Tambayoyin Masu Shela
◼ Ya kamata masu shela su riƙa yin amfani da Intane domin yin wa’azi ko kuma nazari da wani a wata ƙasa?
Wasu masu shela suna yin amfani da Intane don yin nazari da mutane a ƙasashen da aka dakatar da aikinmu ko kuma a inda babu masu shela da yawa. A wasu lokuta, ana samun sakamako masu kyau. Duk da haka, aika saƙonni ta Imel ko kuma yin hira da mutanen da ba mu sani ba ta Intane yana da haɗari sosai. (Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2011, shafuffuka na 3-5.) Ko da yake manufar hirar ita ce don mutane su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki, hakan zai iya sa ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta soma cuɗanya da abokan banza kamar ’yan ridda. (1 Kor. 1:19-25; Kol. 2:8) Ƙari ga haka, hukuma za ta iya bincika tattaunawa da mutane ke yi a ƙasashen da aka dakatar da aikinmu, don haka, ’yan’uwan da ke amfani da Intane wajen yin wa’azi za su iya saka kansu cikin haɗari. Saboda haka, kada masu shela su shiga Intane don neman mutane a wasu ƙasashe da za su yi musu wa’azi.
Idan muka yi wa wani da ya zo daga wata ƙasa wa’azi sa’ad da muke ayyukanmu na yau da kullum, ba zai dace mu ci gaba da tattauna Littafi Mai Tsarki da shi ba bayan ya koma ƙasarsu, sai dai idan ofishinmu ya ce mu yi hakan. Maimakon haka, za mu iya nuna masa yadda zai yi amfani da dandalinmu na jw.org don samun ƙarin bayani ko yadda zai tuntuɓi ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasarsu. Za mu kuma iya ƙarfafa shi ya halarci taro a Majami’ar Mulki da ke kusa da shi. Hakika, babu Majami’un Mulki a wasu ƙasashe. Idan yana son Shaidu su riƙa ziyartarsa, zai dace mu cika fom ɗin nan Please Follow Up (S-43) kuma mu ba wa sakataren ikilisiyarmu don ya aika shi ta dandalin jw.org. ’Yan’uwan da ke kula da ayyukanmu a ƙasar da mutumin yake da zama sun fi sanin yanayin wurin, saboda haka, za su iya shirya yadda za a taimaka wa mutumin ya koya game da Jehobah.—Ka duba Hidimarmu ta Mulki ta Yuni 2014, shafi na 7, da Hidimarmu ta Mulki ta Nuwamba 2011, shafi na 4.
Idan wani da muke nazari da shi ya ƙaura zuwa wata ƙasa ko kuma muna nazari da wani da ke wata ƙasa ta Intane kuma ba mu san shi ba, zai dace mu bi umurnin da aka bayar a baya. Amma, za mu iya ci gaba da nazari da shi har sai wani mai shela da ke ƙasarsu ya tuntuɓe shi. Duk da haka, idan yana zama ne a ƙasar da aka dakatar da aikinmu, zai dace mu mai hankali sosai sa’ad da muke tattauna Littafi Mai Tsarki ta wasiƙa da tarho da dai sauransu.—Mat. 10:16.