Jehobah Yana Kāre Mu Don Mu Samu Ceto
“Ku da ke bisa ikon Allah kiyayayyu ta wurin bangaskiya zuwa ceto wanda yana nan a shirye ga bayyanuwa a ƙarshen zamani.”—1 BIT. 1:5.
MECE CE AMSARKA?
Ta yaya Jehobah ya jawo mu zuwa bauta ta gaskiya?
Ta yaya za mu ƙyale Jehobah ya ja-gorance mu da shawararsa?
Ta yaya Jehobah yake ƙarfafa mu?
1, 2. (a) Me ya sa muka tabbata cewa Allah zai taimaka mana mu kasance da aminci har ƙarshe? (b) Shin Jehobah ya san mu ƙwarai da gaske? Ka bayyana.
“WANDA ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.” (Mat. 24:13) Yesu ya yi amfani da waɗannan kalaman wajen bayyana sarai cewa wajibi ne mu kasance da imani har ƙarshe don mu samu ceto sa’ad da Allah ya halaka wannan muguwar duniya ta Shaiɗan. Amma hakan ba ya nufin cewa Jehobah yana son mu yi amfani da hikimarmu da kuma ƙarfinmu wajen jimrewa. Littafi Mai Tsarki ya ba mu wannan tabbacin: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Kor. 10:13) Mene ne hakan yake nufi?
2 Jehobah ya san kome game da mu da ƙalubalen da muke fuskanta da yanayinmu. Kuma hakan ya sa yana tabbatar cewa ba mu fuskanci jarabar da ta fi ƙarfinmu ba. Amma shin da gaske ne cewa Allah ya san mu sosai? Hakika. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Jehobah ya san kowannenmu sosai. Ya san abubuwan da muke yi kullum da kuma halayenmu. Ya kuma san abin da muke tunani.—Karanta Zabura 139:1-6.
3, 4. (a) Ta yaya misalin Dauda ya nuna cewa Jehobah ya san da kowanne mutum? (b) Wane aiki na musamman ne Jehobah yake cim ma a yau?
3 Shin abin mamaki ne a ce Allah ya san kowanne ɗan Adam da ba kome ba ne? Dauda marubucin zabura ya yi tunani a kan wannan kuma ya ce wa Jehobah: “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya; wane abu ne mutum, da ka ke tuna da shi?” (Zab. 8:3, 4) Wataƙila Dauda ya yi wannan tambayar domin yadda Jehobah ya kula da shi. Sa’ad da Dauda autan Jesse yake aiki a matsayin makiyayi, Jehobah ya ce shi mutum ne “gwargwadon zuciyarsa,” kuma ya zaɓe shi ya ja-gorance mutanensa. (1 Sam. 13:14; 2 Sam. 7:8) Mahaliccin sararin samaniya ya san abin da ke cikin zuciyar Dauda ko da yake shi makiyayi ne kawai. Ya yi tunani a kan irin farin cikin da Dauda ya yi sa’ad da ya san da hakan!
4 Yadda Jehobah yake kula da mu ma a yau yana da ban mamaki sosai. Yana tattara “muradin dukan dangogi” don su bauta masa. (Hag. 2:7) Yana kuma taimaka wa bayinsa don su kasance da aminci har ƙarshe. Muna bukata mu fahimci yadda Jehobah yake jawo mutane don su bauta masa domin mu iya fahimtar yadda yake taimaka mana mu kasance da aminci.
JEHOBAH YANA JAWO MUTANE
5. Ta yaya Jehobah yake jawo mutane ga Ɗansa? Ka ba da misali.
5 Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yoh. 6:44) Wannan ya nuna cewa wajibi ne Allah ya taimaka mana kafin mu soma bauta masa. Ta yaya Jehobah yake jawo mu ga Ɗansa? Yana yin amfani da aikin wa’azi da kuma ruhu mai tsarki. Alal misali, akwai wata rana a birnin Filibi, Bulus da waɗanda yake wa’azi a ƙasar waje tare da su sun haɗu da wata mata mai suna Lidiya kuma suka soma mata wa’azi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji kuwa ya buɗe zuciyarta, da za ta lura da abin da Bulus yana faɗi.” Babu shakka, Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarkinsa don ya taimaka mata ta fahimci wa’azin da ake mata. A sakamako, ita da iyalinta suka yi baftisma.—A. M. 16:13-15.
6. Ta yaya Jehobah ya jawo dukanmu ga bauta ta gaskiya?
6 Shin Lidiya ce kaɗai ta more wannan gatan? A’a. Idan ka keɓe kanka a matsayin Kirista, to Jehobah ne ya jawo ka ga bauta ta gaskiya. Kamar yadda Ubangiji ya lura cewa Lidiya tana da halin kirki, hakan ma ya lura cewa kana da hali mai kyau. Sa’ad da ka soma sauraron bishara, Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya taimaka maka ka fahimci abin da ake koya maka. (1 Kor. 2:11, 12) Ya albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ka yi don yin amfani da abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki. Kuma ya yi matuƙar farin ciki sa’ad da ka keɓe masa kanka. Ko shakka babu cewa tun sa’ad da ka soma bauta wa Jehobah, yana tare da kai sawu da kafa don ya taimaka maka.
7. Ta yaya muka san cewa Allah zai taimaka mana mu kasance da aminci?
7 Jehobah ya taimaka mana mu soma bauta masa, kuma zai ci gaba da taimaka mana mu kasance da aminci. Ya san cewa tun da ba mu soma bauta masa da kanmu ba, ba za mu iya yin nasara don bauta masa mu kaɗai ba. Sa’ad da manzo Bitrus yake magana da Kiristoci amintattu, ya ce: “Ku da ke bisa ikon Allah kiyayayyu ta wurin bangaskiya zuwa ceto wanda yana nan a shirye ga bayyanuwa a ƙarshen zamani.” (1 Bit. 1:5) Abin da Bitrus ya ce ya shafi dukan Kiristoci, domin dukanmu muna bukatar taimakon Allah don mu kasance da aminci.
JEHOBAH YANA KĀRE MU DON KADA MU YI ZUNUBI
8. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali don kada mu yi kuskure?
8 Matsin da muke fuskanta yau da kullum da kuma ajizancinmu zai iya sa mu daina mai da hankali ga bautarmu ga Jehobah kuma zai iya sa mu yi zunubi ba tare da saninmu ba. (Karanta Galatiyawa 6:1.) Abin da ya taɓa faruwa da Dauda ke nan.
9, 10. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Dauda don kada ya yi zunubi, kuma mene ne yake mana a yau?
9 Dauda ya nuna kamun kai sosai sa’ad da Sarki Saul yake neman ya kashe shi. Kuma sa’ad da Dauda ya samu zarafin yin ramako, bai yi hakan ba. (1 Sam. 24:2-7) Amma ba da daɗewa ba bayan wannan lokacin, Dauda bai nuna kamun kai ba. Yana bukatar abinci da kuma ruwa don shi da mazajensa, saboda haka ya roƙi wani Ba’isra’ila mai suna Nabal don ya taimaka masa. Amma Nabal ya yi masa baƙar magana, kuma hakan ya ɓata wa Dauda rai. A sakamako, Dauda ya tafi don ya halaka dukan maza da ke gidan Nabal. Dauda bai tuna cewa zai ɗauki alhakin jini, idan ya kashe mutanen da ba su san hawa ba ba su san sauƙa ba. Amma Abigail matar Nabal ta hana Dauda yin wannan kuskure. Sa’ad da Dauda ya san cewa Jehobah ne ya taimake shi, sai ya ce: “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni: mai-albarka ce hikimarki, mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini, da in rama wa kaina da hannuna kuma.”—1 Sam. 25:9-13, 21, 22, 32, 33.
10 Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin? Jehobah ya yi amfani da Abigail don ya hana Dauda yin zunubi. Kuma yana yin hakan da mu ma a yau. Ko da yake bai kamata mu sa rai cewa Allah zai aiko da wani ya tare mu a duk lokacin da muke son mu yi zunubi ba. Kuma ba za mu iya sanin abin da Allah zai yi a wani yanayi ba ko kuma abin da zai ƙyale ya faru don ya cika nufinsa ba. (M. Wa. 11:5) Amma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana sane da yanayinmu a kowane lokaci kuma zai taimaka mana mu kasance da aminci. Ya yi mana alkawari: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.” (Zab. 32:8) Ta yaya Jehobah yake ba mu shawara? Ta yaya za mu iya amfana daga wannan shawarar? Kuma yaya za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana wa mutanensa ja-gora a yau? Ka lura da yadda littafin Ru’ya ta Yohanna ya amsa waɗannan tambayoyin.
JEHOBAH YANA KĀRE MU TA WAJEN BA MU SHAWARA
11. Shin Jehobah ya san abin da ke faruwa a ikilisiyoyi a yau sosai? Ka bayyana.
11 A wahayin da aka rubuta a littafin Ru’ya ta Yohanna surori 2 da 3, an nuna cewa Sarki Yesu Kristi ya lura da abin da ke faruwa a ikilisiyoyi bakwai da ke Asiya Ƙarama. A wannan wahayin, Yesu ya lura da takamammun abubuwa da ke faruwa a kowace ikilisiya. A wasu yanayi ya ambata kowace ikilisiya, ya yaba mata ko kuma ya faɗa mata gyaran da take bukata ta yi. Mene ne hakan ya nuna? Bayan shekara ta 1914, ikilisiyoyin bakwai sun wakilci Kiristoci shafaffu. Kuma shawarar da aka ba waɗannan ikilisiyoyi bakwai ta shafi dukan ikilisiyoyin da ke duniya a yau. Saboda haka, za mu iya faɗa da tabbaci cewa Jehobah yana amfani da Ɗansa wajen yi wa mutanensa ja-gora a yau. Ta yaya za mu iya amfana daga wannan ja-gorar?
12. Ta yaya za mu iya ƙyale Jehobah ya yi mana ja-gora?
12 Hanya ɗaya da za mu iya amfana daga ja-gorar Jehobah ita ce ta yin nazari mu kaɗai. Jehobah yana yin amfani da littattafan da bawan nan mai-aminci mai-hikima yake wallafawa don ya gargaɗe mu. (Mat. 24:45) Amma don mu amfana daga wannan tanadin, wajibi ne mu keɓe lokaci don yin nazari da kuma yin amfani da darussan da muka koya. Idan muna nazarin mu kaɗai, hakan zai kāre mu daga yin zunubi. (Yahu. 24) Shin ka taɓa yin nazarin wani batu a cikin littattafanmu kuma ka ce, ‘Lallai, ni aka rubuta wa wannan abun.’ Zai dace ka amince cewa Jehobah ne yake maka gyara. Kamar yadda abokinka zai iya taɓa kafaɗarka don ya gaya maka wani abu, Jehobah zai iya yin amfani da ruhunsa don ya taimaka maka ka fahimci cewa kana bukatar yin gyara a halinka ko ayyukanka. Idan mun amince da ja-gorar ruhu mai tsarki, za mu ƙyale Jehobah ya yi mana ja-gora. (Karanta Zabura 139:23, 24.) Yanzu bari mu tattauna game da yawan lokaci da kuma ƙoƙarce-ƙoƙarcen da muke yi don yin nazari.
13. Me ya sa ya dace mu yi tunani a kan sa’o’i da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da muke yi sa’ad da muke nazari?
13 Idan mun cika ɓatar da lokaci don yin nishaɗi, ba za mu samu isashen lokaci don yin nazari na kanmu ba. Wani ɗan’uwa ya ce: “Yana da sauƙi sosai mu daina yin nazari na kanmu a kai a kai. Akwai nishaɗi sosai a yau fiye da dā kuma bai da tsada. Za mu iya samun shi a talabijin da kwamfuta da kuma wayar selula. Muna kewaye da shi.” Idan ba mu yi hankali ba, za mu riƙa ɓata lokaci sosai don yin nishaɗi kuma hakan zai cinye lokacin da za mu yi nazari da shi. (Afis. 5:15-17) Ya dace kowannenmu ya tambayi kansa: ‘Sa’o’i nawa ne nake yi ina yin nazarin Kalmar Allah? Shin sa’ad da nake da jawabi a taro ko ina shirya taro ne kawai nake yin nazari?’ Idan haka ne, za mu iya yin amfani da lokacin da muke yin nazari mu kaɗai ko yammar da muke Bauta ta Iyali don yin bimbini sosai. Kuma zai dace mu bincika Littafi Mai Tsarki kamar yadda muke yin bincike sa’ad da muke neman lu’u lu’u mai tamanin gaske. Idan mun yi hakan za mu samu hikima daga wurin Jehobah da za ta taimaka mana mu kasance da aminci har ƙarshe.—Mis. 2:1-5.
ƘARFAFA TANA TAIMAKA MANA MU JIMRE
14. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana lura da yadda muke ji?
14 Dauda ya fuskanci matsaloli da yawa a rayuwarsa. (1 Sam. 30:3-6) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Jehobah ya san yadda yake ji. (Karanta Zabura 34:18; 56:8.) Jehobah ya san yadda mu ma muke ji. Yana ƙarfafa mu duk sa’ad da muke da “karyayyar zuciya.” Waɗannan kalaman sun ƙarfafa Dauda kuma saboda haka, ya rera waƙa ga Jehobah. Ya ce: “Zan yi murna in yi farinciki cikin jinƙanka: gama kā ga ƙuncina; Kā san masifun raina.” (Zab. 31:7) Jehobah yana lura da matsalolin da muke fuskanta. Amma ban da haka, yana ƙarfafa mu don mu jimre da matsalolin da muke fuskanta. Hanya ɗaya da yake ƙarfafa mu ita ce ta tarurrukan Kirista.
15. Wane darassi ne labarin Asaph ya koya mana?
15 Labarin wani marubucin zabura mai suna Asaph ya nuna amfanin halartar tarurruka. Asaph ya yi sanyin gwiwa domin ya ci gaba da yin tunani cewa masu adalci suna shan wahala, amma wai miyagu suna yin nasara. Ya ce: “Gama zuciyata ta damu, na soku a cikina.” A sakamakon haka, ya kusan daina bauta wa Jehobah. Amma mene ne ya taimaki Asaph don hankalinsa ya dawo jikinsa. Ya ce: “Na shiga wuri mai-tsarki na Allah.” Ya daidaita ra’ayinsa ta wajen yin tarayya da masu bauta wa Jehobah. Ya lura cewa samun ci gaba da miyagu suke yi na ɗan lokaci ne kawai. Kuma ya lura cewa babu shakka, Jehobah zai daidaita kome. (Zab. 73:2, 13-22) Muna iya ji kamar Asaph. Muna iya yin sanyin gwiwa don muguntar da ke faruwa a duniyar Shaiɗan. Amma idan mun halarci taro tare da ’yan’uwanmu, za mu samu ƙarfafa kuma hakan zai sa mu ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.
16. Ta yaya za mu iya amfana daga misalin Hannatu?
16 Amma idan wani abin da ke faruwa a cikin ikilisiya ya sa halartar taro yana mana wuya kuma fa? Wataƙila ka rasa gatan da kake da shi kuma hakan ya kunyatar da kai sosai. Ko kuma wataƙila ka samu matsala da wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa. Idan kana da wannan matsalar, wataƙila labarin Hannatu zai taimaka maka. (Karanta 1 Sama’ila 1:4-8.) Abin da ya faru tsakanin ta da kishiyarta mai suna Peninnah ya ɓata mata rai sosai. Matsalar tana daɗa tsanani sosai duk shekara sa’ad da iyalin ta je yin hadaya ga Jehobah a Shiloh. Hannatu ta damu sosai har ‘ta riƙa kuka, ta ƙi cin abinci.’ Amma duk da haka, ba ta ƙyale wannan matsalar ta hana ta bauta wa Jehobah ba. Jehobah ya lura da amincinta kuma ya albarkace ta.—1 Sam. 1:11, 20.
17, 18. (a) A waɗanne hanyoyi ne muke samun ƙarfafa daga tarurrukanmu? (b) Yaya kake ji game da yadda Jehobah yake kula da kai?
17 Hannatu takan halarci tarurruka a kai a kai, kuma ya kamata Kiristoci a yau su yi koyi da ita. Kamar yadda muka sani, muna samun ƙarfafa a taronmu. (Ibran. 10:24, 25) Ƙaunar da ’yan’uwanmu maza da mata suke mana yana ƙarfafa mu sosai. Alal misali, abin da wani ya faɗa a jawabi ko kuma kalami zai iya ƙarfafa mu. Kafin mu soma taro ko bayan an tashi daga taro, ɗan’uwa zai iya saurari abin da za mu ce ko kuma ya faɗi abin da zai sanyaya zuciyarmu. (Mis. 15:23; 17:17) Muna samu matuƙar kwanciyar rai sa’ad da muka rera waƙa ga Jehobah. Muna bukatar ƙarfafa daga taro musamman sa’ad da muke da matsalar da ke ci mana tuwo a ƙwarya. A tarurruka ne Jehobah yake “ta’azantar” da mu kuma yake taimaka mana mu jimre da kuma kasance da aminci.—Zab. 94:18, 19.
18 Muna farin ciki sosai domin Jehobah yana kāre mu kuma yana taimaka mana mu jimre har ƙarshe! Yadda Jehobah yake kula da mu ya sa mu samu kāriya kamar Asaph, wani marubucin zabura wanda ya rera waƙa ga Jehobah. Ya ce: “Ka riƙe ni a hannuna na dama. Za ka bishe ni da shawararka.”—Zab. 73:23, 24.
[Hoto a shafi na 28]
Jehobah ya jawo ka ma zuwa bauta ta gaskiya
[Hoto a shafi na 30]
Jehobah zai kāre mu idan mun yi biyayya ga shawararsa
[Hoto a shafi na 31]
Ƙarfafa tana taimaka mana mu jimre