Gabatarwa
Hasumiyar Tsaro Mayu–Yuni
“Muna rarraba wa kowa wannan warƙar a yankinku. [Ka ba maigidan warƙar nan Mene Ne Ra’ayinka Game da Littafi Mai Tsarki? kuma ka yi masa tambayar da ke shafin farko. Ka nuna masa amsar a littafin 2 Timotawus 3:16, kuma ka ƙarfafa shi ya karanta warƙar idan ya sami lokaci.] Mutane da yawa ba su san cewa Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa ga irin waɗannan tambayoyin ba. [Ka nuna masa tambayoyin farko a talifi na farko a cikin Hasumiyar Tsaro ɗin.] Wannan mujallar ta bayyana yadda za ka iya samun amsoshin a naka Littafi Mai Tsarki.”
Awake! Mayu
“Kana ganin zai yiwu kowa ya sami gida mai kyau kuma a kawar da talauci gabaki ɗaya a duniya? [Ka bari ya ba da amsa.] Don Allah ka lura da alkawarin da Allah ya yi wa ’yan Adam a kan wannan batun. [Karanta Ishaya 65:21, 22.] Wannan talifin Awake! ya tattauna yadda Allah zai cika alkawuransa ga ’yan Adam da kuma yadda za mu iya moran wannan albarkar.”