Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 3/15 pp. 19-23
  • “Masu-adalci Za Su Haskaka Kamar Rana”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Masu-adalci Za Su Haskaka Kamar Rana”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misalin Alkama da Zawan
  • “Bar Su Duka Biyu Su Yi Girma Tare har Kaka”
  • Lokacin Kaka da Ake Jira da Daɗewa
  • “Za Su Haskaka Kamar Rana”
  • Kwatancin Alkama da Zawan
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • ‘Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • An Fallasa Maƙiyin Imani
    Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
  • ‘Bari Mulkinka Ya Zo’
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 3/15 pp. 19-23

“Masu-adalci Za Su Haskaka Kamar Rana”

“Sa’annan masu-adalci za su haskaka kamar rana a cikin mulkin Ubansu.”—MAT. 13:43.

1. Yesu ya yi amfani da misalai don ya bayyana waɗanne fannoni dabam-dabam na Mulki?

YESU KRISTI ya yi amfani da misalai ko almara masu yawa, don ya bayyana fannoni dabam-dabam na Mulki. Ya “faɗa wa taron da misalai; ba ya faɗa masu kome ba sai tare da misali.” (Mat. 13:34) A misalai na shuka iri na gaskiyar Mulki, Yesu ya nanata hakkin yanayin zuciyar mutum wajen karɓan saƙon, da kuma hakkin Jehobah wajen sa a samu girma na ruhaniya. (Mar. 4:3-9, 26-29) Yesu ya kuma kwatanta ƙaruwa na musamman na mutane da suka yi biyayya ga saƙon Mulki ko da yake da farko ba a cika ganin ƙaruwan. (Mat. 13:31-33) Ƙari ga hakan, ya nuna cewa ba dukan waɗanda suka saurari saƙon Mulkin ba ne talakawan wannan Mulkin da suka dace.—Mat. 13:47-50.a

2. A cikin misalin Yesu na alkama da zawan, menene iri mai kyau yake wakilta?

2 Amma, ɗaya daga cikin misalan Yesu ya mai da hankali ga tattara waɗanda za su yi sarauta da Yesu a Mulkinsa. Sau da yawa mutane suna kiransa almarar alkama da zawan, kuma yana rubuce a Matta sura ta 13. Amma a cikin wani misali Yesu ya gaya mana cewa irin da aka shuka “zancen mulki” ne, a cikin wannan misalin, ya gaya mana cewa iri mai kyau yana wakiltar wani abu dabam, wato, ‘’ya’yan mulki.’ (Mat. 13:19, 38) Waɗannan ba talakawan Mulkin ba ne, amma su “ya’ya,” ko magādan, Mulkin ne.—Rom. 8:14-17; Karanta Galatiyawa 4:6, 7.

Misalin Alkama da Zawan

3. Ka bayyana matsalar da mutumin da ke cikin misalin yake fuskanta da kuma yadda ya tsai da shawarar magance matsalar?

3 Ga misalin: ‘Mulkin sama yana kama da mutum wanda ya shuka iri mai-kyau cikin gonarsa: amma lokacinda mutane suna barci, maƙiyinsa ya zo, ya shuka zawan kuma a tsakanin alkama, ya tafi. Amma sa’anda hatsi ya yi girma, har ya yi ƙwaya, sa’annan zawan kuma suka bayyana. Sai bayin mai-gidan suka zo, suka ce masa, Malam, ba iri mai-kyau ba ka shuka a gonarka? Ina fa ta sami zawan? Ya ce masu, wani maƙiyi ya yi wannan. Bayin suka ce masa, kana so mu tafi mu tumɓuke su? Amma ya ce, A’a; kada ya zama lokacinda ku ke tumɓuken zawan, ku tumɓuke alkama tare da su. Bar su duka biyu su yi girma tare har kaka: lokacin kaka kuma in ce wa masu-girbi, Ku tattara zawan tukuna, a ɗaure su cikin kaya, domin a ƙone su: amma ku tattara alkama, ku kai rumbuna.’—Mat. 13:24-30.

4. (a) Wanene mutumin cikin misalin? (b) A wane lokaci ne Yesu ya soma shuka wannan irin, kuma yaya?

4 Wanene mutumin da ya shuka iri mai kyau a gonarsa? Yesu ya ba da amsar daga baya sa’ad da ya bayyana wa almajiransa: “Mai-shibkan iri mai-kyau Ɗan mutum ne.” (Mat. 13:37) Yesu, “Ɗan mutum,” ya shirya gonarsa don yin shuka a cikin shekaru uku da rabi na hidimarsa a duniya. (Mat. 8:20; 25:31; 26:64) Daga ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., zuwa gaba ya soma shuka iri mai kyau, wato, “’ya’yan mulkin.” Babu shakka, wannan shukar ta soma, sa’ad da Yesu a matsayin wakilin Jehobah ya soma zubo ruhu mai tsarki a kan almajiransa, ta hakan ya naɗa su ’ya’yan Allah.b (A. M. 2:33) Iri mai kyau ya yi girma ya zama alkama. Dalilin shuka iri mai kyau shi ne daga baya a tara cikakken adadin waɗanda za su zama sarakuna da Yesu a Mulkinsa.

5. Wanene maƙiyi a cikin misalin, kuma su wanene suke wakiltar zawan?

5 Wanene maƙiyin, kuma su wanene zawan? Yesu ya gaya mana cewa maƙiyin “Shaiɗan ne.” An kwatanta zawan a matsayin “ya’yan Mugun.” (Mat. 13:25, 38, 39) A zahiri, zawan da Yesu yake maganarsa a nan wataƙila irin ciyawar nan mai suna bearded darnel. Wannan shuka mai guba yana kama da alkama sosai sa’ad da yake girma kafin ya nuna. Wannan kwatanci ne mai kyau na jabun Kiristoci, waɗanda suke da’awar cewa su ’ya’yan Mulki ne amma ba su da hali mai kyau! Waɗannan Kiristoci na ƙarya waɗanda suke da’awar cewa su mabiyan Kristi ne, babu shakka su sashe ne na “zuriyar” Shaiɗan Iblis.—Far. 3:15.

6. A wane lokaci ne zawan ya soma bayyana, kuma ta yaya mutane suke “barci” a lokacin?

6 A wane lokaci ne waɗannan Kiristoci masu kama da zawa suka bayyana? “Lokacinda mutane suna barci,” in ji Yesu. (Mat. 13:25) A wane lokaci ne wannan? Mun samu amsar a cikin kalaman manzo Bulus ga dattawan Afisa: ‘Na sani bayan tashina kerketai masu-zafin hali za su shiga wurinku, ba za su kewaye wa garke ba; daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.’ (A. M. 20:29, 30) Ya gargaɗi waɗannan dattawa su kasance a faɗake a ruhaniya. Bayan da manzanni, waɗanda suke ‘hana’ ridda suka soma mutuwa, Kiristoci da yawa sun yi barci a ruhaniya. (Karanta 2 Tasalonikawa 2:3, 6-8.) A lokacin ne babban ridda ya soma.

7. Wasu cikin alkamar sun zama zawa ne? Ka ba da bayani.

7 Yesu bai ce alkamar za ta zama zawan ba amma an shuka zawan cikin alkamar. Saboda haka, wannan misalin ba ya nuni ga Kiristoci na gaskiya da suka bar gaskiya ba. Maimakon haka, yana nuna ƙoƙarin da Shaiɗan yake yi sosai don ya ɓata ikilisiyar Kirista ta wajen shigo da mugayen mutane a cikinta. A lokacin da manzo na ƙarshe, wato, Yohanna ya tsufa, wannan riddan ya riga ya bayyana sarai.—2 Bit. 2:1-3; 1 Yoh. 2:18.

“Bar Su Duka Biyu Su Yi Girma Tare har Kaka”

8, 9. (a) Me ya sa masu sauraron Yesu za su fahimci umurnin Maigidan ga bayinsa? (b) A cikar misalin, ta yaya alkamar da zawan suka yi girma tare?

8 Bayin Maigidan sun gaya masa matsalar kuma suka yi tambaya: “Kana so mu tafi mu tumɓuke [zawan]?” (Mat. 13:27, 28) Amsarsa ta kasance da ban mamaki. Ya gaya musu su ƙyale alkamar da zawan su yi girma tare har sai lokacin kaka. Almajiran Yesu za su fahimci wannan umurnin. Za su fahimci cewa zai yi wuya a bambanta alkamar daga zawa. Waɗanda suka san game da noma za su fahimci cewa tushen wannan zawan yana sarƙe na alkama.c Shi ya sa Maigidan ya ce su jira!

9 Haka nan ma, a cikin ƙarnuka da yawa, ɗarikoki dabam-dabam na Kiristendam sun ba da ’ya’yan zawa da yawa, da farko tsakanin Cocin Roma Katolika da na Orthodox kuma daga baya tsakanin rukunonin Farostatan da yawa da suka taso. Haka kuma an shuka iri ƙalilan na tabbatacciyar alkama a cikin duniya. Maigidan da ke cikin misalin ya jira lokacin yin girma na dogon lokaci cikin haƙuri har sai lokacin kaka ya zo.

Lokacin Kaka da Ake Jira da Daɗewa

10, 11. (a) A wane lokaci ne za a yi girbin? (b) Yaya ake kai alkama ta alama cikin rumbun Jehobah?

10 Yesu ya gaya mana: “Kaka kuma matuƙar zamani ce; masu-girbi mala’iku ne.” (Mat. 13:39) A kwanaki na ƙarshe na wannan mugun zamani, ana aikin warewa, za a tara ’ya’yan Mulkin kuma a ware su daga masu kama da zawa. Manzo Bitrus ya gaya mana game da wannan: “Lokaci ya yi da shari’a za ta faru a kan gidan Allah: idan kuwa a wajenmu ta faru, ina matuƙar waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?”—1 Bit. 4:17.

11 Ba da daɗewa ba bayan somawar kwanaki na ƙarshe ko kuma “matuƙar zamani,” aka soma yi wa masu da’awar cewa su Kiristoci na gaskiya ne shari’a, ko su “’ya’yan mulki” ne da gaske ko kuma “’ya’yan mugun.” A somawar girbin, da farko Babila Babba ta faɗi, sai aka tattara ’ya’yan Mulki. (Mat. 13:30) Amma ta yaya ake kai alkama ta alama yanzu zuwa cikin rumbun Jehobah? Za a kai waɗannan da aka girbe zuwa ikilisiyar Kirista da aka mai do, inda za su samu amincewar Allah da kāriya, ko kuma su samu ladarsu ta samaniya.

12. Har tsawon wane lokaci ne za a ci gaba da girbin?

12 Har tsawon wane lokaci ne aka yi shari’ar? Yesu ya ambata “lokacin” kaka, wanda yakan ci gaba har na tsawon wani lokaci. (R. Yoh. 14:15, 16) Shari’ar mutane ɗaɗɗaya da suke cikin shafaffu ta ci gaba a dukan kwanaki na ƙarshe. Za a yi hakan har sai sun samu hatiminsu na ƙarshe.—R. Yoh. 7:1-4.

13. A wace hanya ce zawan ke sa tuntuɓe, kuma yaya suke aikata mugunta?

13 Su wanene za a fitar daga Mulkin, kuma ta yaya suke sa tuntuɓe da aikata mugunta. (Mat. 13:41) Limaman Kiristendam masu kama da zawan sun yaudari miliyoyin mutane a cikin ƙarnuka da yawa. Sun yi hakan ta hanyar koyarwa da ba ta daraja Allah, “abin da ke sa tuntuɓe,” kamar koyarwa na horon har abada a wutar jahannama da kuma allah-uku-cikin ɗaya da ke rikitar da mutane. Shugabannin addinai da yawa sun kafa wa garkensu mummunan misali ta wajen yin abuta na zina da wannan duniya da kuma a wani lokaci ta hanyar halinsu na lalata. (Yaƙ. 4:4) Ƙari ga haka, Kiristendam tana ƙara amincewa da lalata a tsakanin mabiyanta. (Karanta Yahuda 4.) Duk da waɗannan abubuwan, sun ci gaba da nuna a waje cewa su masu ibada ne. ’Ya’yan Mulki suna farin ciki cewa an ware su daga irin wannan tasiri mai kama da zawa da kuma lalatattun koyarwa da ke sa tuntuɓe.

14. Ta yaya masu kama da zawan suke kuka da cizon haƙoransu?

14 Ta yaya masu kama da zawa suke kuka da cizon haƙoransu. (Mat. 13:42) “’Ya’yan mugun” suna baƙin cikin cewa “’ya’yan mulki” sun fallasa mugun yanayi na ruhaniya na waɗannan masu kama da zawa. Suna ɓata rai cewa tallafin da suke samu daga mabiyansu yana raguwa, kuma ba su da iko a kansu.—Karanta Ishaya 65:13, 14.

15. A wane azanci aka ƙone masu kama da zawan?

15 A wane azanci ne aka tattara zawan kuma aka ƙone su da wuta? (Mat. 13:40) Wannan yana nuni ga abin da zai faru da zawan a ƙarshe. Da yake an jefa su cikin wuta a alamance, hakan yana nuna cewa za su fuskanci halaka na dindindin. (R. Yoh. 20:14; 21:8) Za a kawar da jabun Kiristoci masu kama da zawa, da masu ruɗi a lokacin “ƙunci mai-girma.”—Mat. 24:21.

“Za Su Haskaka Kamar Rana”

16, 17. Menene Malachi ya annabta game da haikalin Allah, kuma yaya hakan ya soma cika?

16 A wane lokaci ne masu kama da alkama suka “haskaka kamar rana”? (Mat. 13:43) Game da tsabtace haikalin Allah, Malachi ya yi annabci: “Za ya zo a haikalinsa ba labari; mala’ikan alkawari kuma, wanda ku ke murna da shi, ga shi, yana zuwa, in ji Ubangiji mai-runduna. Amma wanene za ya daure da ranar zuwansa? wanene kuwa za ya tsaya kadan ya bayyana? Gama yana kama da wutar mai-gyaran ƙarfe, kamar sabulun mai-gyaran tufa; za ya kuwa zauna kamar mai-gyaran azurfa mai-tsarkakewarta, kuma za ya tsarkake ’ya’yan Levi, yana tsabtatar da su kamar zinariya da azurfa; har su miƙa ma Ubangiji hadayu cikin adalci.”—Mal. 3:1-3.

17 A zamani, wannan annabci ya soma cikawa a shekara ta 1918 sa’ad da Jehobah tare da “mala’ikan alkawari” Yesu Kristi, suka bincika haikali na ruhaniya. Malachi ya gaya mana abin da ya faru muddin aka gama wannan tsabtacewa: “Sa’annan za ku komo, ku rarrabe tsakanin adali da mugu, tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” (Mal. 3:18) Ƙarin aiki da Kiristoci na gaskiya da aka sake ƙarfafa suka samu ya nuna cewa a wannan lokacin ne aka soma girbi.

18. Menene Daniyel ya annabta zai faru a zamaninmu?

18 Annabi Daniyel ya yi maganar zamaninmu sa’ad da ya annabta: “Waɗanda ke da hikima kuma za su haskaka kamar walƙiyar sararin sama; waɗanda suka juya mutane da yawa kuma zuwa adalci za su haskaka kamar taurari har abada abadin.” (Dan. 12:3) Su waye ne waɗannan da suke haskakawa sosai? Shafaffu Kiristoci ne, tabbatacciyar alkama da Yesu ya yi maganarta a misalinsa na alkama da zawan! Taro mai girma masu kama da tumaki da suke ƙaruwa sun fahimci cewa ana “tattara” jabun Kiristoci masu kama da zawan. Sa’ad da suka soma tarayya da Isra’ila na ruhaniya da suka rage, waɗannan talakawa da suke da begen kasancewa a ƙarƙashin Mulki a nan gaba sun sa haskensu ya haskaka a wannan duniya mai duhu.—Zech. 8:23; Mat. 5:14-16; Filib. 2:15.

19, 20. Menene “’ya’yan mulkin” suke jira, kuma menene za mu tattauna a talifi na gaba?

19 A yau, “’ya’yan mulkin” suna ɗokin jiran ladarsu mai ɗaukaka a samaniya. (Rom. 8:18, 19; 1 Kor. 15:53; Filib. 1:21-24) Amma, kafin lokacin, dole ne su kasance da aminci, su ci gaba da haskakawa, su kasance dabam da “’ya’yan Mugun.” (Mat. 13:38; R. Yoh. 2:10) Dukanmu muna farin ciki cewa muna da gatan ganin sakamakon “tattara” wannan zawan a alamance a zamaninmu!

20 Amma wace dangantaka ce ke tsakanin waɗannan ’ya’yan Mulkin da taro mai girma da suke daɗa ƙaruwa, waɗanda suke da begen yin rayuwa har abada a duniya a matsayin talakawan Mulki? Talifi na gaba zai amsa wannan tambayar.

[Hasiya]

a Don samun bayani dalla-dalla na waɗannan misalai, ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuli, 2008, shafuffuka na 12-21.

b A cikin wannan almarar, yin shukar ba ta nufin yin aikin wa’azi da almajirantarwa, da zai kawo sababbi waɗanda za su zama shafaffu Kiristoci. Game da iri mai kyau da aka shuka cikin gonar, Yesu ya ce: “’Ya’yan mulki ke nan [bai ce “za su zama”] ba.” Shukar tana nuni ga naɗa waɗannan ’ya’yan Mulkin a cikin gonar duniya.

c Tushen wannan muguwar ciyawar yana sarƙe tushen alkama sosai, saboda haka idan an tuge su kafin girbi za a yi hasarar alkama.—Ka duba littafin nan Insight on the Scriptures, Littafi na ɗaya, shafi na 1178.

Ka Tuna?

A misalin Yesu na alkama da zawan, menene waɗannan sashe na misalin yake nufi?

• Iri mai kyau

• Mutumin da ya shuka irin

• Shuka irin

• Maƙiyin

• Zawan

• Lokacin girbi

• Rumbun

• Kuka da cizon haƙora

• Wuta

[Hotuna da ke shafi na 20]

Fentakos na shekara ta 33 A.Z. ne ya nuna somawar shuka iri mai kyau

[Hoton da ke shafi na 23]

Ana kai alkama ta alama yanzu zuwa cikin rumbun Jehobah

[Inda Aka Ɗauko]

Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba