DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IBRANIYAWA 4-6
Ku Yi Iya Ƙoƙarinku don Ku Shiga Hutun Allah
Za mu iya shiga hutun Jehobah ta wurin yin ayyukan da suka jitu da nufinsa kamar yadda ƙungiyarsa ta bayyana mana. Don haka, mu tambayi kanmu: ‘Idan wani ya gargaɗe ni, nakan bi gargaɗin? Idan aka yi gyara a yadda muka fahimci wani nassi, nakan amince da gyarar?’
Me yake jaraba ni in yi ma Jehobah rashin biyayya?