RAYUWAR KIRISTA | KU KAFA MAƘASUDAI DON SABUWAR SHEKARA TA HIDIMA
Ku Cika Fom na Zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki
Ba sai kome yana tafiya sumul a rayuwarka ba ne za ka iya halartar Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Abu mafi muhimmanci da ake bukata shi ne, kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma zama a shirye don amincewa da duk wata hidimar da ƙungiyar Jehobah ta ce mu yi.—Ish 6:8.
KU KALLI BIDIYON NAN KU ƘARA ƘWAZO A HIDIMARKU DA BANGASKIYA—KU CIKA FOM NA MAKARANTAR MASU YAƊA BISHARAR MULKI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Me ya sa Gabriel bai san ko ya cika fom na zuwa makarantar ba? Ta yaya ya amfana sa’ad da ya yi bimbini a kan Filibiyawa 4:13?