Shawarar Hikima ta Uwa
Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yasda ita.”—Misalai 1:8.
IYAYENMU—mamarmu da babanmu—za su iya zama tushe mai kyau na ƙarfafawa, goyon baya, da kuma shawara. Littafin Misalai na Littafi Mai-Tsarki ya faɗi game da wani sarki saurayi, Lemuel, wanda uwarsa ta yi masa ‘jawabi mai ƙarfi’ na ‘gyara.’ Waɗannan kalmomi suna rubuce a Misalai sura 31, mu ma za mu amfana daga wannan shawarar hikima ta uwarsa.—Misalai 31:1.
Shawara da ta Dace Wa Sarki
Uwar Lemuel ta soma da tambayoyi mai yawa da ya ƙara marmarinmu: “Me ke nan ɗana? me ke nan, ya ɗan cikina? Me ke nan kuma, ya ɗa na wa’adodina?” Roƙo da ta maimaita sau uku ya nuna damuwarta ƙwarai don ɗanta ya mai da hankali ga maganarta. (Misalai 31:2) Damuwarta game da ruhaniyar ɗanta ya zama misali mai kyau ga iyaye Kirista a yau.
Game da lafiyar ɗanta, me zai dami uwa im ba wasan hauka da lalata ta giya, mata, da waƙa ba? Uwar Lemuel ta faɗi batun daidai: “Kada ka bada ƙarfinka ga mata.” Ta kwatanta lalata cewa abin da “ke halaka sarakuna” ke nan.—Misalai 31:3.
Kada a manta shan giya mai yawa. Ta yi gargaɗi, “Ba aikin sarakuna, ya Lemuel, ba aikin sarakuna ba ne su sha ruwan anab.” Yaya sarki zai yi shari’a da tunani mai kyau bai “manta da shari’a, ɓata shari’ar kowane ƙuntace” idan ko yaushe yana buge?—Misalai 31:4-7.
Akasarin haka, ta wajen kasancewa a ware daga irin munanan ayyukan nan, sarkin zai iya “hukunta shari’a da gaskiya, hukunta shari’a ga fakirai da masu-mayata.”—Misalai 31:8, 9.
Ko da matasa Kirista ba za su zama “sarakuna” ba a yau, shawarar hikima ta uwar Lemuel tana kan lokaci, im ba fiye da haka ba ma ke nan. Buguwa da giya, shan taba, lalatar jima’i suna ko’ina tsakanin matasa a yau, saboda haka, yana da muhimmanci matasa Kirista su mai da hankali lokacin da iyayensu suke ba su ‘jawabi masu ƙarfi.’
Mace Mai Tsarkin Rai
Uwaye suna damuwa da ta dace game da auren ’ya’yansu da suke girma. Uwar Lemuel ta mai da hankali ga halayen mace ta kirki. Babu shakka, saurayi zai amfana sosai ta wajen bincika matsayin mace a wannan muhimmin batu.
A aya ta 10, an kamanta “mace mai-tsarkin rai” da lu’u lu’ai da ke da tamani da kuma mai wuyan gani, wanda a lokuttan Littafi Mai-Tsarki kafin a same su sai an yi ƙoƙari sosai. Haka yake, samun mace mai tsarkin rai yana bukatar ƙoƙari. Maimakon hanzartawa ya yi aure, ya kamata saurayi ya ɗauki lokaci da ya dace ya zaɓi wadda zai aura. Sa’annan zai ɗauka abin da ya samo da tamani ƙwarai.
Game da mace mai tsarkin rai, an gaya ma Lemuel: “Zuciyar mijinta tana dogara gareta.” (Aya ta 11) A cikin wasu kalmomi, bai kamata ya nace cewa matarsa ta karbi izini daga wurinsa a kowane al’amari ba. Hakika, ya kamata mata da miji su haɗu kafin su tsai da muhimman shawarwari, irinsu sayen abubuwa masu tsada ko kuma renon yaransu. Yin zance a waɗannan wurare yana kawo gami na ƙwarai a tsakaninsu.
Hakika, mace mai tsarkin rai tana da abubuwa da yawa da za ta yi. A cikin ayoyi 13 zuwa 27 an tsara shawara da ƙa’idodi da mata a kowane zamani za su yi amfani da su don amfanin iyalinsu. Alal misali, da sutura da kayan adon ɗaki da ke ƙara tsada, mace mai tsarkin rai za ta koyi aikin hannu da yin amfani mai kyau da kuɗi don iyalinta su samu isashen tufafi kuma su yi kyau. (Ayoyi, 13, 19, 21, 22) Don ta rage kuɗin cefane, tana shuka abin da za ta iya kuma tana mai da hankali a wajen cefane.—Ayoyi 14, 16.
Hakika, wannan matar ba ta cin “abincin ragonci.” Tana aiki sosai, kuma tana gudanar da ayyukan iyalinta da kyau. (Aya 27) Tana ɗaura “gindinta da ƙarfi,” wanda yake nufin cewa, tana shirye ta yi aiki mai wuya. (Aya 17) Tana tashiwa da asuba ta soma aikinta, kuma ta yi aiki sosai har dare. Kamar dai fitila da take haskaka aiki tana ci ko da yaushe.—Ayoyi 15, 18.
Fiye da kome, mace mai tsarkin rai mutuniya ce ta ruhaniya. Tana tsoron Allah kuma tana bauta masa cikin biyayya sosai da kuma cikin tsoro. (Aya 30) Tana kuma taimakon mijinta a renon yaransu don su yi hakan. Aya 26 ta ce: “Da hikima” tana koyar da yaranta, kuma “ƙa’idar nasiha kuma tana kan harshenta.”
Miji Mai Tsarkin Rai
Don ya sa mace mai tsarkin rai ta yi sha’awarsa, Lemuel yana bukatar ya cika nawayoyi na miji mai tsarkin rai. Uwar Lemuel ta tunatar masa da yawa cikin waɗannan.
Miji mai tsarkin rai “dattiɓan gari” za su yaba masa. (Misalai 31:23) Wannan yana nufin cewa zai zama mai ƙarfi, mai gaskiya, mai riƙon amana, da kuma mai tsoron Allah. (Fitowa 18:21; Kubawar Shari’a 16:18-20) Saboda haka, zai zama “sananne ne a ƙofofin gari,” inda sanannun mutane suke taruwa su yi zance yadda za a tafiyar da harƙoƙin garin. Don ya zama “sanannen” mai tsoron Allah, zai na yin abu da kyau kuma zai na yin aiki cikin jituwa da dattiɓan “garin,” wataƙila wannan yana nufin gunduma ko kuwa yanki.
Babu shakka tana magana daga abin da ita kanta ta sani, uwar Lemuel ta tunatar wa ɗanta game da muhimmancin yin godiya ga wadda za ta zama matarsa. Babu wata a duniya da zai so kamar ita. Saboda haka, ka ƙaga yadda yake ji lokacin da ya ce a gaban dukan mutane: “ ’Yan mata dayawa sun yi al’amura masu-tsarki, amma duk kin fi su hali.”—Misalai 31:29.
A bayyane yake cewa Lemuel ya ji daɗin shawarar hikima ta uwarsa. Alal misali, mun lura cewa a aya ta ɗaya ya nuna maganar uwarsa kamar ta shi. Saboda haka, ya ɗauki “gyara” na uwarsa a zuci kuma ya amfana daga shawararta. Bari mu ma mu amfana daga wannan ‘jawabi mai ƙarfi’ ta wurin yin amfani da ƙa’idodinsa a rayuwanmu.
[Hotuna a shafi na 31]
Mace mai tsarkin rai ba ta cin “abincin ragonci”