Tsarin Ayyuka na Makon 27 ga Yuli
MAKON 27 GA YULI
Waƙa ta 18 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 28 sakin layi na 1-9 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sarakuna 15-17 (minti 8)
Na 1: 1 Sarakuna 15:16-24 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Mata?—igw 26 sakin layi na 3-4 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Dukan Aljanu Sun Yi Imani da Wanzuwar Allah?—Yaƙ. 2:19 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: ‘Ku je ku almajirtar’ da mutane.—Mat. 28:19, 20, Littafi Mai Tsarki.
Waƙa ta 65
Minti 7: “Gayyata ga Kowa.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Sa’ad da kake tattauna sakin layi na 3, ka sa a yi gwaji da ya nuna yadda za a rarraba takardar gayyatar.
Minti 10: “Tunasarwa Game da Taron Yanki.” Tattaunawa da sakatare zai yi. Ka mai da hankali ga ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da aka nanata a talifin da kuma yadda za a iya yin amfani da su a taron yanki na 2015. Ka kuma tattauna wasu batutuwan da ke cikin wasiƙa ta 3 ga Agusta, 2013, zuwa ga dukan ikilisiyoyi game da matakan da ya kamata a ɗauka don guje wa haɗarurruka sa’ad da ake halartar taro.
Minti 7: Ku Yi Amfani da Ƙasidar Nan “Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah” don Taimaka wa Ɗalibanku. Tattaunawa. Ka tattauna yadda za mu iya yin amfani da wannan ƙasidar don taimaka wa ɗalibanmu su iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki: (1) “Yadda za a iya samun nassi a cikin Littafi Mai Tsarki.” (2) Tambaya ta 19: “Yaya aka tsara littattafan Littafi Mai Tsarki?” (3) Tambaya ta 20: “Ta yaya za ka amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki?” Ka sa wani mai shela ya gwada yadda za a tattauna ɗaya cikin waɗannan shawara da ɗalibinsa bayan sun kammala nazari.
Minti 6: “Kayan Aikin da Muke da Shi don Koyarwa.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 125 da Addu’a