Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Nuwamba p. 3
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Komawa Ziyara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Komawa Ziyara
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yin Shiri don Ziyara ta Gaba
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—⁠Yin Shiri don Ziyara ta Gaba
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Za Ku Iya Soma Nazari da Waɗanda Kuka Saba Ba Mujallunmu
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Nuwamba p. 3

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Komawa Ziyara

ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Yawancin mutanen da suke saurarar wa’azinmu sun daɗe suna son su san gaskiya game da Allah. (Ish 55:6) Don mu taimaka musu su san gaskiyar, wajibi ne mu riƙa komawa a kai a kai. Ƙalubalen da mutane suke fuskanta ya bambanta. Don haka, yadda za mu taimaka musu ba zai zama iri ɗaya ba. Duk da haka, nazarin zai yi tasiri sosai idan muka shirya da kyau da kuma tsara abubuwan da za mu tattauna a kowace ziyara. Mu kuma kafa maƙasudin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da maigidan.

Wata ’yar’uwa tana shiri don koma ziyara

YADDA ZA KA YI HAKAN:

’Yan’uwa mata guda biyu sun sake ziyarar maigidan kuma suna nuna mata bidiyo
  • Ka koma da wuri, wataƙila bayan kwanaki kaɗan.​—Mt 13:19

  • Ka daraja maigidan kuma ka mai da shi abokinka. Ka saki jiki a gidan

  • Ka fara da gaisuwa. Ka kira shi da sunansa. Ka tuna masa dalilin da ya sa ka dawo, wataƙila don ka amsa wata tambaya ko don ka ba shi sabuwar mujalla, ko don ka nuna masa dandalinmu, ko bidiyo ko kuma ka nuna masa yadda muke nazari da mutane. Ka canja batun da kuke tattaunawa idan maigidan ya zaɓi wani batu dabam.​—Fib 2:4

  • Ka taimaka masa ya so gaskiya ta wajen karanta masa wani Nassi ko kuma ka ba shi wata mujalla. (1Ko 3:6) Ka kasance da dangantaka mai kyau da shi

  • Ka yi shiri don ziyara ta gaba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba