Ku Gabatar da Talifi Ɗaya, Amma Ku Ba da Mujallu Biyu
Mujallu biyu da suke fita kowane wata suna ɗauke da batutuwa dabam-dabam masu ƙayatarwa. Maimakon mu riƙa tattauna batutuwa da yawa sa’ad da muke wa wani wa’azi, zai dace mu tattauna batu ɗaya kawai. Idan mun lura da abin da maigidan yake so kuma mun san abin da ke cikin mujallun da muke ɗauke da su, za mu iya zaɓan wani batu a cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! da maigidan zai so. Alal misali, idan mun lura cewa akwai alamar yara a cikin gidan, za mu iya zaɓan talifin da ya tattauna batun iyali daga cikin mujallun. Idan namiji ne ya zo ya tarbe mu a bakin ƙofa, za mu iya tattauna wani abu da maza da yawa suna sha’awar tattaunawa, alal misali, za mu iya tattauna batun gwamnati nagari. Zai dace mu ba maigidan mujallu biyun idan yana son saƙonmu, ko da yake batu ɗaya ne muka tattauna da shi.