Ka Tuna?
Ka karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwana kwanan nan sosai? Ka gwada ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
Ta yaya Sulemanu zai iya zama misalin kashedi a gare mu?
Allah ya albarkaci Sarki Sulemanu kuma ya yi amfani da shi. Amma a lokacin da yake sarauta, Sulemanu ya daina bauta wa Allah. Ya auri ’yar Fir’auna wadda take bauta wa gumaka kuma ya auri mata da yawa da suka sa ya daina bauta wa Jehobah. Muna bukatar mu guji koyon halaye marasa kyau. (K. Sha 7:1-4; 17:17; 1 Sar. 11:4-8)—12/15, shafuffuka na 10-12.
Yaya muka san cewa akwai Kiristoci shafaffu na gaske a duniya tun daga ƙarni na farko zuwa yanzu?
“Iri mai-kyau” yana nufin “’ya’yan mulki ke nan” a cikin almarar da Yesu ya yi game da “alkama” da “zawa.” (Mat. 13:24-30, 38) Zawan zai yi girma tare da alkama har sai lokacin kaka. Muna tare da shafaffu har yanzu, ko da yake ba za mu iya faɗa wanda rukunin nan na alkama yake wakilta ba.—1/15, shafi na 7.
Ta yaya za mu yi ƙoƙari mu magance halin yin hassada?
Hanyoyin da za su taimaka mana su ne: Ku ƙaunaci ’yan’uwanku da yin cuɗanya da masu bauta wa Allah da neman hanyoyin yin nagargarun ayyuka da kuma ‘yin farin zuciya tare da waɗanda ke farin zuciya.’ (Rom. 12:15)—2/15, shafuffuka na 16-17.
Waɗanne ƙa’idodi ne ya kamata mu tuna sa’ad da muke ba da shawara?
Ka fahimci yanayin da kyau. Ka guji ba da amsa da garaje. Ka kasance da tawali’u wajen yin amfani da kalmar Allah. Ka yi amfani da littattafai. Kada ka tsai da wa wasu shawara.—3/15, shafuffuka na 7-9.