DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 29-33
“Wani Sarki Za Ya Yi Mulki Cikin Adalci”
Sarki Yesu ya naɗa “hakimai” ko kuma dattawa don su kula da tumakinsa
32:1-3
Kamar “makāri . . . daga hadarin ruwa,” dattawa suna iya ƙoƙarinsu wajen kāre tumakin Allah daga hamayya da kuma abin da zai iya sa su karaya
Kamar “koguna cikin ƙeƙasashiyar ƙasa,” suna yi musu tanadin abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah
Kamar “inuwar babban dutse cikin ƙasa mai-agazari,” suna taimaka musu ta wajen yin amfani da Kalmar Allah don su yi musu ja-gora da kuma ƙarfafa