Ku Ɗauki Mataki Nan da Nan
Tun daga lokacin da aka ƙaddamar da Yanar gizonmu da aka canja mata tsari, yawan mutanen da ke cika fom a dandalinmu don a yi nazari da su ya ƙaru sosai. Sabuwar hanyar yin wa’azi a inda akwai jama’a ma ta sa an sami ƙarin mutanen da suke so a yi nazari da su. Ofishin reshe yana ɗaukan mataki a kan wannan batun nan da nan. Alal misali, idan mutumin ya ba da sunansa ta dandalin jw.org ne, sai ofishin reshe ya sanar da dattawan da ke yankin mutumin cikin kwana biyu. Amma rahotanni daga yankuna da dama sun nuna cewa ba a je neman waɗanda suka ce a zo a yi nazari da su ba har bayan makonni da yawa. Ta yaya za mu tabbata cewa mun taimaki waɗannan mutanen kafin su daina sha’awar saƙonmu?—Mar. 4:14, 15.
Idan mutumin da ke son saƙonmu ba ya zama a yankinku, ku cika fom ɗin Please Follow Up (S-43) nan da nan kuma ku ba sakatare a taron ikilisiyarku na gaba. Sakataren ya ba da bayanin mutumin ga ikilisiyar da ke yankinsa ko kuma ya shigar da bayanin a sashen Congregation a dandalin jw.org sa’an nan ya aika zuwa ofishin reshe. Ya kamata ya yi hakan cikin kwana ɗaya ko biyu. Dattawa su riƙa shiga dandalinmu a kai a kai kuma idan aka sanar da su cewa su ziyarci wani, su ɗauki mataki nan da nan. Duk mai shela da aka tura ya je ya sami mutumin ya ɗauki wannan hakkin da muhimmanci sosai. Idan ba ku sami mutumin a gida ba, za ku iya rubuta sunanku da adireshinku ko kuma lambar wayarku kuma ku ajiye masa.