Ka Tuna?
Ka ji daɗin karanta fitowar Hasumiyar Tsaro ta kwanan baya? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyin da ke gaba:
Ta yaya za mu iya kashe wutar yin magana da garaje?
Ya kamata mu bincika zuciyarmu. Maimakon sūkar ɗan’uwanmu, zai dace mu yi tunani a kan dalilin da ya sa muke yin hakan. Muna sūkarsa ne don abubuwan da muke yi su fi burge mutane sosai? Bugu da ƙari, sūkar mutane zai iya daɗa taɓarɓare yanayin.—8/15, shafi na 21.
Ta yaya dokokin da Allah ya ba Isra’ilawa suka nuna yadda yake son a bi da mata?
Mata Isra’ilawa suna da’yanci da kuma zarafin samun ilimi. An ba su girma da kuma daraja, kuma an kāre hakkinsu.—10/1, shafuffuka na 5-7.
Waɗanne abubuwa ne za su faru kafin ƙarshe ya zo?
Za a yi shelar “kwanciyar rai da lafiya.” Al’ummai za su kai wa “Babila Babba” hari kuma su halaka ta. Za a kai wa bayin Allah farmaki. Za a yi yaƙin Armageddon, bayan haka, za a jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar-matuƙa.—9/15, shafi na 4.
Ta yaya muke amfana da yake ba mu san lokacin da ƙarshe zai zo ba?
Da yake ba mu san lokacin da ƙarshe zai zo ba, yana sa mu nuna ainihin abin da ke cikin zuciyarmu. Hakan yana ba mu zarafin faranta wa Allah rai. Yana ƙarfafa mu mu ba da kai don taimaka wa mutane su dogara ga Allah da kuma Kalmarsa. Bugu da ƙari, yana sa mu koya darasi daga matsalolin da muke fuskanta kuma hakan yana ƙarfafa bangaskiyarmu.—9/15, shafuffuka na 24-25.
Su waye ne “taurari bakwai” da ke hannun damar Yesu da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 1:16, 20 suke wakilta?
Waɗannan taurarin suna wakiltar dattawa shafaffu, amma abin da aka ce musu zai iya shafan dukan dattawan ikilisiya.—10/15, shafi na 14.
Ta yaya Yesu ya kasance da tawali’u, kamar yadda littafin Ishaya 50:4, 5 suka ambata?
Ayoyin sun ce mutumin da ke da “harshe na koyayyun mutane” ba zai “bada baya ba.” Yesu ya kasance da tawali’u kuma ya mai da hankali ga abin da Jehobah ya koya masa. Yesu yana ɗokin koyan abubuwa daga Allah na gaskiya, ya lura da yadda Jehobah ya yi wa ’yan Adam masu zunubi jin ƙai.—11/15, shafi na 11.