Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 12/1 pp. 26-31
  • ‘Ku Nuna Ku Masu Godiya Ne’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Nuna Ku Masu Godiya Ne’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dalilai na Yin Godiya
  • Darussa Uku Daga Dokar Musa
  • Furcinmu na Godiya
  • Ka Koya Kuma Ka Riƙe Ruhu na Majagaba
  • Nuna Godiya da ‘Wadatarmu’
  • Bayarwa da Take Kawo Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Kuna Ba da Zakka Kuwa?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • “Ina Ƙaunar Shari’arka Ba Misali!”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 12/1 pp. 26-31

‘Ku Nuna Ku Masu Godiya Ne’

“Bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatanku . . . ku zama masu-godiya.”—KOLOSSIYAWA 3:15.

1. Wane saɓani muka gani tsakanin ikilisiyar Kirista da kuma duniyar da take ƙarƙashin tasirin Shaiɗan?

A CIKIN ikilisiyoyi 94,600 na Shaidun Jehovah a kewaye da duniya, muna ganin halin godiya. Ana soma kowanne taro kuma a rufe da addu’ar da ta haɗa da godiya ga Jehovah. Sau da yawa muna jin furcin “godiya,” daga bakin manya da ƙanana da kuma sababbi ko kuma waɗanda suka daɗe su Shaidu ne da suke bauta cikin zumunci da farin ciki. (Zabura 133:1) Hakika wannan ya saɓa da son kai da ke tsakanin mutane da yawa da ‘ba su san Jehovah ba kuma ba sa biyayya da bishara’! (2 Tassalunikawa 1:8) Muna zama cikin duniya ta rashin godiya. Kuma ba abin mamaki ba ne idan muka tuna wanda shi ne allahn wannan duniya—Shaiɗan Iblis, wanda ya fi da son kai, wanda fahariyarsa da halin tawaye ke shafan dukan jama’a!—Yohanna 8:44; 2 Korinthiyawa 4:4; 1 Yohanna 5:19.

2. Wane gargaɗi muke bukatar mu bi, kuma waɗanne tambayoyi za mu bincika?

2 Ko da yake duniyar Shaiɗan ta kewaye mu, muna bukatar mai da hankali domin kada halayensu ya shafe mu. A ƙarni na farko, manzo Bulus ya tunasar da Kiristoci a Afisus: “Inda ku ke tafiya a dā bisa ga zamanin wannan duniya, ƙarƙashin sarkin ikon sararin sama, ruhun da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara; a cikinsu kuwa mu duka muna zamanmu a dā a cikin sha’awoyin jikinmu, muna bin gurin jiki da na tunani; bisa ga tabi’a kuma ’ya’yan fushi ne, kamar sauran mutane.” (Afisawa 2:2, 3) Mutane da yawa a yau ma haka suke. To, ta yaya za mu iya riƙe halin godiya? Wane taimako Jehovah ya yi tanadinsa? A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna da gaske cewa muna godiya?

Dalilai na Yin Godiya

3. Domin me muke godiya ga Jehovah?

3 Muna bukatar mu yi godiya ga Jehovah Allah ne, Mahaliccinmu kuma Mai Ba da Rai, musamman idan muka yi tunanin wasu cikin kyautarsa masu yawa da yake ba mu. (Yaƙub 1:17) Kowacce rana, muna gode wa Jehovah cewa muna da rai. (Zabura 36:9) A kewaye da mu, muna ganin tabbacin ayyukan Jehovah, kamar su rana, wata, da kuma taurari. Arzikin ƙasa da ke tallafa wa rai, yanayin iska da ta dace, da kuma kewayar abubuwan rai masu wuyan ganewa duka suna tabbatar da dalilin yin godiya ga Ubanmu mai ƙauna na samaniya. Sarki Dauda ya rera haka: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka; ko da ni ke so in bayyana su in bada labarinsu, sun fi gaban lissafi.”—Zabura 40:5.

4. Me ya sa ya kamata mu yi godiya ga Jehovah domin tarayya ta farin ciki da muke mora a ikilisiyoyi?

4 Ko da yake ba ma cikin aljanna ta zahiri, bayin Jehovah a yau suna moran zama cikin aljanna ta ruhaniya. A Majami’un Mulki namu, a manyan taro da kuma ƙanana, muna ganin aikin ruhun Allah a wurin ’yan’uwanmu masu bi. Hakika, sa’ad da suke wa’azi ga mutane da suke da ko kuma ba su da addini, wasu Shaidu suna yin nuni ga abin da Bulus ya kwatanta cikin wasiƙarsa ga Galatiyawa. Da farko suna ambata “ayyukan jiki” sai su tambayi masu sauraronsu abin da suka lura. (Galatiyawa 5:19-23) Yawanci sukan yarda cewa hakan na kwatanta jama’ar duniya a yau. Sa’ad da aka nuna musu kwatancin ruhun Allah kuma aka gayyace su zuwa Majami’ar Mulki su ga tabbacin wannan da kansu, mutane da yawa sukan yarda da sauri cewa: “Allah yana wurinku.” (1 Korinthiyawa 14:25) Kuma wannan ba a Majami’ar Mulki ba kawai. Duk inda ka je, idan ka sadu da ɗaya cikin Shaidun Jehovah da suke fiye da miliyan shida, za ka ga hali iri ɗaya na farin ciki da murna. Hakika, wannan tarayya mai ƙarfafawa dalili ne na yin godiya ga Jehovah, wanda yake ba da ruhunsa domin ya yiwu.—Zephaniah 3:9; Afisawa 3:20, 21.

5, 6. Ta yaya za mu nuna mu masu godiya ne ga fansar, kyautar Allah mafi girma?

5 Kyauta mafi kyau, wadda kamiltacciya ce da Jehovah ya bayar, ita ce ta Ɗansa, Yesu, wanda ta wurinsa aka tanadar da hadayar fansa. “Idan Allah ya ƙaunace mu,” in ji manzo Yohanna, “ya kamata mu kuma mu yi ƙaunar junanmu.” (1 Yohanna 4:11) Hakika, muna nuna mu masu godiya ne ga fansar ba kawai ta furta ƙauna da kuma godiya ga Jehovah ba amma kuma ta yin rayuwa a hanyar da za ta nuna ƙauna ga wasu.—Matta 22:37-39.

6 Za mu iya ƙara koyo game da nuna godiya ta wurin bincika hanyar da Jehovah ya bi da Isra’ila ta dā. Ta wurin Dokar, wadda ya ba wa al’ummar ta wurin Musa, Jehovah ya koya wa mutanen darussa da yawa. “A cikin shari’a kana da surar sani da surar gaskiya,” za mu koyi abubuwa da yawa da za su taimake mu mu bi gargaɗin Bulus: “Ku zama masu-godiya.”—Romawa 2:20; Kolossiyawa 3:15.

Darussa Uku Daga Dokar Musa

7. Ta yaya tsarin ba da zakka ya ba wa Isra’ilawa zarafin nuna godiyarsu ga Jehovah?

7 A cikin Dokar Musa, Jehovah ya yi tanadin hanyoyi uku da Isra’ilawa za su iya nuna godiya daga zuciya ga nagartansa. Da farko, akwai batun zakka. Kashi ɗaya cikin goma na amfanin gona, haɗe da “zakkan garke na shanu, da na tumaki,” za ta zama “mai-tsarki ga Ubangiji.” (Leviticus 27:30-32) Sa’ad da Isra’ilawa suka yi biyayya, Jehovah ya albarkace su sosai. “Ku kawo dukan zakka a cikin ma’aji, domin abinci ya samu a gidana, ku gwada ni hakanan yanzu, in ji Ubangiji mai-runduna, ko ba zan buɗe muku sakatan sama ba, in zuba muku da albarka, har da ba za a sami wurinda za a karɓa ba.”—Malachi 3:10.

8. Menene ya bambanta hadayar ba da kyauta daga zakka?

8 Na biyu, ban da farilla ta zakka, Jehovah ya shirya Isra’ilawa su ba da kyauta. Ya ce wa Musa ya gaya wa Isra’ilawa: “Kadan kun shiga cikin ƙasa inda zan kawo ku, za ya zama, kadan kun ci abincin ƙasa, za ku kawo ma Ubangiji hadaya ta cirawa.” Su kawo wasu cikin girbin farko “cikin ɓarjen[su] za [su] kawo waina” a ba da shi “hadaya ta cirawa ga Ubangiji,” da dukan tsararrakinsu. Ka lura cewa ba a ba da ainihin yawan girbin farko na waɗannan abubuwa ba. (Litafin Lissafi 15:18-21) Amma da Isra’ilawa suka ba da hadaya ta godiya, sun tabbata za su sami albarka daga Jehovah. Makamancin tsarin ya kasance game da haikali na wahayin Ezekiel. Mun karanta: “Na fari cikin dukan ’ya’yan fari na kome, da kowace hadaya ta cirawa ta kome, wajen dukan hadayunku, sai su zama na [firistoci]: kuma za ku ba [firist] mafi kyau na gārinku, domin albarka ta zama a bisa kan gidanka.”—Ezekiel 44:30.

9. Menene Jehovah ya koyar ta wurin tanadin yin kala?

9 Na uku, Jehovah ya shirya tsarin yin kala. “Sa’anda ku ke girbin amfanin ƙasarku kuma,” Allah ya ce, “ba za ka ƙarasa girbin ƙusurwoyin gonarka ba, ba kuwa za ka tattara kalar amfaninka ba. Ba za ka girbe kalar gonar anab naka, ba kuwa za ka tattara ’ya’yan gonar anab naka waɗanda suka fāɗi: za ka bar ma masu-mayata da baƙo: ni ne Ubangiji Allahnku.” (Leviticus 19:9, 10) Har ila, ba a ambata ainihin yawan abin da ake bukata ba. Ya rage ga kowanne Ba’isra’ile ne ya tsai da yawan yadda zai ƙyale wa mabukata. Sarki Sulemanu mai hikima ya bayyana: “Mai-jin tausayin fakirai yana bada rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” (Misalai 19:17) A ta haka, Jehovah ya koyar da juyayi da kuma kulawa da tsiyayyu.

10. Menene ya sami mutanen Isra’ila da suka kasa nuna godiyarsu?

10 Jehovah ya albarkaci Isra’ila sa’ad da suka kawo zakka, ba da kyauta, kuma yi wa tsiyayyu tanadi. Amma sa’ad da mutanen Isra’ila suka kasa nuna godiya, sun yi rashin tagomashin Jehovah. Wannan ya kai su cikin bala’i a ƙarshe kuma suka shiga bauta. (2 Labarbaru 36:17-21) To, waɗanne darussa muka koya?

Furcinmu na Godiya

11. Wace hanya ce musamman za mu iya nuna godiyarmu ga Jehovah?

11 Muhimmiyar hanya da za mu iya yin yabo ga Jehovah kuma mu nuna godiyarmu ma ya shafi “hadaya.” Hakika, mu Kiristoci ba ma ƙarƙashin Dokar Musa, da za a bukaci mu ba da hadayar dabbobi ko ’ya’yan itace ba. (Kolossiyawa 2:14) Duk da haka, manzo Bulus ya aririce Kiristoci Ibraniyawa: “Ta wurinsa fa bari mu miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa.” (Ibraniyawa 13:15) Ta wurin yin amfani da iyawarmu da kuma wadatarmu mu ba da hadayar yabo ga Jehovah, ko a hidimar fage ko a “taron jama’a” na ’yan’uwa Kiristoci, za mu furta godiyarmu daga zuci ga Ubanmu na samaniya mai ƙauna, Jehovah Allah. (Zabura 26:12) A yin haka, me za mu koya a hanyoyi da Isra’ilawa suka nuna godiyarsu ga Jehovah?

12. Game da hakkinmu na Kirista, me za mu koya daga tsarin zakka?

12 Na farko, kamar yadda muka gani, batun zakka babu zaɓe ciki; kowanne Ba’isra’ile yana da wannan hakkin. Mu Kiristoci muna da hakkin mu sa hannu a hidima kuma mu halarci taron Kirista. Ayyukan nan babu na zaɓe ciki. Yesu ya faɗa cikin annabcinsa mai girma game da zamanin ƙarshe: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14; 28:19, 20) An hure manzo Bulus ya rubuta game da taron Kirista: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Muna nuna godiyarmu ga Jehovah sa’ad da muka karɓi hakkinmu da farin ciki na mu yi wa’azi mu koyar kuma mu yi tarayya a kai a kai da ’yan’uwanmu a taron ikilisiya, muna ɗaukan wannan gata ce kuma daraja.

13. Wane darasi ke cikin tsarin ba da kyauta da kuma yin kala?

13 Ban da haka ma, za mu iya amfana daga bincika tanadi biyu da Isra’ilawa suke nuna godiyarsu—ba da kyauta da kuma yin kala. Dabam da zakka, da aka tsara ta ainihi, ba da kyauta ta yardan rai da kuma yin kala ba sa bukatar a ambata ainihin yawansu ba. Maimakon haka, sun yarda wa bawan Jehovah ya nuna godiyarsa daga zuciyarsa. Haka nan ma, ko da yake mun fahimta cewa sa hannu cikin hidima da kuma halartan taron Kirista sune hakkin da kowanne bawan Jehovah ke da shi, muna sa hannu da zuciya ɗaya da niyya kuwa? Muna ganinsu zarafi ne na nuna godiyarmu ta zuci ga dukan abin da Jehovah ya yi dominmu? Muna sa hannu a sake cikin ayyukan nan, yadda yanayin kowannenmu ya yarda mana? Ko kuwa muna ɗaukan dukan wannan cewa hakki ne kawai da za mu cika? Hakika, waɗannan tambayoyi da dole ne mu amsa wa kanmu. Manzo Bulus ya sa shi haka: “Bari kowane mutum shi auna nasa aiki, sa’annan za ya sami fahariyarsa bisa ga zancen kansa kaɗai, ba ga zancen wani ba.”—Galatiyawa 6:4.

14. Menene Jehovah ke tsammani daga wajenmu a hidimarmu gare shi?

14 Jehovah Allah ya san yanayinmu sarai. Ya san inda muka kasa. Yana daraja hadaya, babba ko ƙarami da bayinsa suke bayarwa da yardan rai. Ba ya tsammanin dukanmu mu kasance da iyawa daidai da wasu ba. Sa’ad da yake tattauna bayar da kyauta, manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci na Koranti: “Idan nufi yana nan, abin karɓa ne gwargwadon abin da ke wurin mutum, ba gwargwadon abin da ba shi da shi” ba. (2 Korinthiyawa 8:12) Ƙa’idar da ke ciki ya shafi hidimarmu ga Allah. Me ya sa hidimarmu ga Jehovah ba yawan abin da muke yi ba ne amma yadda muke yinsa ne—da farin ciki da kuma zuciya ɗaya.—Zabura 100:1-5; Kolossiyawa 3:23.

Ka Koya Kuma Ka Riƙe Ruhu na Majagaba

15, 16. (a) Ina mahaɗin hidimar majagaba da godiya? (b) Ta yaya waɗanda ba su iya aikin majagaba ba za su nuna ruhu na majagaba?

15 Hanya ta albarka da za mu nuna godiyarmu ga Jehovah ita ce ta shigan hidima ta cikakken lokaci. Domin ƙaunar Jehovah ta motsa su da kuma godiya ga alherinsa, bayin da suke keɓe kansu da yawa sun yi gyara a rayuwansu don su iya samun ƙarin lokaci don su bauta wa Jehovah. Wasu suna hidimar majagaba na kullum, suna ɓad da averijin sa’o’i 70 kowacce wata suna wa’azin bishara da kuma koya wa mutane gaskiya. Wasu, da ƙila yanayinsu ya naƙasa su, a wasu lokatai sukan shirya su ɓad da sa’o’i 50 a wata suna wa’azi su majagaba na ɗan lokaci.

16 Amma bayin Jehovah da yawa da ba su iya yin hidima ta majagaba na kullum ko na ɗan lokaci ba fa? Za su iya nuna godiya ta wurin koya kuma riƙe ruhu na majagaba. Ta yaya? Ta wurin ƙarfafa waɗanda suke majagaba, ta koyar da yaransu su so aikin hidima na cikakken lokaci, kuma ta sa hannu sosai a wa’azi dangane da yanayinsu. Abin da muka yi cikin hidimarmu ya dangana ga godiyar zuciyarmu ga abin da Jehovah ya yi mana, yake yi mana, da kuma waɗanda zai yi.

Nuna Godiya da ‘Wadatarmu’

17, 18. (a) Ta yaya za mu nuna godiya da ‘wadatarmu’? (b) Yaya Yesu ya ɗauki kyautar da gwauruwar ta bayar, kuma me ya sa?

17 “Ka girmama Ubangiji da wadatanka,” in ji Misalai 3:9, “da nunan fari na dukan gallarka.” Bayin Jehovah ba sa bukatar su ba da zakka. Maimako, Bulus ya rubuta wa ikilisiyar Koranti: “Kowane mutum shi aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Korinthiyawa 9:7) Ba da kyauta da yardan rai don toƙara wa aikin wa’azi na Mulki ma na nuna godiyarmu. Godiya ta zuci tana taimakon mu mu yi haka a kai a kai, ƙila ta wurin yin ajiyar wani abu mako mako, yadda Kiristoci na farko suka yi.—1 Korinthiyawa 16:1, 2.

18 Ba yawan abin da muka bayar ne ke nuna yawan godiyarmu ga Jehovah ba. Maimako, ruhun da ya motsa mu mu bayar ne. Abin da Yesu ya lura da shi ke nan sa’ad da yake kallon mutane suna ba da kyautarsu cikin akwatin ma’aji a haikali. Sa’ad da Yesu ya ga wata gwauruwa da ta saka “anini biyu,” ya ce: “Gaskiya ni ke faɗa muku, abin da wannan gwauruwa matalauciya ta zuba ciki ya fi nasu duka: gama waɗannan duka daga cikin falalarsu suka zuba zuwa cikin sadakoki: amma ita daga tsiyatta ta zuba dukan iyakar abin zaman gari da ta ke da shi.”—Luka 21:1-4.

19. Me ya sa yake da kyau a sake bincika hanyoyi da muke nuna godiya?

19 Bari wannan nazari game da yadda za mu nuna godiyarmu ya motsa mu mu sake bincika hanyoyi da muke nuna godiya. Za mu iya ƙara hadayarmu ta yabo ga Jehovah, da kuma yadda muke toƙara wa aiki na dukan duniya da abin da muke da shi? Iyakar yadda muke haka, za mu tabbata cewa Ubanmu mai ƙauna, mai karimci, Jehovah, zai yi farin ciki cewa muna nuna godiya.

Ka Tuna?

• Domin waɗanne dalilai ya kamata mu yi godiya ga Jehovah?

• Waɗanne darussa muka koya a ba da zakka, ba da kyauta, da kuma yin kala?

• Ta yaya za mu koyi ruhu na majagaba?

• Ta yaya za mu yi amfani da ‘wadatarmu’ mu gode wa Jehovah?

[Hotuna a shafi na 27]

“Kowacce kyakkyawar baiwa da kowacce cikakkiyar kyauta”

[Hotuna a shafi na 28]

Waɗanne darussa uku ne daga Dokar aka nuna a nan?

[Hotuna a shafi na 30]

Waɗanne irin hadayu za mu iya yi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba