Za Ku Iya Soma Nazari da Waɗanda Kuka Saba Ba Mujallunmu
1. Me ya sa ƙungiyar Jehobah ta daɗe tana ƙarfafa masu shela su nemi waɗanda za su riƙa ba su mujallunmu?
1 Mutane da yawa suna son karanta mujallunmu, amma ba sa so mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Saboda haka, ƙungiyar Jehobah ta daɗe tana ƙarfafa masu shela su nemi mutanen da za su riƙa ba su mujallunmu kowane wata. Yayin da mutane suke karanta mujallunmu a kai a kai, suna iya soma sha’awar Kalmar Allah. (1 Bit. 2:2) A kwana a tashi, suna iya karanta abin da za su so kuma hakan zai sa su yarda mu soma nazari da su.
2. Yaya za mu sa waɗanda muka saba ba su mujallunmu su ci gaba da son saƙonmu?
2 Ku Taimaka Musu Su Ci Gaba da Son Gaskiya: Maimakon ku riƙa ba mutane mujallunmu kawai, ku yi ƙoƙari ku tattauna da su don ku iya ƙulla dangantaka da su. Wannan zai sa ku fahimci yanayinsu da abubuwan da suke so da kuma imaninsu. Hakan zai taimaka muku ku bi da su cikin dabara. (Mis. 16:23) Ku shirya da kyau kafin ku ziyarce su. Idan da hali, ku ɗan tattauna wani batu da kuma nassi daga cikin mujallun da kuke so ku ba su. Ta hakan, za ku yi wa gaskiyar da ke zuciyarsu ban ruwa. (1 Kor. 3:6) Ku riƙa rubuta ranar da kuka kai musu ziyara da mujallun da kuka ba su da batu da kuma nassosin da kuka tattauna da su.
3. Sau nawa ya kamata mu riƙa ziyartar waɗanda muka saba ba su mujallunmu?
3 Sau Nawa Zai Dace Ku Riƙa Komawa? Zai dace ku koma sau ɗaya a wata don ku ba da sabbin mujallu ga waɗanda kuka saba ba su mujallunmu. Amma idan da hali kuma mutumin yana sha’awar saƙonmu, za ku iya komawa fiye da sau ɗaya a wata. Alal misali, za ku iya komawa bayan mako ɗaya ko biyu da ba shi mujallun, kuma ku ce, “Na bi wurinka ne don in ɗan nuna maka wani abu a cikin mujallun da na ba ka.” Hakan zai sa mutumin ya yi marmarin karanta talifin. Idan ya riga ya karanta talifin, za ku iya tambayar ra’ayinsa game da abin da ya karanta, sa’an nan ku ɗan tattauna talifin da shi. Idan kuma mutumin yana jin daɗin karanta littattafanmu, za ku iya dawowa don ku ba shi warƙa ko ƙasida ko kuma littafin da muke ba mutane a watan.
4. Mene ne za mu iya yi a loto-loto don mu san ko waɗanda muka saba ba su mujallunmu suna so mu yi nazari da su?
4 Kada ku jira har sai maigidan ya ce ku soma nazari da shi, amma ku tambaye shi ko zai so hakan. Ko da bai yarda ku yi nazari da shi ba a dā, a loto-loto za ku iya nuna masa jerin talifofin nan “Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki” da ke Hasumiyar Tsaro don ku ga ko zai yarda ku tattauna da shi. Wataƙila hakan zai ba ku damar soma nazari da shi nan da nan. Amma idan ba ku iya soma nazari da shi ba, ku riƙa ba shi mujallunmu don ya ci gaba da yin marmarin saƙonmu.