Tambayoyi Daga Masu Karatu
Menene “hutu” da aka ambata a Ibraniyawa 4:9-11, kuma ta yaya mutum yake “shiga cikin wannan hutu”?
Zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa na ƙarni na farko, manzo Bulus ya rubuta: “Akwai fa hutun asabaci ajiyayye domin jama’ar Allah. Gama wanda ya shiga cikin hutunsa shi da kansa ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah ya yi daga nasa. Mu yi anniya fa mu shiga cikin wannan hutu.”—Ibraniyawa 4:9-11.
Yayin da Bulus ya ce Allah ya huta daga Aikinsa, lalle yana magana ne game da abin da ke Farawa 2:2, inda ya ce: “A kan rana ta bakwai fa Allah ya gama aikinsa wanda ya yi; ya huta fa a kan rana ta bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.” Me ya sa Jehovah ya “huta a rana ta bakwai”? Hakika ba saboda ya gaji ba ne da ya bukaci ya huta gajiyar “dukan aikinsa da ya yi.” Aya ta gaba ta gaya mana: “Kuma Allah ya albarkaci rana ta bakwai, ya tsarkake ta: domin a cikinta ya huta daga dukan aikinsa wanda Allah ya halitta da wanda ya aika.”—Farawa 2:3; Ishaya 40:26, 28.
“Rana ta bakwai” dabam take daga kowacce cikin ranaku shida, domin Allah ne ya albarkace ta kuma ya tsarkake ta, watau, rana da aka tsara ta, ko kuma aka keɓe ta domin wani nufi na musamman. Menene nufin? Da farko, Allah ya bayyana nufinsa game da bil Adam da kuma duniya. Allah ya gaya wa mutum na farko da matarsa, cewa: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” (Farawa 1:28) Ko da yake Allah ya fara mutane da kuma duniya kamiltattu, zai ɗauki lokaci kafin su mallake dukan duniya kuma su sa ta zama aljanna da za ta cika da iyalin ’yan Adam kamiltattu, yadda Allah ya nufa. Saboda haka, a “rana ta bakwai,” Allah ya huta, ko kuma ya daina aikin halitta a duniya domin ya ƙyale abin da ya yi, su bunƙasa daidai da nufinsa. A ƙarshen ‘ranar,’ dukan abin da Allah ya nufa zai cika. Har yaushe ne hutun zai kasance?
Idan muka koma ga maganar Bulus a Ibraniyawa, za mu lura ya ambaci cewa “akwai fa hutun asabaci ajiyayye domin jama’ar Allah,” sai ya aririci ’yan’uwansa Kirista su yi iyakacin ƙoƙarinsu su “shiga cikin wannan hutu.” Wannan ya nuna cewa lokacin da Bulus ya rubuta waɗancan kalmomi, “rana ta bakwai” na hutun Allah, wanda ya soma shekaru 4,000 tun farko yana kan ci gaba. Ba zai ƙare ba har sai nufin Allah game da mutane da kuma duniya ya cika sarai a ƙarshen Sarautar Shekara Dubu na Yesu Kristi, wanda shi ne “Ubangijin asabaci.”—Matta 12:8; Ru’ya ta Yohanna 20:1-6; 21:1-4.
Tare da irin zaton nan mai girma, Bulus ya bayyana yadda mutum zai iya shiga hutun Allah. Ya rubuta: “Wanda ya shiga cikin hutunsa shi da kansa ya huta daga ayyukansa.” Wannan yana gaya mana ne cewa ko da yake mutane suna da kamilcaccen somi, mutane gabaki ɗaya ba su shiga hutun Allah ba. Wannan haka ne domin Adamu da Hauwa’u ba su kiyaye hutun Allah da daɗewa ba a “rana ta bakwai” ta amincewa da tsarinsa dominsu. Maimako, sun yi tawaye kuma sun so su sami ’yancin kai daga Allah. Hakika, sun bi dabarar da Shaiɗan ya yi maimakon bin ja-gorar ƙauna na Allah. (Farawa 2:15-17) Sakamakon haka, sun yi hasarar zato na rayuwa har abada a aljanna a duniya. Tun daga lokacin, dukan mutane sun shiga bauta ga zunubi da kuma mutuwa.—Romawa 5:12, 14.
Tawayen mutane bai hana nufin Allah ba. Ranar hutunsa ta ci gaba. Amma, Jehovah ya yi tanadi na ƙauna—fansa—ta wurin Ɗansa, Yesu Kristi, domin duka wanda ya amince da ita bisa bangaskiya ya iya duba gaba don sakewa da kuma hutu daga dukan wahalar zunubi da mutuwa. (Romawa 6:23) Abin da ya sa Bulus ya aririce ’yan’uwansa Kiristoci su ‘huta daga ayyukansu.’ Suna bukatar su amince da tanadin Allah don ceto kuma kada su yi ƙoƙari su yi nasu aiki don nan gaba a nasu hanya, yadda Adamu da Hauwa’u suka yi. Suna kuma bukatar su guje biɗan ayyukansu na ganin ba su da laifi.
Daina biɗa na kanka ko kuma abubuwan zaman rayuwa don ka yi nufin Allah yana wartsekarwa kuma yana ba da hutu. Yesu ya yi wannan gayyatar: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.”—Matta 11:28-30.
Tattaunawar da Bulus ya yi game da hutun Allah da kuma yadda mutum zai iya shiga ciki babu shakka ƙarfafa ce ga Kiristoci Ibraniyawa da suke Urushalima, da suka jimre wa tsanani da ba’a don bangaskiyarsu. (Ayukan Manzanni 8:1; 12:1-5) Hakanan kuma, kalmomin Bulus suna iya zama abin ƙarfafa ga Kiristoci a yau. Fahimtar cewa cikar alkawarin Allah na kawo aljanna a duniya a ƙarƙashin Mulkinsa na adalci ya yi kusa, mu ma ya kamata mu huta daga ayyukanmu kuma mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu shiga cikin wannan hutun.—Matta 6:10, 33; 2 Bitrus 3:13.
[Hotuna a shafi na 31]
Alkawarin Allah na aljanna ta duniya zai cika a ƙarshen ranar hutunsa