Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb16 Nuwamba p. 3
  • Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Kwatanta Matar Kirki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Kwatanta Matar Kirki
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Makamantan Littattafai
  • Shawarar Hikima ta Uwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Mijinta Sananne Ne a Kofofin Gari”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • “Miji Kuma Shi Ne Shugaban Matarsa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Iyalinka Za Ta Zauna Lafiya
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
mwb16 Nuwamba p. 3

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MISALAI 27-31

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Kwatanta Matar Kirki

Misalai sura 31 yana ɗauke da saƙo mai muhimmanci da mahaifiyar Sarki Lemuel ta aika masa. Shawarar da ta ba shi ta koya masa yadda zai gane macen kirki.

Macen kirki tana da riƙon amana

Wata mata a zamanin dā tana rarraba wa iyalinta abinci

31:10-12

  • Tana ba da shawara mai kyau a iyali kuma tana ladabi da biyayya

  • Maigidanta yana barin ta ta tsai da wasu shawara ba tare da cewa sai lallai ta nemi izininsa ba

Macen kirki tana da ƙwazo

Wata mata a zamanin dā tana nika

31:13-27

  • Ta san yadda za ta kashe kuɗi don iyalinta su riƙa saka tufa mai kyau kuma su ci abinci mai gina jiki

  • Tana aiki da ƙwazo kuma tana kula da iyalinta dare da rana

Macen kirki tana ƙaunar Allah

Wata mata tana addu’a

31:30

  • Tana tsoron Allah kuma tana da dangantaka mai kyau da shi

KA SAN CEWA?

Ana ɗaukan lu’u lu’u da tamani sosai a zamanin dā. Yana da kyan gaske kuma sai mutum ya sha wuya kafin ya same shi. Ana samun shi a Bahar Rom da Jar Teku kuma ana cinikinsa sosai.

Jar lu’u lu’u

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi da zinariya da azurfa da kuma saffir don yana da tamani sosai.

Kalmar Allah ta ce darajar macen kirki ta “fi gaban lu’u lu’ai.”—Mis 31:10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba