DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN FIRISTOCI 16-17
Abin da Za Mu Iya Koya Daga Ranar Gafara
16:12-15
Me za mu koya daga yadda aka yi amfani da turare a Ranar Gafara?
Addu’o’i da bayin Jehobah masu aminci suke masa suna kama da turare. (Za 141:2) Kamar yadda babban firist yakan kawo turare ga Jehobah da ladabi, haka ma ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah da ladabi
Sai babban firist ya ƙona turare kafin ya miƙa hadayu. Haka ma, kafin Yesu ya ba da ransa hadaya, ya shirya yadda Jehobah zai karɓi hadayar ta wurin kasancewa da aminci
Ta yaya zan tabbata cewa Jehobah zai amince da sadaukarwa da nake yi dominsa?