DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 44-45
Yusuf Ya Gafarta ma ’Yan’uwansa
44:1, 2, 33, 34; 45:4, 5
Idan wani ya ci mana mutunci da gangan, zai yi mana wuya mu gafarta masa. Me ya taimaka ma Yusuf ya gafarta ma ’yan’uwansa bayan sun ci mutuncinsa?
Yusuf bai rama abin da ’yan’uwansa suka yi masa ba, amma ya gafarta musu.—Za 86:5; Lu 17:3, 4
Bai riƙe ’yan’uwansa a zuciya ba, amma ya yi koyi da Jehobah ta wajen gafarta musu da dukan zuciyarsa.—Mi 7:18, 19
Ta yaya zan yi koyi da yadda Jehobah yake gafartawa?