Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yin Shiri don Ziyara ta Gaba
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: Sa’ad da mutum ya yi sha’awar saƙonmu, za mu so mu koma a lokacin da za mu same shi a gida don mu yi ban ruwan iri na gaskiya da muka shuka a zuciyarsa. (1 Kor. 3:6) Don mu yi hakan, muna bukatar mu yi shiri don ziyara ta gaba ta wajen tambayar maigidan lokacin da zai so mu sake dawowa. Ƙari ga haka, zai dace mu yi wa maigidan tambayar da za mu so mu amsa a ziyara ta gaba. Hakan zai sa maigidan ya sa rai cewa za mu sake dawowa, kuma idan amsar tambayar tana cikin littafin da muka ba shi, zai so ya karanta littafin. Idan mun yi shiri don ziyara ta gaba, ba za mu yi jinkirin komawa ba domin mun riga mun zaɓi batun da za mu tattauna kuma maigidan ya san da hakan. Sa’ad da muka dawo, za mu iya gaya masa cewa mun dawo ne don mu amsa tambayar da muka yi masa a wancan karon sa’an nan mu ci gaba da tattaunawa.
Ku Bi Shawarar Nan Wannan Watan:
Yayin da kake shirya abin da za ka faɗa a wa’azi gida-gida, ka shirya tambayar da za ka yi wa maigida bayan ka yi masa wa’azi, don ka amsa ta a ziyararka ta gaba. Ka gaya wa masu shela da kuke wa’azi tare abin da ka shirya.