Tsarin Ayyuka na Makon 24 ga Yuni
MAKON 24 GA YUNI
Waƙa ta 123 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 8, sakin layi na 10-15 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayyukan Manzanni 8-10 (minti 10)
Bitar Makarantar Hidima ta Allah (minti 20)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 93
Minti 10: “Ku Gabatar da Talifi Ɗaya, Amma Ku Ba da Mujallu Biyu.” Jawabi. Bayan ka kammala jawabin, ka sa a nuna yadda za a iya amfani da gabatarwa da ke shafi na 4 wajen soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a Asabar ta farko a watan Yuli.
Minti 10: Hidimarmu Ba a Banza Take Ba. (Ibran. 6:10) Ka tattauna bayanin da ke shafuffuka na 16-18 na Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2008. Ka ba masu sauraro dama su faɗi darussan da suka koya.
Minti 10: Littattafan da Za A Ba da a Watannin Yuli da Agusta. Tattaunawa. Ka ɗan bayyana wasu abubuwa da ke cikin ƙasidun da za a ba da. Ka sa a gwada yadda za a ba da ƙasidu biyu a cikin su. Ɗayan gwajin ya zama a kan ƙasidar Albishiri Daga Allah!, kuma a yi amfani da gabatarwa da ke shafi na 4 ko ɗaya daga cikin gabatarwa da ke cikin Hidimarmu ta Mulki na watan Maris 2013.
Waƙa ta 129 da Addu’a