Ka Bayar Ka Hana Kanka
“KANA iya kirana maroƙi; wannan bai dame ni ba. Ni maroƙi ne domin Yesu.” Waɗannan kalmomin minista na ’yan farotasta ya bayyana ruɗani da yake tattare da yadda addini yake samun kuɗi. Kafaffen addini kamar dai yana iya ci gaba ne idan yana iya samun kuɗi mai yawa. Ana bukatar a biya ma’aikata, ana bukatar a gina haikali kuma a ci gaba da adana su, ana bukatar a tallafa wa aikin wa’azi da kuɗi. Ta yaya za a samu kuɗi da ake bukatarsa?
Ga coci da yawa, amsar ita ce ushiri.a “Da ushiri Allah yake samun kuɗi domin mulkinsa a duniya,” in ji mai wa’azi Norman Robertson. “Hanyar samun kuɗinsa ke nan da ya sa wa’azin Lingila ta tabbata.” Ba ya jinkirin tunasar da mabiyansa su cika hakkinsu na bayarwa, da kuzari ya ce: ‘Ushiri ba abin da za ka bayar ba ne domin za ka iya bayarwa. Hanyar nuna biyayya ce. Idan ba ka ba da ushiri ba ka taka dokar Allah. Zamba ce.’—Tithing—God’s Financial Plan.
Wataƙila ka yarda cewa bayarwa ya kamata ya zama ɓangaren bauta ta Kiristoci. Duk da haka, nacewa wajen roƙon kuɗi yana damunka, ko ƙila ma yana ɓata maka rai? Wani masanin addini na Brazil Inácio Strieder ya tuhumi coci da yin amfani da ushiri domin su “magance matsalolinsu na addini” kuma ya kira irin ayyukan nan “haramu, cuta da kuma bauɗewa ta addini.” Ya lura cewa sakamakon wannan, “mutanen da ba su da aiki, gwauraye mata, matalauta da kuma waɗanda ba sa hujja sun kammala da cewa Allah ya yi watsi da su kuma ya tilasta su su yi wa ‘mai wa’azi’ kyauta mai yawa kuma nasu iyalan su kwana da yunwa.”
Kana iya mamaki: ‘Shin coci da suke tilasta ba da ushiri suna amfani da Nassosi daidai kuwa? Ko kuma dai wasu addinai suna amfani ne da tsoron horo daga Allah, wajen mu kashe mu raba? Da gaske Allah yana so ne mu bayar har mu hana kanmu?’
[Hasiya]
a An ce ma’anar ushiri ita ce ba da kashi ɗaya cikin goma na dukan abin da aka samu.