Bayarwa da Take Kawo Farin Ciki
GENIVAL, yana da zama a wani gari a ƙasar Brazil, yana ciyar da matarsa da kuma ’ya’yansa daga ɗan kuɗi da yake samu a aikinsa na gadi a asibiti. Duk da wahalar da yake sha, Genival yana ba da ushirinsa babu fasawa. “Wani lokaci iyalina takan kwana da yunwa,” in ji shi yana faɗa yana shafa tumbinsa, “amma ina so in bai wa Allah abin da ya fi kyau, ko da me zan sadaukar.”
Bayan da aka kore shi a aiki, Genival ya ci gaba da ba da ushirinsa. Limaminsa ya aririce shi ya gwada Allah ta wajen ba da kyauta mai yawa. Limamin ya tabbatar masa cewa Allah hakika zai yi masa albarka ƙwarai. Saboda haka, Genival ya yanke shawarar zai sayar da gidansa ya ba da kuɗin ga coci.
Ba Genival ba ne kawai yake da irin wannan sahihanci wajen bayarwa. Matalauta da yawa suna ba da ushiri domin cocinsu ya koyar da su cewa ushiri farilla ce cikin Littafi Mai Tsarki. Amma hakan gaskiya ne?
Ba da Ushiri da Kuma Dokar Musa
Dokar ba da ushiri ɓangaren Doka ce da Jehovah Allah ya bai wa ƙabilu 12 na Isra’ila ta dā fiye da shekaru 3,500 da suka shige. Dokar ta ce ushirin abin da aka samu a gona da kuma ’ya’yan itatuwa da kuma ushirin dabbobi a bai wa ƙabilar Lawi domin tallafa hidimarsu a mazauni.—Leviticus 27:30, 32; Litafin Lissafi 18:21, 24.
Jehovah ya tabbatar wa Isra’ilawan cewa Dokar ‘ba za ta yi musu wuya ba.’ (Kubawar Shari’a 30:11) Idan suka ci gaba da bin umurnin Jehovah cikin aminci, haɗe da na ba da ushiri, ya yi musu alkawarin kaka mai albarka. Domin kāriya, ƙarin ushiri da za a bayar kowacce shekara, ana yin amfani da wannan wajen biki na addini, domin haka ana keɓe wannan. Ta haka ‘baƙi, marayu, da kuma gwauraye’ za su samu abinci.—Kubawar Shari’a 14:28, 29; 28:1, 2, 11-14.
Dokar ba ta ce ga horon da za a yi ba idan wani ya ƙi ya ba da ushiri, amma farilla ce ga kowane Ba’isra’ile ya tallafa wa bauta ta gaskiya a wannan hanyar. Hakika, Jehovah ya tuhumi Isra’ilawa da suka yi watsi da ushiri a zamanin Malachi da yi ‘masa fashi na ushiri da kyauta.’ (Malachi 3:8, New International Version) Za a iya irin wannan tuhumar ga Kiristoci da ba su ba da ushiri ba?
Bari mu ga dalilin. Dokokin wata ƙasa ba sa aiki a wata ƙasa. Alal misali, dokar da ta tilasta wa masu mota su bi hannun hagu a Britaniya ba ta shafi direbobi ba a Faransa. Hakazalika, dokar da take bukatar ushiri ɓangare ne na alkawari tsakanin Allah da al’ummar Isra’ila. (Fitowa 19:3-8; Zabura 147:19, 20) Isra’ilawa ne kawai suke ƙarƙashin dokar.
Bugu da ƙari, ko da yake gaskiya ne cewa Allah ba ya canjawa, farillansa wani lokaci suna canjawa. (Malachi 3:6) Littafi Mai Tsarki ya faɗa babu tantama cewa mutuwar hadaya ta Yesu, a shekara ta 33 A.Z., ta “shafe,” ko kuma ta “kawar,” da Dokar tare da ‘umurnin su karɓi ushiri.’—Kolossiyawa 2:13, 14; Afisawa 2:13-15; Ibraniyawa 7:5, 18.
Bayarwa ta Kirista
Duk da haka, kyauta domin a tallafa wa bauta ta gaskiya har yanzu ana bukatarsu. Yesu ya umurci almajiransa su ‘zama shaidunsa, har iyakan duniya.’ (Ayukan Manzanni 1:8) Sa’ad da adadin masu bi ya ƙaru, haka bukatar malamai Kirista da kuma masu kula domin su ziyarci ikilisiyoyi su ƙarfafa su ta ƙaru. Gwauraye, marayu, da kuma wasu mabukata dole a kula da su a wani lokaci. Menene Kiristoci na ƙarni na farko suka yi domin su biya kuɗin da wannan ya ƙunsa?
Kusan shekara ta 55 A.Z., an roƙi Kiristoci na al’ummai a Turai da kuma Asiya Ƙarama su taimaka wa matalauciyar ikilisiya a Yahudiya. A cikin wasiƙarsa zuwa ga ikilisiyar da take Koranti, manzo Bulus ya kwatanta yadda aka tsara wannan ‘tattara kuɗi domin tsarkaka.’ (1 Korinthiyawa 16:1) Wataƙila ka yi mamaki game da abin da kalmomin Bulus suka nuna game da bayarwa ta Kiristoci.
Manzo Bulus bai rinjayi ’yan’uwansa masu bi ba domin su bayar da kuɗi. Kiristocin Makidoniya waɗanda suke “shan ƙunci mai-yawa” kuma suke cikin ‘talauci ainun’ ‘suka yi ta roƙonsa domin su saka hannu wajen bayarwa cikin wannan hidima domin tsarkakku.’—2 Korinthiyawa 8:1-4.
Hakika, Bulus ya ƙarfafa Korantiyawa da suka fi arziki su yi koyi da ’yan’uwansu a Makidoniya. Duk da haka, wani littafin bincike ya ce, bai ba da umurni ba, maimakon haka ya yi roƙo, ya ba da shawara, ya ƙarfafa. Bayarwa da yardar rai da kuma murna ba za su kasance ba a bayarwar Korantiyawa, da a ce an tilasta musu ne. Bulus ya sani cewa “Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai,” ba wanda yake bayarwa da “cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba.”—2 Korinthiyawa 9:7.
Bangaskiya da kuma ilimi haɗe da ƙauna ta gaskiya ga ’yan’uwa Kiristoci sun motsa Korantiyawan suka bayar da daɗin rai.—2 Korinthiyawa 8:7, 8.
“Yadda Ya Annita a Zuciyarsa”
Maimakon ambata ko nawa za a bayar ko kuma yawan ushiri, Bulus ya ba da shawara cewa “a kan rana ta fari ga bakwai kowane a cikinku shi ajiye ajiya, gwargwadon samuwa da ya ke yi.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; 1 Korinthiyawa 16:2) Ta wajen shiri da kuma ajiyar ɗan kuɗi a kai a kai, Korantiyawa ba za su ji an matsa musu ba su bayar da cicijewa ko kuma don motsin rai sa’ad da Bulus ya isa wajensu. Ga kowane Kirista, shawarar ko nawa zai bayar, wannan bai shafi kowa ba, abin da ya “annita a zuciyarsa” ne.—2 Korinthiyawa 9:5, 7.
Domin su yi girbi mai yawa, dole ne Korantiyawa su yi shuki mai yawa. Ba a taɓa ba da shawarar a “bayar a hana kai” ba. ‘Ba domin ku yi wahala ba,’ Bulus ya tabbatar musu. Bayarwa ‘abin karɓa ne gwargwadon abin da ke wurin mutum, ba gwargwadon abin da ba shi da shi ba.’ (2 Korinthiyawa 8:12, 13; 9:6) A wata wasiƙarsa ta baya, manzon ya yi gargaɗi: “Amma idan wani ba ya yi tattalin . . . na iyalinsa, ya musanci imani, gwamma marar-bangaskiya da shi.” (1 Timothawus 5:8) Bulus bai ƙarfafa a yi bayarwa da zai karya wannan mizanin ba.
Yana da muhimmanci da Bulus ya kula da ‘tattarawa domin tsarkakku’ da suke cikin bukata. Ba mu karanta a cikin Nassosi ba cewa Bulus ko kuma wasu manzanni sun tsara karɓan kyauta ko kuma karɓan ushiri domin su ci gaba da hidimarsu ba. (Ayukan Manzanni 3:6) Ko da yake yana godiya kullayaumi ga kyauta da ikilisiyoyi suka aika masa, Bulus ya guje ɗora wa ’yan’uwansa ‘nauyi.’—1 Tassalunikawa 2:9; Filibbiyawa 4:15-18.
Bayarwa da Yardar Rai a Yau
A bayyane yake cewa a ƙarni na farko, mabiyan Kristi sun bayar ne da yardar rai, ba ushiri ba. Duk da haka, za ka yi mamaki idan wannan har yanzu ita ce hanya mafi kyau na samun kuɗi da za a ci gaba da wa’azin bishara kuma a kula da Kiristoci waɗanda suke da bukata.
Ka yi la’akari da wannan. A shekara ta 1879, edita na wannan jaridar ya faɗa a fili cewa ba za su “taɓa roƙo ba ko kuma su tuntuɓi mutane domin agaji.” Wannan shawarar ta kawo wani cikas ne ga ƙoƙarin Shaidun Jehovah su yaɗa gaskiya ta Littafi Mai Tsarki?
A yanzu, Shaidun suna raba Littafi Mai Tsarki, littattafai na Kirista, da wasu littattafai a ƙasashe 235. Hasumiyar Tsaro, jaridar ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki, da farko ana buga 6,000 kowane wata a cikin harshe ɗaya. Amma tuni ta zama sau biyu a wata kuma ana buga fiye da 24,000,000 a cikin harsuna 146. Domin su tsara aikinsu na ilimantarwa a duniya, Shaidun sun gina ko kuma sun tsayi wuraren gudanar da ayyukansu a ƙasashe 110. Bugu da ƙari, sun gina dubban wuraren taruwa haɗe da manyan majami’u domin taro masu girma domin mutane da suke so su ƙara ilimi na Littafi Mai Tsarki.
Ko da yake biyan bukatu ta ruhaniya shi ya fi muhimmanci, Shaidun Jehovah ba sa watsi da bukatun rayuwa na ’yan’uwansu masu bi. Sa’ad da ’yan’uwansu suka wahala domin yaƙe-yaƙe, girgizar ƙasa, fari, ko kuma hadari, suna tanadin magunguna, abinci, tufafi, da kuma wasu abubuwa da suka wajaba babu ɓata lokaci. Dukan waɗannan suna samun kuɗaɗansu ne ta wurin ba da kyauta da Kiristoci suke yi da kuma ikilisiyoyi suke yi.
Domin a inganta, ba da kyauta da yardar rai ta ɗauke nauyi daga waɗanda ba su da shi, kamar su Genival, da aka ambata a baya. Abin farin ciki, kafin ya sayar da gidansa, Maria Mashaidiyar Jehovah mai aikin wa’azi na cikakken lokaci ta ziyarci Genival. “Wannan taɗin ya ceci iyalina daga wahala,” in ji Genival.
Genival ya fahimci cewa aikin Ubangiji bai dangana bisa ushiri ba. Hakika, ushiri ba farilla ta Nassi ba ce kuma. Ya fahimci cewa Kiristoci suna samun albarka idan suka bayar, amma bai wajaba su bayar fiye da abin da suke da shi ba.
Bayarwa da yardar rai ya kawo wa Genival farin ciki ta gaske. Ya furta farin cikinsa da cewa: “Ƙila na ba da kashi goma ko kuma a’a, amma ina farin ciki da abin da nake bayarwa, kuma na tabbata cewa Jehovah ma yana farin ciki.”
[Box/Pictures on 6]
Shugabannin Coci na Farko Sun Koyar da Ushiri Ne?
“Masu arziki a tsakaninmu sun taimaki matalauta . . . Waɗanda suke da hannu da shuni, kuma suna da yardar rai, sun ba da abin da suke gani ya dace.”—The First Apology, Justin Martyr, a misalin 150 A.Z.
“Hakika Yahudawa sun biya ushiri na kayansu da suka keɓe ga Allah, amma Kiristoci sun keɓe dukan kayansu don nufin Ubangiji, . . . yadda wannan gwauruwa ta ba da dukan dukiyarta ga Allah.”—Against Heresies, Irenaeus, a misalin 180 A.Z.
“Ko da yake muna da asusunmu, bai ƙunshi kuɗin sayan ceto ba, kamar na addini da yake da farashi. Sau ɗaya a wata, idan ya ga dama, kowa yana ba da ɗan kyauta; amma idan haka zai faranta masa rai, kuma idan yana da abin yin hakan: domin babu tilas; duka da yardar rai ne.”—Apology, Tertullian, a misalin 197 A.Z.
“Sa’ad da Coci ya faɗaɗa kuma wasu ɓangarori suka taso, ya zama wajibi a kafa doka da zai kasance hanyar tallafawa da ta dace kuma na dindindin ga shugabannan addini. Saboda haka, aka ɗauko biyan ushiri daga Tsohuwar Doka . . . Dokar ta farko game da batun kamar tana ƙunshe cikin wasiƙar bishop da suka taru a Tours a shekara ta 567 da kuma [littafin] Taro na Macon a shekara ta 585.”—The Catholic Encyclopedia.
[Inda aka Dauko]
Tsaba ta kuɗi, sama a hannun hagu: Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.
[Hoto a shafi nas 4, 5]
Bayarwa da yardar rai tana kawo farin ciki
[Hotuna a shafi na 7]
Ta bayarwa da yardar rai ake samun kuɗin ci gaba da aikin wa’azi, kayan agaji, da gina wuraren taro