Tsarin Ayyuka Makon 20 Ga Afrilu
MAKON 20 GA AFRILU
Waƙa ta 3 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 23 sakin layi na 10-18 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sama’ila 23-25 (minti 8)
Na 1: 1 Sama’ila 23:13-23 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Wane Alkawari Ne Littafi Mai Tsarki Ya Yi Game da Nan Gaba?—igw 16 sakin layi na 1-3 (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Yana da Kyau Mu Yi Tunani Kafin Mu Yi Magana?—Mis. 16:23 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: Ku zama masu hikima ta yin “amfani da lokaci” a hanya mafi inganci.—Afis. 5:15, 16, Littafi Mai Tsarki.
Waƙa ta 97
Minti 15: “Yadda Za A Yi Wa’azi ta Wajen Yin Amfani da Tebura da Amalanke.” Tattaunawa. Ka sa a yi wannan gwajin: Masu shela biyu suna tsaye a inda aka ajiye teburi ko amalanke. Mai shela na farko ya yi murmushi kawai yayin da wani mutum yake kallon teburin sa’ad da ya zo wucewa. Amma mai shela na biyu ya yi murmushi yayin da wani mutum ya zo kusa da teburin, sa’an nan ya soma magana da shi. Ta yaya za mu bi wannan dabarar ko da ba ma wa’azi da tebura ko amalanke?
Minti 15: Ku Sa Bikin Aurenku Ya Kasance da Daraja Sosai. Tattaunawa. Za ka iya yin tambayoyi na gaba: (1) Wane ne ke da hakkin kula da abubuwan da za su faru a wurin ɗaurin aure da kuma bikin aure? (1 Kor. 11:3; w06 11/1 shafi na 13, sakin layi na 10) (2) Me zai taimaka wa amarya ta yi adon da zai daraja Allah? (1 Tim. 2:9; 1 Bit. 3:3, 4) (3) Me ya sa ba zai dace amarya da angon su ci bashi don bikin aurensu ba?—fy babi na 2, sakin layi na 22, 23; Mis. 22:7; Rom. 13:8; 1 Tim. 6:6.
Waƙa ta 70 da Addu’a