Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 24 ga Yuni, 2013. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan ne domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta a kowane mako.
1. Me ya sa Yesu ne ya cancanta ya bayyana Ubansa? (Yoh. 1:14; 3:18) [6 ga Mayu, w12 4/15 shafi na 4, sakin layi na 4]
2. Su waye ne suke “ratsa mutuwa zuwa cikin rai”? (Yoh. 5:24, 25) [13 ga Mayu, w08 4/15 shafi na 30, sakin layi na 8]
3. Me ya sa ya dace dukan Kiristoci su saurari ’yan’uwan Kristi? [20 ga Mayu, w09 2/15 shafi na 28, sakin layi na 16]
4. Mene ne muka koya daga yadda Yesu ya “yi hawaye” sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu? (Yoh. 11:35) [20 ga Mayu, w08 7/1 shafi na 10, sakin layi na 2-5]
5. Yaya ne Yesu zai “shirya” wa amintattun bayinsa wuri a sama? (Yoh. 14:2) [27 ga Mayu, w08 4/15 shafi na 32, sakin layi na 5]
6. Ta yaya ruhun Allah zai yi mana ja-gora da kyau? (Yoh. 14:26) [27 ga Mayu, w11 12/15 shafi na 14, sakin layi na 9]
7. Mene ne “waɗannan” abubuwa da Yohanna 21:15 ya yi maganarsu, kuma wane darasi ne za mu koya? [3 ga Yuni, w08 4/15 shafi na 32, sakin layi na 12]
8. Wane hali ne Kiristoci za su koya bisa ga Ayyukan Manzanni 2:44-47 da Ayyukan Manzanni 4:34, 35? [10 ga Yuni, w08 5/15 shafi na 30, sakin layi na 5]
9. Istifanus yana yin addu’a ne ga Yesu bisa ga abin da aka rubuta a Ayyukan Manzanni 7:59? [17 ga Yuni, w08 5/15 shafi na 31, sakin layi na 2]
10. Waɗanne abubuwa masu kyau ne Dokas ta yi wa mutane? (A. M. 9:36-42) [24 ga Yuni, w08 2/15 shafi na 10, sakin layi na 19]