’Yan’uwa Maza Matasa, Kuna Burin Yin Hidima a Cikin Ikilisiya?
1. Yaushe ne ɗan’uwa matashi ya kamata ya soma bin umurnin da ke 1 Timotawus 3:1?
1 “Idan mutum yana biɗan aiki . . . , nagarin aiki yake biɗa.” (1 Tim. 3:1) Waɗannan kalmomin da aka hure suna ƙarfafa ’yan’uwa maza su biɗi yin aiki don su cancanci yin hidima a cikin ikilisiya. Shin, wajibi ne sai kun zama manya kafin ku yi hakan? A gaskiya, ya fi kyau ku soma ba da kanku don yin hidima tun kuna ƙanana. Ta hakan za ku sami koyarwa da kuma damar nuna halaye masu kyau da za su sa ku cancanci yin aikin bayi masu hidima a lokacin da shekarunku sun kai. (1 Tim. 3:10) Idan kai ɗan’uwa ne matashi, ta yaya za ka yi burin yin hidima a cikin ikilisiya?
2. Ta yaya mutum zai iya kasancewa da wannan halin ba da kai?
2 Ba da Kai: Kada ku manta cewa kuna ba da kanku a cikin ikilisiya don yin nagargarun ayyuka ne, ba don neman suna ba. Saboda haka, ya kamata ku zama masu son taimaka wa ’yan’uwanku maza da mata. Wani abin da zai taimaka muku shi ne yin bimbini a kan misali mai kyau da Yesu ya kafa. (Mat. 20:28; Yoh. 4:6, 7; 13:4, 5) Ku roƙi Jehobah ya taimake ku ku ƙaunaci mutane. (1 Kor. 10:24) Shin, za ku iya taimakon ’yan’uwa tsofaffi ko naƙasassu da ke cikin ikilisiyarku? Za ku iya ba da kanku don nome ciyawa, yin shara, ko kuma yin wasu abubuwa don kula da Majami’ar Mulki? Za ku iya yin shiri don ba da jawabi a Makarantar Hidima ta Allah idan ainihin mai jawabin ya kasa bayarwa saboda wata larura? Idan kuka ba da kanku don taimakon mutane, hakan zai sa ku farin ciki.—A. M. 20:35.
3. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da dangantaka mai kyau tsakaninmu da Jehobah, kuma ta yaya za mu yi hakan?
3 Dangantaka Mai Kyau da Allah: Yana da muhimmanci mai hidima a cikin ikilisiya ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, maimakon ya dogara ga wani baiwa ko iyawa da yake da shi. Wanda yake da dangantaka mai kyau tsakaninsa da Jehobah, zai kasance da ra’ayin Jehobah da Yesu. (1 Kor. 2:15, 16) Yana nuna halaye masu kyau, wato, ‘’yar ruhu.’ (Gal. 5:22, 23) Shi mai himma ne a yin wa’azi kuma yana saka Mulkin Allah farko a rayuwarsa. (Mat. 6:33) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai zai sa ku kasance da halaye masu kyau. Hakan ya ƙunshi karanta Littafi Mai Tsarki kullum, karanta kowace fitowar Hasumiyar Tsaro da Awake!, yin shiri da kuma halartan taron ikilisiya. (Zab. 1:1, 2; Ibran. 10:24, 25) Sa’ad da manzo Bulus yake ƙarfafa Timotawus ya inganta ibadarsa, ya gaya masa: “Ka maida hankali da . . . koyarwarka.” (1 Tim. 4:15, 16) Saboda haka, ku riƙa yin shiri sosai idan kuna da jawabi a Makarantar Hidima ta Allah. Ku riƙa yin shiri kafin ku fita wa’azi kuma ku fita a kai a kai. Ku ƙafa maƙasudai masu kyau irin su hidimar majagaba, hidima a Bethel, ko kuma zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure. Kasancewa da dangantaka mai kyau tsakaninku da Jehobah zai taimaka muku ku “guje wa sha’awoyin ƙuruciya.”—2 Tim. 2:22.
4. Me ya sa kasancewa da aminci yake da muhimmanci?
4 Aminci: ’Yan’uwan da aka zaɓa su rarraba abinci wa Kiristoci mabukata a ƙarni na farko maza ne da aka yi “shaidarsu” cewa suna da aminci. Saboda haka, manzannin sun tabbata cewa za su yi aikin da kyau. Hakan ya ba manzannin dama su mai da hankali ga wasu muhimman ayyuka. (A. M. 6:1-4) Saboda haka, sa’ad da aka ba ku wani aiki a cikin ikilisiya, ku yi shi da ƙwazo. Ku bi misalin Nuhu, don ya bi umurnin da aka ba shi na gina jirgi sau da ƙafa. (Far. 6:22) Kasancewa da aminci yana da muhimmanci a gaban Jehobah kuma yana nuna cewa kuna da dangantaka mai kyau da Shi.—1 Kor. 4:2; ku duba akwatin nan, “Amfanin Horar da ’Yan’uwa.”
5. Me ya sa ya dace ’yan’uwa maza matasa su yi burin yin hidima a cikin ikilisiya?
5 Kamar yadda aka annabta, Jehobah yana hanzarta aikin tattara mutane. (Isha. 60:22) Abirejin mutane dubu ɗari biyu da hamsin ne suke yin baftisma kowace shekara. Saboda waɗannan sababbin da suke shigowa cikin ƙungiyar Jehobah, ana bukatar ƙwararrun maza waɗanda suke da dangantaka mai kyau tsakaninsu da Jehobah su yi hidima a cikin ikilisiya. Babu shakka, yanzu muna da ayyukan yi sosai a hidimar Jehobah fiye da dā. (1 Kor. 15:58) Shin, ’yan’uwa maza matasa, kuna burin yin hidima kuwa? Idan amsarku e ce, aiki mai kyau ne kuke biɗa!
[Bayanin da ke shafi na 2]
Saboda waɗannan sababbin da suke shigowa cikin ƙungiyar Jehobah, ana bukatar ƙwararrun maza waɗanda suke da dangantaka mai kyau tsakaninsu da Jehobah su yi hidima a cikin ikilisiya
[Akwati a shafi na 3]
Amfanin Horar da ’Yan’uwa
’Yan’uwa maza matasa da suka cancanta suna amfana sosai sa’ad da dattawa suka horar da su ta wajen ba su aiki. Wani mai kula da da’ira yana zaune a kan bagadi yana ƙarfafa wani mai shela bayan taro, sai ya lura cewa akwai wani matashi da yake tsaye kusa da su. Mai kula da da’irar ya tambayi matashin ko yana jiransa ne, matashin kuma ya ce an ba shi gatan share kan bagadin bayan an tashi taro. Iyayensa suna son su koma gida amma ba ya son ya koma gida ba tare da ya gama aikinsa ba. Hakan ya sa mai kula da da’irar farin ciki sosai kuma ya ba shi wuri nan da nan. Ya ce: “Dattawan wannan ikilisiyar suna mai da hankali ga horar da ’yan’uwa maza matasa da suka cancanta ta wajen ba su ayyuka a cikin ikilisiya. Saboda haka, ba na mamaki sa’ad da suka ba da sunan wani ɗan’uwa matashi don a naɗa shi bawa mai hidima a duk lokacin da na ziyarci ikilisiyarsu.”