RAYUWAR KIRISTA
Ƙauna Ce Alamar Kiristoci Na Gaskiya—Kada Ka Ɓata Haɗin Kai da Muke Mora
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: A daren da za a kashe Yesu, ya yi addu’a don almajiransa “su zama ɗaya.” (Yoh 17:23) Idan muna so mu ci gaba da kasancewa da haɗin kai, wajibi ne mu ƙaunaci ’yan’uwanmu kuma ƙauna “ba ta riƙe laifi a zuciya.”—1Ko 13:5.
YADDA ZA MU YI HAKAN:
Kamar Jehobah, mu riƙa lura da halaye masu kyau da mutane suke da shi
Mu yafe wa mutane daga dukan zuciyarmu
Idan mun sasanta wata matsala, kada mu tuna da batun kuma.—K. Ma 17:9
KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”—KADA KU RIƘE JUNA A ZUCIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
A bidiyo na farkon, ta yaya Helen ta nuna cewa ta riƙe ’yar’uwarta a zuciya?
A bidiyo na biyu, ta yaya Helen ta canja tunaninta kuma ta kasance da ra’ayin da ya dace?
Ta yaya abin da Helen ta yi ya sa an ƙara kasance da haɗin kai a ikilisiyar?
Idan muna riƙe mutane a zuci, wa zai fi baƙin ciki?