Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Disamba p. 7
  • Za Ka Iya Cika Fom na Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Cika Fom na Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Ake Koyar da Masu Hidimar Mulkin
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ku Cika Fom na Zuwa Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Masu Wa’azi a Kasashen Waje “Har Zuwa Iyakar Duniya”
    Yadda Ake Amfani da Gudummawarka
  • Wace Makaranta Ce Aka Shirya don Majagaba?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Disamba p. 7
Dalibai da yawa suna halartar Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki.

RAYUWAR KIRISTA

Za Ka Iya Cika Fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki?

Shin kana tsakanin shekaru 23 zuwa 65 kuma kana hidima ta cikakken lokaci? Kana da ƙoshin lafiya kuma za ka iya yin hidima a inda ake da bukatar masu shela? Idan ka amsa e ga waɗannan tambayoyin, ka taɓa yin tunanin cika fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? Tun daga lokacin da aka kammala aji na farko, dubban ma’aurata da ’yan’uwa maza da mata sun halarci makarantar. Amma an fi bukatar ’yan’uwa maza su halarci makarantar. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka zama da marmarin faranta masa rai kuma ka yi koyi da Ɗansa. (Za 40:8; Mt 20:28; Ibr 10:7) Don haka, ka yi tunanin hakkokin da kake da su kamar su hakkin kula da iyalinka ko aikinka ko kuma bashi da ake bin ka. Idan kana da ɗaya daga cikin waɗannan hakkokin, za ka iya daidai shi don ka iya cancanci zuwa makarantar?

A waɗanne hanyoyi da wurare ne waɗanda aka horar a makarantar za su iya yin hidima? An tura waɗanda suka sauke karatu a makarantar zuwa wuraren da ake wasu yaruka ko wuraren da ake wa’azi da amalanke na musamman. Wasu kuma daga baya sun zama masu taimaka wa mai kula da da’ira ko masu kula da da’ira ko kuma waɗanda suke wa’azi a ƙasashen waje. Yayin da kake tunanin yadda za ka faɗaɗa hidimarka ga Jehobah, ka kasance da ra’ayin annabi Ishaya wanda ya ce: “Ga ni nan, ka aike ni!”​—Ish 6:8.

KU KALLI BIDIYON NAN MASU HIDIMA A ƘASASHEN WAJE SUNA WA’AZI DA ƘWAZO, SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoton da aka dauka daga bidiyon nan Masu Hidima a Kasashen Waje Suna Wa’azi da Kwazo.’ Wasu ma’aurata da suke wa’azi a kasar waje suna wa’azi a wata anguwa.

    Ta yaya ake zaɓan waɗanda suke hidima a ƙasashen waje?

  • Hoton da aka dauka daga bidiyon nan Masu Hidima a Kasashen Waje Suna Wa’azi da Kwazo.’ Wata ’yar’uwa da ke wa’azi a kasar waje tare da wata ’yar’uwa suna nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata.

    Wane aiki mai kyau ne ’yan’uwa da suke wa’azi a ƙasashen waje suke yi?

  • Hoton da aka dauka daga bidiyon nan Masu Hidima a Kasashen Waje Suna Wa’azi da Kwazo.’ Wani mai wa’azi a kasar waje kuma a yaren kurame yana tattaunawa da wani dan’uwa game da fom na hidima ta musamman.

    Waɗanne albarku ne waɗanda suke wa’azi a ƙasashen waje suke samuwa?

Shin kana so ka sami ƙarin bayani game da Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? Ka danna “Bidiyo” a sashen Laburare a dandalin jw.org, kuma ka duba AYYUKANMU > MAKARANTUNMU DA ILIMANTARWA. Ku kalli waɗannan bidiyon Theocratic Schools in the Heart of Africa da Albarkun da Koyarwar Jehobah Ke Kawowa da kuma SKE First Graduation.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba