Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Agusta p. 8
  • Ayyukan Kirki da Jehobah Ba Zai Manta da Su Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ayyukan Kirki da Jehobah Ba Zai Manta da Su Ba
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Gayyata ga Kowa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Wane Irin Wuri Ne Bethel?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Agusta p. 8
Wata ’yar’uwa tana aiki a kicin da ke Bethel

RAYUWAR KIRISTA

Ayyukan Kirki da Jehobah Ba Zai Manta da Su Ba

Dukan bayin Jehobah za su iya yin ayyukan da Jehobah ba zai manta da su ba har abada. Kamar yadda uba ba ya mantawa da ayyuka masu kyau da yaransa suka yi, haka ma Jehobah ba zai manta da ayyuka masu kyau da muka yi da kuma ƙaunar da muka nuna masa ba. (Mt 6:20; Ibr 6:10) Ko da yake yanayinmu ya bambanta, amma idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu bauta ma Jehobah, za mu yi farin ciki sosai. (Ga 6:4; Kol 3:23) Shekaru da yawa yanzu, dubban ’yan’uwa maza da mata sun yi hidima a Bethel. Shin za ka iya yin hidima a Bethel? Idan ba za ka iya ba, za ka iya ƙarfafa wani ya yi hidima a Bethel ko ka taimaka ma wani da yake hidima a Bethel ya ci gaba da yin hidimarsa?

KU KALLI BIDIYON NAN KU BA DA KANKU DON KU YI HIDIMA A BETHEL, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Wane abu ne ya kamata ya sa mutum ya so yin hidima a Bethel?

  • Wace albarka ce wasu suka ce sun samu don hidimar da suke yi a Bethel?

  • Waɗanne abubuwa ne za su sa mutum ya cancanci yin hidima a Bethel?

  • Me za ka yi don ka iya yin hidima a Bethel?

Wasu ’yan’uwa uku da ke hidima a Bethel suna aiki tare da kwamfuta; wani dan’uwa yana sa littattafai a cikin kwali; wani dan’uwa yana aikin kafinta a Bethel

Abubuwan da za su sa ka cancanci yin Hidima a Bethel

  • Ƙaunar Jehobah da kuma ƙungiyarsa

  • Ɗabi’a mai kyau da kuma zuciya mai tsabta a gaban Jehobah

  • Saka tufafin da suka dace da Kirista

  • Yin nishaɗin da suka dace da Kirista

  • Mai shekara 19 zuwa 35

  • Koshin lafiya

  • Iya karatu da rubutu da kuma yaren da ake amfani da shi a ofishin

  • Ka amince za ka yi hidimar aƙalla shekara ɗaya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba