Tsarin Ayyuka na Makon 20 ga Yuli
MAKON 20 GA YULI
Waƙa ta 73 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 27 sakin layi na 19-22, da akwatin da ke shafi na 279 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sarakuna 12-14 (minti 8)
Na 1: 1 Sarakuna 12:21-30 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Hanyoyin da Za Mu Iya Yin Tsayayya da Iblis—Yaƙ. 4:7 (minti 5)
Na 3: Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Yake Taimaka wa Mazaje da Kuma Ubanni?—igw 26 sakin layi na 1-2 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: ‘Ku je ku almajirtar’ da mutane.—Mat. 28:19, 20, Littafi Mai Tsarki.
Waƙa ta 89
Minti 20: Lokacin Yin Farin Ciki a Kowace Shekara. Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2012, shafuffuka na 31-32, sakin layi na 15-19. Ka sa ’yan’uwa su yi marmarin halartan taron yanki da za a yi a wannan shekarar. Ka ƙarfafa ’yan’uwa su duba tsarin ayyukan taron a dandalin jw.org/ha don su ga abubuwan da za a tattauna a taron.
Minti 10: Tambayoyin Masu Shela. Tattaunawa.
Waƙa ta 74 da Addu’a