Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 5/15 pp. 24-28
  • ’Yan’uwa Maza, Ku Yi Shuka Ga Ruhu Kuma Ku Yi Burin Samun Hakki!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ’Yan’uwa Maza, Ku Yi Shuka Ga Ruhu Kuma Ku Yi Burin Samun Hakki!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Burin Yin Aiki Mai Kyau
  • Ana Bukatar Halin Sadaukar da Kai
  • Ka Gina Muradin Yin Hidima
  • Ana Bukatan Haɗin Kai na Iyali
  • Za Ka Sake Yin Hidima Kuma?
  • Ka Sake Bincika Yanayinka
  • Ku Koyar Da ’Yan’uwa Maza Su Yi Burin Aikin Kula
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Bayi Masu Hidima?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Dattawa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 5/15 pp. 24-28

’Yan’uwa Maza, Ku Yi Shuka Ga Ruhu Kuma Ku Yi Burin Samun Hakki!

“Wanda ya shuka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbe rai na har abada.”—GAL. 6:8.

1, 2. Yaya Matta 9:37, 38 yake samun cikawa, kuma hakan ya sa ake bukatan menene a cikin ikilisiyoyi?

YANZU kuna shaida abubuwa da suke faruwa a tarihi! Ana yin aikin da Yesu Kristi ya ambata sosai. Yesu ya ce: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aiko ma’aikata cikin girbinsa.” (Mat. 9:37, 38) Jehobah Allah yana amsa irin waɗannan addu’o’i a hanya mai ban mamaki. A shekarar hidima ta 2009, adadin ikilisiyoyi na Shaidun Jehobah a dukan duniya ya ƙaru da 2,031, ya kai 105,298. Bisa abireji, mutane 757 ne suke yin baftisma kowace rana!

2 Irin wannan ƙaruwa ya sa ake bukatan ’yan’uwa maza da suka cancanta su yi ja-gora wajen koyarwa da kuma ziyarar ƙarfafawa a cikin ikilisiyoyi. (Afis. 4:11) Cikin shekaru da suka shige, Jehobah ya fito da maza da suka cancanta don su kula da bukatun tumakinsa, kuma muna da tabbaci cewa zai ci gaba da yin hakan. Annabci da ke rubuce a Mikah 5:5 ya tabbatar mana cewa a waɗannan kwanaki na ƙarshe, mutanen Jehobah za su samu “makiyaya bakwai” da “shugabannai takwas” da ke wakilta adadin maza da suka cancanta da za su yi ja-gora tsakaninsu.

3. Ka bayyana abin da yake nufi a yi ‘shuka ga ruhu.’

3 Idan kai ɗan’uwa ne da ya keɓe kansa ga Jehobah, menene zai taimake ka ka cancanci samun wannan gatan? Wani abu na musamman shi ne ka yi ‘shuki ga Ruhu.’ (Gal. 6:8) Yin hakan ya ƙunshi yin rayuwa a hanya da za ta sa ruhu mai tsarki na Allah ya rinjaye ka a rayuwa. Ka ƙuduri aniya ba za ka yi ‘shuka ga jiki’ ba. Kada ka bar abubuwa kamar jin daɗi, hutu, da nishaɗi su rage sha’awarka na ba da kanka ga hidimar Allah. Ya kamata dukan Kiristoci su yi ‘shuka ga ruhu,’ kuma da shigewar lokaci maza da suka yi hakan za su cancanta samun gata a cikin ikilisiya. Domin ana bukatan bayi masu hidima da dattawa sosai a yau, an shirya wannan talifin musamman domin maza Kiristoci. Saboda haka, ’yan’uwa maza, muna ariritarku ku yi addu’a sosai a kan wannan batun.

Ku Yi Burin Yin Aiki Mai Kyau

4, 5. (a) An aririci maza da suka yi baftisma su yi burin samun waɗanne gata a cikin ikilisiya? (b) Ta yaya mutum yake burin samun gata?

4 Namiji Kirista ba ya zama mai kula ba tare da yin ƙoƙari ba. Dole ne ya biɗa wannan “nagarin aiki.” (1 Tim. 3:1) Ya ƙunshi yin hidima ga ’yan’uwa masu bi ta wajen kula da bukatunsu. (Karanta Ishaya 32:1, 2.) Ɗan’uwan da yake burin samun gata da muradin da ya dace ba mai son iko ba ne. Maimakon haka, yana da muradi na rashin son kai ya amfane wasu.

5 Mutum yana biɗan ya zama bawa mai hidima kuma ya samu matsayin dattijo ta wajen yin ƙoƙari ya cika bukatun da aka kafa cikin Nassosi. (1 Tim. 3:1-10, 12, 13; Tit. 1:5-9) Idan kai, ɗan’uwa ne da ya keɓe kansa, ka tambayi kanka: ‘Ina fita aikin wa’azi sosai, kuma ina taimaka wa mutane su yi hakan? Ina ƙarfafa ’yan’uwana masu bi ta wajen nuna cewa na damu da lafiyarsu? An san ni da nazarin Kalmar Allah sosai? Ina kyautata kalami na kuwa? Ina kula da ayyukan da dattawa suka ba ni da kyau?’ (2 Tim. 4:5) Muna bukatan mu yi tunani sosai game da irin waɗannan tambayoyin.

6. Menene ainihin abin da zai sa mutum ya cancanci samun hakki a cikin ikilisiya?

6 Wata hanya da mutum zai cancanci samun hakki a cikin ikilisiya ita ce ta wajen samun ‘ƙarfafa da iko ta wurin Ruhun [Allah] cikin mutum na ciki.’ (Afis. 3:16) Mutum ya zama bawa mai hidima ko dattijo a cikin ikilisiyar Kirista ba batun zaɓansa a wani ofishi ba ne. Mutum yana samun wannan gatar ta wurin kyautata dangantakarsa da Jehobah. Ta yaya ake samu wannan dangantaka? Hanya ɗaya ita ce ta wurin yin “tafiya bisa ga Ruhu,” da kuma nuna ’yar ruhunsa. (Gal. 5:16, 22, 23) Yayin da ka nuna tabbaci cewa ka ƙware a ba ka ƙarin hakki, da kuma sa’ad da ka bi gargaɗin yin gyara, ‘ci gabanka zai bayyanu ga kowa.’—1 Tim. 4:15.

Ana Bukatar Halin Sadaukar da Kai

7. Yi wa mutane hidima ya ƙunshi me?

7 Yi wa mutane hidima ya ƙunshi yin aiki tuƙuru kuma yana bukatar halin sadaukar da kai. Domin masu kula na Kirista suna hidimar makiyaya na ruhaniya, matsalolin tumakin yana damunsu sosai. Ka lura da yadda hakkinsa na aikin makiyayi ya shafi manzo Bulus. Ya gaya wa ’yan’uwa masu bi a Korinti: “Daga cikin ƙunci mai-yawa da raɗaɗin zuciya na rubuta muku da hawaye da yawa; ba domin a baƙanta muku ciki ba, amma domin ku san ƙauna wadda na ke yi muku mafi yawa.” (2 Kor. 2:4) A bayane yake cewa Bulus ya sa zuciyarsa cikin aikinsa.

8, 9. Ka ba da misalan Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda maza suka kula da bukatun wasu.

8 Ana sanin maza da suke aiki tuƙuru domin bayin Jehobah da halin sadaukar da kansu. Alal misali, da kyar ne mu yi tsammani cewa Nuhu zai gaya wa mutane da suke cikin iyalinsa: ‘Ku sanar da ni sa’ad da aka gama gina jirgin domin na shiga tare da ku.’ Musa bai gaya wa Isra’ilawa da suke ƙasar Masar cewa: ‘Zan sadu da ku a Jar Teku. Ku isa wajen yadda za ku iya.’ Joshua bai taɓa faɗa ba cewa: ‘Ku sanar da ni sa’ad da ganuwar Yariko ya faɗi.’ Kuma Ishaya bai nuna wani ba kuma ya ce: ‘Ga shi! Ka aike shi.’—Isha. 6:8.

9 Yesu Kristi ne misali mafi kyau na mutum da ya ƙyale ruhun Allah ya motsa shi. Ya karɓi aikinsa na zama Mai Ceton ’yan Adam da yardan rai. (Yoh. 3:16) Bai kamata ƙauna na sadaukar da kai na Yesu ya motsa mu ma mu sadaukar da kanmu ba? Sa’ad da yake kwatanta yadda yake ji game da tumakin, wani da ya daɗe yana hidimar dattijo ya ce: “Kalaman Yesu ga Bitrus, ka kula da tumakina ya motsa ni sosai. Da shigewar shekaru, na fahimci yadda ’yan kalamai na ƙauna ko kuma ɗan alheri zai iya ƙarfafa mutum. Ziyarar ƙarfafawa aiki ne da nake jin daɗin yi sosai.”—Yoh. 21:16.

10. Menene zai motsa maza Kiristoci su yi koyi da misalin Yesu wajen yi wa mutane hidima?

10 Sa’ad da ya zo ga tumakin Allah, babu shakka maza da suka keɓe kansu a cikin ikilisiya suna son su nuna halin Yesu, wanda ya ce: Zan “ba ku hutawa.” (Mat. 11:28) Ba da gaskiya ga Allah da kuma ƙauna ga ikilisiya suna motsa maza Kiristoci su yi burin samun wannan aikin mai kyau, ba sa tunanin cewa sadaukarwar ta yi yawa ko kuma yana bukatan lokaci ainun. Idan wani ba ya son ya yi burin samun wani gata kuma fa? Wani ɗan’uwa zai iya kasancewa da muradin yin hidima a ikilisiya kuwa?

Ka Gina Muradin Yin Hidima

11. Yaya mutum zai kasance da muradin yin hidima ga wasu?

11 Idan jin cewa ba ka cancanta ba yana hana ka burin yin hidima ga wasu, ya dace ka yi addu’a don ruhu mai tsarki. (Luk 11:13) Ruhun Jehobah zai taimaka maka ka jimre da kowane damuwa da kake da shi game da wannan. Allah ne yake sa mutum ya kasance da muradin yin hidima ga wasu, gama ruhun Jehobah ne yake motsa ɗan’uwa ya yi burin samun hakki kuma ruhun ne ke ba da ƙarfin yin tsarkakar hidima. (Filib. 2:13; 4:13) Saboda haka, ya dace ka gaya wa Jehobah ya taimaka maka ka kasance da muradin karɓan gatar hidima.—Karanta Zabura 25:4, 5.

12. Ta yaya mutum zai samu isashen hikima don ya kula da hakkin da aka danƙa masa?

12 Domin ya lura cewa bukatun tumakin yana da wuya kuma kula da waɗannan bukatu zai ɗauki lokaci sosai, Kirista yana iya tsai da shawara ba zai yi burin samun wani gata ba. Ko kuma zai ji cewa ba shi da isashen hikima da zai yi waɗannan ayyukan. Idan haka ne, wataƙila zai samu hikima ta wajen yin nazarin Kalmar Allah da littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki sosai. Yana da kyau ya tambayi kansa, ‘Ina keɓe lokaci don nazarin Kalmar Allah, kuma ina yin addu’a don na samu hikima?’ Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙ. 1:5) Ka gaskata da wannan furcin da aka hure kuwa? Da yake amsa addu’ar Sulemanu, Allah ya ba shi “zuciya mai-hikima, mai-ganewa” da ta taimaka masa ya fahimci abin da ke nagari da mugunta sa’ad da yake yanke hukunci. (1 Sar. 3:7-14) Hakika, batun Sulemanu dabam ne. Duk da haka, muna da tabbaci cewa Allah zai ba da hikima ga maza da aka danƙa wa hakkin ikilisiya domin su kula da tumakinsa da kyau.—Mis. 2:6.

13, 14. (a) Ka bayyana yadda “ƙaunar Kristi” ta shafi Bulus. (b) Ta yaya ya kamata “ƙaunar Kristi” ta shafe mu?

13 Wani abin taimako wajen kasancewa da muradin yi wa mutane hidima shi ne yin tunani sosai game da dukan abin da Jehobah da Ɗansa ya yi dominmu. Alal misali, ka yi la’akari da 2 Korantiyawa 5:14, 15. (Karanta.) Ta yaya “ƙaunar Kristi tana i mana”? Ƙaunar da Kristi ya nuna ta wajen ba da ransa a madadinmu bisa nufin Allah tana da muhimmanci yayin da fahiminmu da godiyarmu a gare ta take ƙaruwa, hakan yana motsa zuciyarmu sosai. Bulus ya bar ƙaunar Kristi ta yi masa ja-gora. Ta hana shi aikatawa da son kai kuma ya taimaka masa ya sa yin hidima ga Allah da ’yan’uwansa masu bi a cikin ikilisiya da waje ya zama ainihin muradinsa.

14 Yin bimbini game da ƙaunar Kristi ga mutane yana motsa mu mu nuna godiya. A sakamako, mun fahimci cewa ba zai dace ba mu ci gaba da ‘shuka bisa ga jiki’ ta wajen biɗan makasudai na son kai da kuma yin rayuwa don mu gamsar da muradinmu. Maimakon haka, muna yin gyara don mu sa aikin da Allah ya ba mu farko a rayuwarmu. Mun motsa mu yi “bauta” ga ’yan’uwanmu don muna ƙaunarsu. (Karanta Galatiyawa 5:13.) Idan mun ɗauki kanmu a matsayin bayi da suke yin aiki cikin tawali’u a madadin bayin Jehobah da suka keɓe kansu, za mu bi da su cikin daraja da ladabi. Babu shakka, ba za mu yi koyi da halin yin sūka da Shaiɗan yake gabatarwa ba.—R. Yoh. 12:10.

Ana Bukatan Haɗin Kai na Iyali

15, 16. Wane hakki ne waɗanda suke cikin iyali suke da shi idan mai gida zai cancanta a naɗa shi bawa mai hidima ko dattijo?

15 Idan ɗan’uwa yana da mata da yara, za a yi la’akari da yanayin iyalinsa sa’ad da ake bincika ko ya cancanta ya zama bawa mai hidima ko dattijo. Hakika, ruhaniyar iyalinsa da halinsu zai shafi naɗawarsa. Wannan ya nanata muhimmancin matsayin iyalin wajen goyon bayan mai-gida da uba yayin da yake so ya yi hidima a ikilisiya a matsayin bawa mai hidima ko dattijo.—Karanta 1 Timotawus 3:4, 5, 12.

16 Jehobah yana farin ciki yayin da waɗanda suke cikin iyalin Kirista suke haɗa kai da juna. (Afis. 3:14, 15) Shugaban iyali yana bukatar ya daidaita wajen cika hakkokinsa na ikilisiya da yin shugabanci bisa iyalinsa “da kyau.” Saboda haka, yana da muhimmanci dattijo ko kuma bawa mai hidima ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da matarsa da kuma ’ya’yansa don su amfana daga Bautar Iyali kowane mako. Zai riƙa fita hidimar fage tare da su kullayaumi. Saboda haka, yana da muhimmanci waɗanda suke cikin iyali su haɗa kai da ƙoƙarce-ƙoƙarcen shugaban iyalin.

Za Ka Sake Yin Hidima Kuma?

17, 18. (a) Idan ɗan’uwa ya yi rashin hakkinsa, me yake bukata ya yi? (b) Wane ra’ayi ne ɗan’uwa da ya yi hidima a matsayin dattijo ko kuma bawa mai hidima a dā zai kasance da shi?

17 Wataƙila kai dattijo ne ko bawa mai hidima a dā amma yanzu ba ka yin hidima a wannan matsayin. Kana ƙaunar Jehobah kuma har ila kana da tabbaci cewa yana kula da kai. (1 Bit. 5:6, 7) An gaya maka cewa kana bukatar yin wasu canje-canje ne? Ka kasance a shirye don ka amince da laifinka kuma ka yi gyara da taimakon Allah. Ka guji yin fushi. Ka yi hikima, kuma ka nuna ra’ayi mai kyau. Wani dattijo da ya yi hidima na shekaru da yawa amma ya yi rashin gatarsa ya ce: “Na ƙudura aniya na ci gaba da yadda nake halartan taro, fita hidimar fage, da kuma karanta Littafi Mai Tsarki a lokacin da nake dattijo, makasudi da na iya cim ma wa. Na koyi yin haƙuri da tunanin cewa bayan shekara ɗaya ko biyu zan sake samun gata na, amma ya ɗauki kusan shekaru bakwai kafin na sake yin hidima a matsayin dattijo kuma. A waɗannan lokatan shawarar nan kada na yi kasala amma na ci gaba da yin burin samun gata ya taimake ni sosai.”

18 Idan kai ɗan’uwa ne a yanayi wanda aka kwatanta yanzu, kada ka yi sanyin gwiwa. Ka yi tunani a kan yadda Jehobah yake albarkar hidimarka da kuma iyalinka. Ka ƙarfafa iyalinka a ruhaniya, ka ziyarci masu ciwo, ka ƙarfafa waɗanda suka raunana. Mafi muhimmanci, ka daraja gatarka na yabon Allah da kuma yin shelar bishara na Mulki a matsayin Mashaidin Jehobah.a—Zab. 145:1, 2; Isha. 43:10-12.

Ka Sake Bincika Yanayinka

19, 20. (a) An aririce dukan ’yan’uwa maza da suka yi baftisma su yi menene? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?

19 Ana bukatar masu kula da kuma bayi masu hidima sosai a yau fiye da dā. Saboda haka, muna ariritar maza da suka yi baftisma su sake bincika yanayinsu kuma su tambayi kansu, ‘Idan ni ba bawa mai hidima ba ko kuma dattijo, waɗanne dalilai ne suka sa ba ni da wannan hakkin?’ Bari ruhun Allah ya taimaka maka ka sami ra’ayi mai kyau game da wannan batun.

20 Dukan waɗanda suke cikin ikilisiyar za su amfana daga ƙoƙarce-ƙoƙarce na halin sadaukar da kai na ’yan’uwansu masu bi. Yayin da muka sa hannu a yin ayyukan alheri, da rashin son kai, za mu girbe farin ciki da ake samu daga yi wa wasu hidima da yin shuki bisa ga ruhu. Amma, kamar yadda talifi na gaba zai nuna, kada mu ɓata zuciyar ruhu mai tsarki na Allah. Ta yaya za mu guji yin hakan?

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2009, shafuffuka na 30-32.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Menene annabcin da ke Mikah 5:5 ya tabbatar mana?

• Ka bayyana abin da halin sadaukar da kai ya ƙunsa?

• Ta yaya mutum zai kasance da halin yi wa wasu hidima?

• Ina muhimmancin haɗin kai na iyali idan miji zai cancanci yin hidima na bawa mai hidima ko kuma dattijo?

[Hotuna da ke shafi na 25]

Me za ka iya yi domin ka yi burin samun gata?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba