Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Afrilu pp. 8-13
  • Jehobah Yakan Cika Dukan Alkawuransa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yakan Cika Dukan Alkawuransa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DALILIN DA YA SA ZA MU IYA DOGARA GA JEHOBAH
  • ABIN DA JEHOBAH YAKE YI DON YA CIKA NUFINSA
  • JEHOBAH YANA JAWO MASU SON GASKIYA ZUWA WURINSA
  • MUNA DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI CIKA ALKAWARINSA
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira da Wakilin Reshen Ofishinmu na 2026
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Ka Dogara ga Jehobah Mai Iko Duka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Afrilu pp. 8-13

8-14 GA YUNI, 2026

WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu

Jehobah Yakan Cika Dukan Alkawuransa

“Ka fanshe ni, ya Yahweh Allah mai aminci.”—ZAB. 31:5.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga dalilin da ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kawo aljanna kamar yadda ya yi alkawari, da kuma cewa nan ba da jimawa ba, zai kawo ƙarshen ƙarairayi da Shaiɗan yake yaɗawa.

1. Bisa ga Zabura 31:​2-5, me ya sa za mu iya dogara ga Jehobah?

MUNA rayuwa a duniyar Shaiɗan inda mutane da yawa suke yin ƙarya da ruɗu da kuma cin amana. Da wuya a sami wanda za a iya amincewa da shi. ꞌYan kasuwa da yawa suna cucin mutane. Mutane da yawa suna yin ƙarya game da abin da suke sayarwa don kawai mutane su saya. A wasu lokuta ma, abokai ba sa riƙe alkawari da suka yi wa juna. Amma, abin farin ciki shi ne, za mu iya dogara ga Jehobah kullum. Me ya sa? Domin shi “Allah ne mai aminci.” (Karanta Zabura 31:​2-5.) Jehobah ba ya ƙarya, kuma duk abin da ya faɗa gaskiya ne.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A talifin nan, za mu soma da tattauna dalilan da suka sa za mu iya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu. Saꞌan nan za mu ga yadda Jehobah zai kawo ƙarshen duniyar Shaiɗan, da kuma abubuwan da Jehobah yake yi yanzu don ya cim ma nufinsa ga ꞌyanꞌadam. Waɗannan abubuwan da za mu tattauna, za su taimaka mana mu ci-gaba da gaya wa mutane gaskiya game da Jehobah babu tsoro.

DALILIN DA YA SA ZA MU IYA DOGARA GA JEHOBAH

3. Me ya sa za mu iya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu?

3 Za mu iya dogara ga Jehobah domin shi ne Mahalicci. Shi ne ya halicci sama da duniya da dukan abubuwa. (Far. 1:1; Zab. 36:9; R. Yar. 4:11) Ya halicci duniya yadda za mu iya samun kome da muke bukata don mu ci-gaba da yin rayuwa, kamar iskar da muke shaƙa, da kuma ruwan da muke sha. Shi ne mai iko duka. Da yake Jehobah ne ya halicce mu, ya san kome da kome, kuma ikonsa bai da iyaka. Don haka, za mu iya dogara gare shi, kuma mu kasance da tabbaci cewa zai ba mu abubuwa masu kyau a nan gaba.

4. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana ƙaunar mu?

4 Za mu iya dogara ga Jehobah domin yana ƙaunar mu. Jehobah ya halicci ꞌyanꞌadam domin yana so su ji daɗin rayuwa. Ya halicce mu a kamaninsa, wato mu kasance da halaye masu kyau irin nashi kamar ƙauna da kuma alheri. (Far. 1:26) Ya ba mu damar zaɓan abubuwan da muke so mu yi. Ya halicci duniya da kuma abubuwa masu kyau a ciki don mu ji daɗin su. (Zab. 115:16) Kuma ya ba iyayenmu na farko aikin mayar da duniya ta zama aljanna. (Far. 1:28; 2:15) Ya ba su abinci iri-iri, da itatuwa, da dabbobi, da dai sauran su don su ji daɗin rayuwa, kuma su yi farin ciki. Abubuwan nan da Jehobah ya yi, sun nuna cewa yana ƙaunar mu, kuma ƙaunarsa “marar farko marar ƙarshe ce.”—Zab. 103:17.

5. (a) Mene ne Jehobah ya yi saꞌad da Adamu da Hauwaꞌu suka yi masa rashin biyayya? (b) Waɗanne alkawura ne Allah ya cika? (Ka duba akwatin nan “Allah Yana Cika Alkawuransa.”)

5 Za mu iya dogara ga Jehobah domin yana cika alkawuransa. Jehobah bai “halicci duniya ta zama wofi ba, ya yi ta domin a zauna a cikinta.” (Isha. 45:​18, 19) Rashin biyayyar da Adamu da Hauwaꞌu suka yi ne ya sa suka mutu. Shin, hakan na nufin cewa Shaiɗan ya hana Jehobah cika nufinsa ga duniya? Aꞌa, babu wani abin da zai iya hana Jehobah yin abin da yake so. Yana cika duk alkawuran da ya yi. (Isha. 46:​10, 11) Har ila, yana so ꞌyanꞌadam su yi rayuwa har abada a duniya. Shi ya sa Jehobah ya bar Adamu da Hauwaꞌu su haifi ꞌyaꞌya. Kuma ya aiko Ɗansa ya zo ya ba da ransa domin mu sami begen yin rayuwa har abada.—Yoh. 3:16.

Allah Yana Cika Alkawuransa

Ka yi laꞌakari da wasu alkawuran da Jehobah ya yi kuma ya cika:

  • Ya yi wa Musa alkawari cewa za su zauna a ƙasar da ake samun abinci da yawa.—Fit. 3:​6-8; M. Sha. 27:3.

  • Ya yi alkawari cewa Almasihu zai zo ya ceci ꞌyanꞌadam daga zunubi da mutuwa.—Isha. 53:​11, 12.

  • Ya ce za a yi waꞌazi a duk faɗin duniya don a taimaka wa masu zuciyar kirki su zo su bauta masa kafin ƙarshe ya zo.—Mat. 24:14.

Shin, ka tuna da wasu alkawuran da Jehobah ya yi kuma ya cika su?

ABIN DA JEHOBAH YAKE YI DON YA CIKA NUFINSA

6. Mene ne Jehobah ya ce zai faru bayan Adamu da Hauwaꞌu suka yi masa tawaye?

6 Ainihin wanda ya sa Adamu da Hauwaꞌu su yi wa Allah tawaye shi ne, “dodo mai siffar macijin nan na tun dā, wanda ake ce da shi Mugun, ko kuma Shaiɗan.”a (R. Yar. 12:9; Far. 3:​4, 5; Yoh. 8:44) Wannan abin da Shaiɗan ya yi ya sa Jehobah ya ce za a hallaka shi a nan gaba. (Far. 3:15) Kafin lokacin, mutane da yawa za su bi halin Shaiɗan, kuma su yi munanan abubuwa. Amma, wasu mutane za su yi biyayya ga Jehobah kuma su bauta masa.

7. Su waye ne suke goyon bayan Shaiɗan, kuma me zai faru da su?

7 Waɗanda suke koyi da Shaiɗan su ne, malaꞌikun da suka yi wa Jehobah tawaye, da kuma mutanen da ba sa so su yi wa Jehobah biyayya. Da yake suna adawa da nufin Jehobah, hakan ya sa sun zama ꞌyaꞌyan Shaiɗan. Amma, Jehobah ya riga ya sa ranar da zai hallaka dukansu, har da Shaiɗan.—Dan. 2:44; Rom. 16:20.

8. Mene ne Yesu ya yi a 1914? (Ka kuma duba hotunan.)

8 Me ya tabbatar mana cewa Jehobah zai hallaka Shaiɗan da magoya bayansa? A 1914, Yesu ya zama sarki. Shi da Shaiɗan da aljanunsa sun yi yaƙi, kuma Yesu ne ya yi nasara. Saꞌan nan ya jefo Shaiɗan da aljannunsa a nan duniya. (R. Yar. 12:​7-9) Duk da cewa a sama ne aka yi yaƙin, sakamakon yaƙin ya shafi mutane a duniyar nan. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ya ke duniya, da kai teku, kaitonku! Gama Mugun nan ya sauko muku, cike da fushi gama ya san lokacinsa ya rage kaɗan!” (R. Yar. 12:12) Tun daga shekara ta 1914, Shaiɗan ya mai da hankalinsa a kan duniya. Kuma hakan ya sa yanayin duniya ya ci-gaba da yin muni. Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai ɗaura Shaiɗan har shekara dubu kuma ya hallaka magoya bayansa. (R. Yar. 6:2) Yesu zai sa kowa ya san cewa Shaiɗan mugu ne da yake yaɗa ƙarya game da Jehobah. (Zab. 45:​4-6) Kuma dukan mutane za su san cewa Jehobah Allah maɗaukaki ne mai faɗin gaskiya!—Ezek. 38:23.

Hotuna: Abubuwan da suke faruwa a duniya tun daga 1914. Na 1. An jefo Shaiɗan duniya. Na 2. Sojoji a bakin daga sun zauna da shiri a ramin da suka haƙa. Na 3. Wani bam da ya tashi kuma hayakinsa yana tashi sama. Na 4. Wata mata da ba ta da wurin zuwa, tana zaune a kan titi kuma ta riƙe ɗanta da yake kuka. Na 5. Wani soja yana ƙoƙarin yin harbi. Na 6. Wani mutum yana tafiya a cikin wani gari da aka yi kaca-kaca da shi. Na 7. Gurɓatacciyar hayaƙi na fitowa daga wani kamfani. Na 8. Mutane suna yawo a cikin gari sanye da takunkumin fuska. Na 9. Masu zanga-zanga suna faɗa da ꞌyanꞌsanda.

World War I: U.S. National Archives photo; bomb: USAF photo; pandemic: blvdone/stock.adobe.com; riot: inhauscreative/E+ via Getty Images

Tun daga 1914, yanayin duniya sai ƙara taɓarɓarewa yake yi (Ka duba sakin layi na 8)


JEHOBAH YANA JAWO MASU SON GASKIYA ZUWA WURINSA

9. Su waye ne Jehobah yake tattarawa a yau?

9 Jehobah yana “harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Almasihu, wato dukan abubuwan da suke a sama da abubuwan da suke a ƙasa gaba ɗaya.” (Afis. 1:10) “Abubuwan da suke a sama” suna nufin shafaffun Kristoci da Jehobah ya zaɓa su yi mulki tare da Yesu a sama. “Abubuwan da suke a ƙasa” suna nufin mutanen da za su yi rayuwa har abada a aljanna a duniya. Bayin Jehobah suna iya ƙoƙarinsu wajen nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Suna kuma taimaka wa mutane su san gaskiya game da Jehobah.

10. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa mutane su koyi gaskiya? (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 14:​6, 7)

10 Jehobah yana amfani da bayinsa a duk faɗin duniya wajen koyar da masu zuciyar kirki su san gaskiya game da shi. Yadda bayin Jehobah suke waꞌazi a duk faɗin duniya a yau ba a taɓa ganin irinsa ba. (Karanta Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 14:​6, 7.) Ko da yake Jehobah yana amfani da bayinsa wajen koya wa masu zuciyar kirki gaskiya game da shi, malaꞌiku ma suna taimaka wa bayinsa su haɗu da irin mutanen nan. Saꞌad da bayin Jehobah suke koya wa mutane gaskiya game da shi, suna taimaka musu su fahimci cewa Shaiɗan yana amfani da addinan ƙarya don ya yaɗa ƙarairayi game da Jehobah. (R. Yar. 18:​2, 4) Nan ba da daɗewa ba, za a hallaka dukan addinan ƙarya, hakan zai sa a ɗaukaka sunan Jehobah domin ya cancanci hakan.—R. Yar. 17:16.

11. Ta yaya za a iya gane waɗanda suke bauta wa Allah na gaskiya?

11 Jehobah yana taimaka wa mutane dabam-dabam a duk faɗin duniya su zo su bauta masa. (R. Yar. 7:​9, 10) Idan irin mutanen nan suka ji game da Jehobah, sukan fahimci cewa wannan shi ne gaskiya kuma za su so su zama bayinsa. (Mar. 13:10) A yau, gane waɗanda suke bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace bai da wuya. Annabi Malakai ya ce: “Za ku sāke ganin bambanci tsakanin mai adalci da mugu, kuma tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa.” (Mal. 3:18) Bayin Jehobah suna nuna cewa suna bauta wa Allah na gaskiya ta wajen halinsu da kuma waꞌazin da suke yi.

12. Ta yaya waꞌazin da muke yi yake taimaka wajen cim ma nufin Jehobah?

12 Yayin da muke yin waꞌazin Mulkin Allah muna bin umurnin Yesu, kuma muna cika annabci ne. (Mat. 24:14; 28:​18-20) Waꞌazin da muke yi yana sa mutane a duk faɗin duniya su zama mabiyan Yesu, kuma su sami damar ci-gaba da bauta wa Jehobah har abada. Babban gata ne cewa Jehobah yana amfani da mu wajen cim ma nufinsa!

MUNA DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI CIKA ALKAWARINSA

13. Su waye ne musamman Shaiɗan yake tsananta wa, kuma me ya sa?

13 Shaiɗan yana fushi sosai domin ya san “lokacinsa ya rage kaɗan” kuma za a hallaka magoya bayansa. (R. Yar. 12:​12, 13) Saboda haka, yana tsananta wa bayin Allah musamman waɗanda za su yi mulki tare da Yesu domin suna “kiyaye dokokin Allah, suna kuma riƙe da shaidar Yesu.” (R. Yar. 12:17; 14:12) Ƙari ga haka, yana tsananta wa waɗanda suke taimaka wa shafaffu a aikin da suke yi.

14. Me zai faru a lokacin da Shaiɗan zai kawo wa bayin Allah hari? (Ka kuma duba hoton.)

14 Bayan an hallaka addinan ƙarya, magoya bayan Shaiɗan za su yi ƙoƙarin hallaka bayin Allah. Hakan ne zai sa a soma yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:​13, 14, 16) Yesu da malaꞌikunsa za su ceci bayin Jehobah, kuma su hallaka duk magoya bayan Shaiɗan da suka rage. (R. Yar. 19:​19-21) Mugaye da maƙaryata ba za su ƙara kasancewa ba. (R. Yar. 21:8) Kowa zai san cewa Jehobah mai adalci ne kuma yana faɗin gaskiya.

Yesu da sojojinsa a sama a kan fararen dawakai, suna kai wa sojoji da suke ɗauke da makamai hari a duniya. Yesu yana ƙoƙarin harbi da bakarsa, sauran malaꞌikun kuma suna riƙe da wuƙaƙe.

Yesu da sojojinsa suna gangarowa daga sama don sun hallaka magabtan Allah a yaƙin Armageddon (Ka duba sakin layi na 14)


15. Me ya tabbatar mana cewa Jehobah zai cika alkawuransa? (Ishaya 65:​16, 17) (Ka kuma duba hoton.)

15 A yau, yadda mutane suke ƙarya da kuma yin faɗa da juna yana daɗa ƙaruwa. Amma Jehobah yana taimaka wa bayinsa su kasance da haɗin kai. Jehobah yana jawo mutane masu zuciyar kirki zuwa ƙungiyarsa. Babu abin da zai hana Jehobah yi wa mutanensa albarka, kuma za su yi nasara a ayyukan ibadarsu. (Karanta Ishaya 65:​16, 17.) Muna da tabbaci cewa zai cika alkawuransa. Ta yaya muka san hakan? A Romawa 8:​38, 39 manzo Bulus ya ce: “Ina da tabbaci cewa ko mutuwa, ko rai, ko malaꞌiku, ko gwamnatoci, ko abubuwa da suke nan yanzu, ko abubuwa masu zuwa, ko iko, ko tsawo, ko zurfi, ko kuma wata halitta, ba za su iya raba mu ba da ƙaunar da Allah yake nuna mana ta wurin Kristi Yesu Ubangijinmu.”

Wani mutum da matarsa da yaransu biyu namiji da ta mace cike da farin ciki suna zaune a zauren gidansu a aljanna. Wani karkanda yana gefe yana cin ciyawa.

A aljanna za mu mance da matsalolin da muke fama da su a yau (Ka duba sakin layi na 15)


16. Me ya sa muke dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu?

16 Muna da tabbaci cewa duk abin da Jehobah ya faɗa gaskiya ne. Shi ne ya halicce mu kuma yana ƙaunar mu sosai. Yana tattaro mutane masu zuciyar kirki daga wurare dabam-dabam a faɗin duniya don su zo su bauta masa a hanyar da ta dace. (Isha. 60:22; Zak. 8:23) Kuma mun san cewa nan ba da daɗewa ba Jehobah zai cika alkawuransa. Saꞌan nan ya kawar da Shaiɗan da kuma ƙarairayin da yake yaɗawa. Kamar Dauda mu ma muna adduꞌa cewa: “Albarka ta tabbata ga Yahweh, . . . wanda shi kaɗai ne yake yin ayyukan ban mamaki! Albarka ta tabbata ga Sunansa mai ɗaukaka har abada! Bari ɗaukakarsa ta cika dukan duniya.”—Zab. 72:​18, 19.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa muka dogara ga Jehobah?

  • Ta yaya Jehobah zai kawo ƙarshen Shaiɗan da magoya bayansa kamar yadda ya yi alkawari, kuma mene ne yake yi yanzu don ya cika alkawarinsa?

  • Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawuransa?

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

a Littafi Mai Tsarki bai gaya mana ainihin sunan wannan mugun malaꞌikan ba. An kira shi “Iblis” wanda yake nufin maƙaryaci da kuma “Shaiɗan” wanda yake nufin magabci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba