin Jehobah sun amfana daga Makarantar Hidima ta Mulki. Ta yaya? Domin sa’ad da dattawa da bayi masu hidima suka yi amfani da abin da suka koya a makarantar, suna yin koyi da Yesu ta wajen sa ’yan’uwa su sami kwanciyar rai. Babu shakka, kana godiya sa’ad da dattijo ko bawa mai hidima ya ziyarce ka domin ya ƙarfafa ka ko ya yaba maka ko kuma ya saurare ka sosai, ko ba haka ba? (1 Tas. 5:11) Irin waɗannan mazan da suka ƙware albarka ne sosai ga ikilisiyarsu!

19. Waɗanne makarantu ne Kwamitin Koyarwa yake lura da su, kuma mene ne manufar makarantun?

19 Wasu makarantu na ƙungiyar Jehobah. Kwamitin Koyarwa na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne yake lura da makarantun nan da ke koyar da ’yan’uwa maza masu hakki a ƙungiyar Jehobah. An shirya waɗannan makarantun don su taimaki dattawan ikilisiya da masu kula masu ziyara da kuma mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe su cim ma ayyukansu da kyau. Koyarwa ta Littafi Mai Tsarki da ake tanadarwa a makarantun tana ƙarfafa waɗannan ’yan’uwa su ci gaba da kyautata dangantakarsu da Jehobah da kuma yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a yadda suke bi da tumakin da Jehobah ya ba su riƙo.—1 Bit. 5:1-3.

Aji na farko na Makarantar Koyar da Masu hidima a kasar Malawi

Aji na farko na Makarantar Koyar da Masu Hidima da aka yi a shekara ta 2007 a ƙasar Malawi

20. Me ya sa Yesu ya ce Jehobah ne yake ‘koyar’ da dukanmu, kuma mene ne ka ƙudura niyyar yi?

20 Hakika, Sarkin Mulkin Allah ya tabbata cewa an koyar da mabiyansa da kyau. Jehobah ne ya fara koyar da Ɗansa, kuma Ɗan ya koyar da mabiyansa. Shi ya sa Yesu ya ce Jehobah ne yake ‘koyar’ da dukanmu. (Yoh. 6:45; Isha. 54:13) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu amfana daga koyarwar da Sarkinmu yake tanadar mana, ko da ta hanyar Makarantar Hidima ta Allah ne ko wasu taron ikilisiya ko kuma sauran makarantun da aka tattauna a wannan babin. Kada mu manta cewa ainihin manufar waɗannan makarantun ita ce mu ci gaba da kyautata dangantakarmu da Jehobah domin mu yi hidimarmu da kyau.

a Ta yaya muka san cewa Uban ya koya wa Ɗansa yadda zai koyar da mutane? Ka yi la’akari da wannan: Yadda Yesu yake yawan yin amfani da kwatanci sa’ad da yake koyarwa ya cika wani annabci da aka yi shekaru da yawa kafin a haife shi. (Zab. 78:2; Mat. 13:34, 35) Babu shakka, Jehobah, Wanda ya sa aka yi annabcin, ya koya wa Ɗansa tun da wuri yadda zai yi amfani da kwatanci ko almara sa’ad da yake koyarwa.—2 Tim. 3:16, 17.

b ’Yan watanni bayan haka, Yesu ya tura wasu almajirai “saba’in, ya aike su biyu biyu” don su yi wa’azi. Kafin ya aike su, ya koyar da su.—Luk 10:1-16.

c Wasu sun halarci Makarantar Gilead fiye da sau ɗaya.

d Don ƙarin bayani a kan yadda ’yan’uwan da suka sauke karatu a Makarantar Gilead suka taimaka a yin wa’azi a faɗin duniya, ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, babi na 23.

e An mai da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata da kuma Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.

f A yau, dukan dattawa suna amfana daga Makarantar Hidima ta Mulki. Ana gudanar da wannan makarantar bayan ’yan shekaru kuma tsawon ajin yakan bambanta. Tun daga shekara ta 1984, bayi masu hidima ma sun amfana daga wannan makarantar.

Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?

  • Wace koyarwa ce Yesu ya samu daga Ubansa?

  • Ta yaya Sarkin ya koyar da mabiyansa su zama masu shelan bishara?

  • Ta yaya aka koyar da ’yan’uwa maza don su cika ayyukansu a ƙungiyar Jehobah?

  • Ta yaya za ka nuna cewa kana godiya don koyarwar da Sarkin ya tanadar?

MAKARANTUN KOYAR DA MASU HIDIMAR MULKI

MAKARANTAR HIDIMA TA ALLAH

Manufa: Don koyar da masu shela su ƙware wajen koyarwa da kuma yin wa’azin bishara.

Tsawo: Ba a sauke karatu.

Wuri: Majami’ar Mulki da ke yankin.

Yadda Ake Shiga: Dukan waɗanda suke halartan taro a kai a kai da suka amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma suna rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Idan kana so a ba ka aiki a makarantar, ka yi magana da dattijon da ke kula da makarantar.

Amfani: Wata ’yar makarantar mai suna Sharon da take fama da ciwon shanyewar jiki ta ce: “Makarantar Hidima ta Allah ta koya mini yin bincike da kuma bayyana abubuwa da basira. Makarantar ta taimake ni sosai, ƙari ga haka, ta sa in taimaki mutane su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.”

Wani mai suna Arnie da ya daɗe yana hidimar mai kula mai ziyara ya ce: “Ina in’ina tun ina ƙarami kuma sa’ad da nake magana, ba na iya kallon fuskar mutane. Amma, makarantar ta taimaka mini in kasance da gaba gaɗin yin magana a gaban mutane. Jehobah ya yi amfani da wannan makarantar don ya taimaka mini sosai. Yanzu ina yin magana ba tare da yin in’ina ba. Ina godiya sosai don ina yabon Allah a cikin ikilisiya da kuma sa’ad da nake wa’azi.”

Wani yaro yana karatunsa na farko a Makarantar Hidima ta Allah

MAKARANTA DON DATTAWAN IKILISIYAg

Manufa: Don taimaka wa dattawa su inganta yadda suke kula da ayyukansu a cikin ikilisiya kuma su kyautata dangantakarsu da Jehobah.

Tsawo: Kwana biyar.

Wuri: Ofishin reshe ne ke zaɓan wurin, kuma a yawancin lokatai, ana yin ta a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro.

Yadda Ake Shiga: Ofishin reshe ne ke gayyatar dattawa.

Amfani: Ga abin da ’yan’uwan da suka halarci aji na 92 a birnin Patterson, New York a ƙasar Amirka suka ce:

“Na amfana sosai daga makarantar don ta taimaka mini in sake bincika kaina domin in san yadda ya kamata in kula da tumakin Jehobah.”

“Wannan koyarwar za ta taimaka mini muddin raina.”

MAKARANTAR HIDIMA TA MAJAGABA

Manufa: Don taimaka wa majagaba su ‘cika hidimarsu’ da kyau.—2 Tim. 4:5.

Tsawo: Kwana shida.

Wuri: Inda ofishin reshe ya zaɓa; a yawancin lokatai a Majami’ar Mulki.

Yadda Ake Shiga: Ana gayyatar waɗanda suka yi aƙalla shekara ɗaya suna hidimar majagaba na kullum kuma mai kula da da’ira ne yake sanar da su. Ƙari ga haka, za a iya gayyatar wasu majagaba da suka yi shekara biyar da halartar makarantar.

Amfani: Wata ’yar’uwa mai suna Lily, ta ce: “Wannan makarantar ta taimaka mini na jimre da matsaloli da nake fuskanta a hidima da kuma a rayuwata. Makarantar ta kyautata yadda nake nazari da koyarwa da kuma yin amfani da Littafi Mai Tsarki. A yanzu, ina shirye in taimaka wa mutane, in goyi bayan dattawa, kuma in taimaka wa ikilisiya ta sami ƙaruwa.”

Brenda, wadda ta halarci makarantar sau biyu ta ce: “Makarantar ta taimaka mini in kasance da ƙwazo a hidimata ga Jehobah kuma ta inganta lamirina. Bugu da ƙari, ta sa na mai da hankali ga taimaka wa mutane. Hakika, Jehobah mai alheri ne!”

MAKARANTAR SABABBI MASU HIDIMA A BETHEL

Manufa: Don a taimaki sababbi su yi nasara a hidimarsu a Bethel.

Tsawo: Minti 45 a kowane mako har tsawon makonni goma sha shida.

Wuri: A Bethel.

Yadda Ake Shiga: Za a saka sunayen sababbin da suke hidima na dindindin da kuma na ɗan lokaci a Bethel (waɗanda suka yi shekara ɗaya ko fiye da hakan a Bethel).

Amfani: Wani mai suna Demetrius wanda ya halarci makarantar a wani lokaci tsakanin shekara ta 1980 da 1989 ya ce: “Wannan makarantar ta kyautata yadda nake nazari kuma ta shirya ni a hanyar da zan daɗe ina hidima a Bethel. Malaman makarantar da abubuwan da aka koya mana da kuma shawarwari masu kyau da aka ba mu sun sa na amince cewa Jehobah yana ƙaunata sosai kuma yana son ya taimaka mini na yi nasara a hidimata a Bethel.”

MAKARANTAR MASU YAƊA BISHARAR MULKIh

Manufa: Ana koyar da majagaba (marasa aure maza da mata da kuma ma’aurata) don Jehobah da kuma ƙungiyarsa su yi amfani da su sosai. Za a tura ’yan’uwa da yawa da suka sauke karatu su je inda ake bukatar masu shela sosai a ƙasarsu. Ana iya aika waɗanda ba su kai shekara 50 ba yin hidima a yankuna masu nisa a matsayin majagaba na musamman na ɗan lokaci domin su soma wa’azi ko kuma su faɗaɗa hidimar a wurin.

Tsawo: Wata biyu.

Wuri: Ofishin reshe ne ke zaɓa, kuma a yawancin lokaci, ana gudanar da makarantar a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro.

Wata ’yar’uwa tana wa’azi

’Yan’uwa suna amfana daga koyarwar ƙungiyar Jehobah

Yadda Ake Shiga: Majagaba na kullum da na musamman da ke tsakanin shekara 23 da 65, masu koshin lafiya, waɗanda za su iya yin hidima a inda ake da bukata sosai, masu halin sadaukarwa kamar Ishaya wanda ya ce “Ga ni; ka aike ni” za su iya cika afilkeshan. (Isha. 6:8) Wajibi ne ’yan’uwa maza da mata da kuma ma’aurata da suke so su shiga makarantar su kasance waɗanda suka yi hidima ta cikakken lokaci na aƙalla shekara biyu babu fashi. Wajibi ne ma’auratan su kasance waɗanda suka yi aƙalla shekara biyu da aure. Idan mai son shiga makarantar namiji ne, wajibi ne ya kasance dattijo ko kuma bawa mai hidima na aƙalla shekara biyu babu fashi. Idan ana yin wannan makarantar a yankinku, za a yi taro don waɗanda suke so su shiga wannan hidimar a taron yanki.

Amfani: Mutanen da suka halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata sun yaba wa waɗannan makarantun sosai. A shekara ta 2013, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta haɗa waɗannan makarantun su zama ɗaya kuma ana kiran ta Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Yanzu, majagaba da yawa za su amfana daga makarantar, har da ’yan’uwa mata marasa aure.

MAKARANTAR LITTAFI MAI TSARKI TA GILEAD

Manufa: Waɗanda suka sauke karatu daga makarantar za su iya zama masu kula masu ziyara ko masu wa’azi a ƙasashen waje ko kuma masu hidima a Bethel. Idan suka yi amfani da abin da suka koya sosai, za su ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiyoyi, kuma za su kyautata hidimar da ake yi a ofishin reshe.

Tsawo: Wata biyar.

’Yan Ajin Makarantar Koyar da Masu Hidima na Gilead suna sauraron malaminsu

Wani ajin Gilead a Patterson, New York

Wuri: A Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York.

Yadda Ake Shiga: Ma’aurata ko ’yan’uwa maza marasa aure ko ’yan’uwa mata marasa aure da suke hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su halarci makarantar ba ko majagaba na musamman ko masu kula masu ziyara ko kuma masu hidima a Bethel. Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah zai iya gaya wa ma’aurata su cika afilkeshan. Suna bukata su iya Turanci kuma su iya rubutawa.

Amfani: Lade da Monique, wasu ma’aurata a Amirka da suka yi shekaru suna hidima sun yi furucin da ke gaba:

Lade ya ce:“Makarantar ta shirya mu mu yi hidima a duk inda muka sami kanmu kuma mu kasance a shirye don mu iya yin aiki tare da ’yan’uwanmu.”

Monique ta ce: “Yayin da nake yin amfani da abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki, ina jin daɗin hidimata sosai. Kuma hakan ya nuna mini cewa Jehobah yana ƙaunata sosai.”

MAKARANTAR HIDIMA TA MULKI

Manufa: Don a koyar da masu kula masu ziyara da dattawa, kuma a wasu lokatai, bayi masu hidima don dukansu su gudanar da ayyukansu a hanyar da ta dace. (A. M. 20:28) Ana tattauna yanayin ikilisiya, yadda za a bi da abubuwan da za su iya tasowa da kuma bukatun ikilisiya. Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce za ta zaɓi lokacin da za a yi wannan makarantar bayan wasu shekaru.

Tsawo: A shekarun baya, an gudanar da makarantar a tsawon kwanaki dabam-dabam.

Wuri: A yawancin lokatai ana yi a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro.

Yadda Ake Shiga: Mai kula da da’ira zai sanar da dattawa da kuma bayi masu hidima. Ofishin reshe ne ke gayyatar masu kula masu ziyara.

Amfani: Wani ɗan’uwa mai suna Quinn, ya ce: “Ko da yake ana tattauna abubuwa da yawa cikin ɗan lokaci, makarantar tana taimaka wa dattawa su kasance da farin ciki yayin da suke gudanar da ayyukansu da gaba gaɗi. Waɗanda suka daɗe a matsayin dattawa da kuma sababbi suna koyan yadda ake ƙarfafa ’yan’uwa da kyau da kuma kasancewa da haɗin kai ‘da ra’ayi ɗaya.’”

Ɗan’uwa Michael, ya ce: “Wannan koyarwa ta taimaka mana mu fahimci abubuwan da suka shafi bangaskiyarmu sosai, kuma ta yi mana gargaɗi a kan haɗarurruka da za mu guje wa da kuma ba mu shawarwari masu kyau game da yadda za mu kula da ’yan’uwa.”

MAKARANTA DON MASU KULA MASU ZIYARA DA MATANSUi

Manufa: Don a taimaki masu kula masu ziyara su inganta yadda suke taimaka wa ikilisiyoyi kuma su kasance da ƙwazo sosai a “yin wa’azi da koyarwa.”—1 Tim. 5:17, Littafi Mai Tsarki; 1 Bit. 5:2, 3.

Tsawo: Wata biyu.

Wuri: Inda ofishin reshe ya zaɓa.

Yadda Ake Shiga: Ofishin reshe ne yake gayyatar masu kula masu ziyara da matansu.

Amfani: Ma’aurata Joel da Connie waɗanda suka halarci aji na farko, a shekara ta 1999, sun ce: “An taimaka mana mu daɗa kasancewa da godiya ga yadda Yesu yake shugabanci bisa ƙungiyar Jehobah. Mun koya cewa muna bukata mu ƙarfafa ’yan’uwan da muke ziyarta kuma mu sa ikilisiya ta ƙara kasancewa da haɗin kai. Makarantar ta koya mana cewa ko da yake mai kula da da’ira yakan ba da shawara kuma ya yi gyara a wasu lokatai, ainihin maƙasudinsa shi ne ya taimaka wa ’yan’uwa su san cewa Jehobah yana ƙaunarsu.”

MAKARANTA DON MAMBOBIN KWAMITIN DA KE KULA DA OFISHIN RESHE DA MATANSU

Manufa: Don a taimaka wa mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe su kula da gidajen Bethel da kuma batutuwan hidima da suka shafi ikilisiyoyi da da’irori a yankunansu.—Luk 12:48b.

Tsawo: Wata biyu.

Wuri: Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York, Amirka.

Yadda Ake Shiga: Kwamitin Hidima na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne yake gayyatar mambobin kwamitin da matansu.

Amfani: Lowell da Cara da suka sauke karatu a aji na 25 suna hidima a Najeriya yanzu.

Ɗan’uwa Lowell ya ce: “An tuna mini cewa ko da na shagala da aiki kuma ko da wane irin aiki ne aka ba ni, abin da zai taimaka mini in faranta wa Jehobah rai shi ne in ƙarfafa dangantakata da shi.”

Cara ta tuna da wani abin da ta koya a makarantar, kuma ta ce: “Idan ba zan iya bayyana wani batu a hanya mai sauƙi ba, hakan yana nufin cewa ina bukata in sake yin nazari a kan batun kafin in bayyana wannan batun ga wasu.”

g Ba a soma gudanar da makarantar a wasu ƙasashe ba tukun.

h Ba a soma gudanar da makarantar a wasu ƙasashe ba tukun.

i Ba a soma gudanar da makarantar a wasu ƙasashe ba tukun.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba