Kiristoci Suna Bukatar Juna
‘Mu gaɓoɓi ne na junanmu.’—AFISAWA 4:25.
1. Menene wani kundin sani ya ce game da jikin mutum?
JIKIN mutum abin al’ajabi ne na halitta! Littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce: “Mutane wani lokaci suna kiran jikin mutum mashin—mafi ban al’ajabi da aka gina. Hakika, jikin mutum ba mashin ba ne. Amma za a gwada shi da mashin a hanyoyi da yawa. Kamar mashin, jiki yana da gaɓoɓi da yawa. Kowacce gaɓa ta jiki, kamar kowacce gaɓa ta mashin, tana aiki na musamman. Amma dukan gaɓoɓin suna aiki tare, ta haka suna sa jiki ko mashin ya yi aiki da kyau.”
2. A wace hanya ce jikin mutum da ikilisiyar Kirista suke da kamani?
2 Hakika, jikin mutum yana da gaɓoɓi da yawa, kuma kowanne yana ba da abin da ake bukata. Babu jijiya, tsoka, ko wani gaɓa na jikin da ba shi da amfani. Hakanan ma, kowanne cikin ikilisiyar Kirista zai daɗa wani abu ga lafiya da kyanta ta ruhaniya. (1 Korinthiyawa 12:14-26) Ko da yake babu wanda ya kamata ya ji ya fi wasu a cikin ikilisiya, ba kuwa wanda ya kamata ya ɗauki kansa ba shi da muhimmanci ba.—Romawa 12:3.
3. Ta yaya Afisawa 4:25 ta nuna cewa Kiristoci suna bukatar juna?
3 Kamar yadda gaɓoɓin mutum suka dogara ga juna, Kiristoci na bukatar juna. Manzo Bulus ya gaya wa shafaffu ’yan’uwa masu bi: ‘Ku faɗi gaskiya kowane game da ɗan’uwansa, kuna kawarda ƙarya: gama mu gaɓoɓi ne na junanmu.’ (Afisawa 4:25) Tun da ‘gaɓoɓi ne na juna,’ da akwai hulɗa ta gaske da cikakken haɗin kai tsakanin waɗanda suke cikin Isra’ila ta ruhaniya—“jikin Kristi.” Hakika, kowannensu gaɓa ne na wasu. (Afisawa 4:11-13) Waɗanda suke haɗin kai da su cikin farin ciki, Kiristoci ne da suke da begen zama a duniya.
4. A waɗanne hanyoyi ne za a iya taimakon sababbi?
4 Kowacce shekara, mutane dubbai da suke begen zama a aljanna a duniya suna baftisma. Sauran mutanen ikilisiya suna taimaka musu su “nace bi zuwa kammala” da farin ciki. (Ibraniyawa 6:1-3) Wannan taimako zai iya haɗawa da amsa tambayoyi na Nassi ko kuma ba da taimako wajen hidima. Za mu iya taimakon sababbi ta wajen kafa misali mai kyau a yin furci koyaushe a taron Kirista. A lokacin wahala, za mu iya ƙarfafa su kuma ƙila mu yi musu ta’aziyya. (1 Tassalunikawa 5:14, 15) Ya kamata mu nemi hanyoyi da za mu taimake wasu ‘su ci gaba da tafiya cikin gaskiya.’ (3 Yohanna 4) Ko mu tsofaffi ne ko matasa, yanzu muka soma tafiya cikin gaskiya ko kuma mun yi haka na wasu shekaru, za mu iya ƙarfafa ruhaniya na ’yan’uwa masu bi—suna bukatarmu.
Sun Ba da Taimako da Ake Bukata
5. Ta yaya Akila da Biriska suka taimaki Bulus?
5 Ma’aurata Kiristoci suna cikin waɗanda suke samun gamsuwa wajen taimaka wa ’yan’uwa masu bi. Alal misali, Akila da matarsa, Biriska, sun taimaki Bulus. Sun marabce shi a gidansu, sun yi aikin tanti tare da shi, kuma sun taimake shi ƙarfafa sabuwar ikilisiya a Koranti. (Ayukan Manzanni 18:1-4) A hanyar da ba a faɗa ba, sun ɗauki kasada domin Bulus. Suna da zama a Roma sa’ad da Bulus ya gaya wa Kiristoci a wurin: “Ku gaida Biriska da Akila abokan aikina cikin Kristi Yesu, waɗanda suka miƙa wuyansu sabili da raina; su dai ba ni kaɗai ni ke gode musu ba, amma har da dukan ikilisiyoyi na Al’ummai.” (Romawa 16:3, 4) Kamar Akila da Biriska, wasu Kiristoci na zamani suna ƙarfafa ikilisiyoyi suna taimakon ’yan’uwa masu bi a hanyoyi dabam dabam, wani lokaci ma su ɗauki kasada wajen guje wa fallasa bayin Allah don kada a zalunce su ko kuma ’yan adawa su kashe su.
6. Wane taimako Apollos ya samu?
6 Akila da Biriska sun kuma taimaki Kirista Afolos da ya ƙware wajen magana, wanda yake koyar da mazauna Afisus game da Yesu Kristi. A lokacin, iyakan sanin Afolos game da baftisma da Yohanna ya yi ne alamar tuba daga zunubi ga Dokar alkawari. Da suka fahimci cewa Afolos yana bukatar taimako, Akila da Biriska “suka ƙara buɗe masa tafarkin Allah sosai.” Wataƙila sun yi masa bayani cewa baftisma ta Kirista ta ƙunshi nitsarwa cikin ruwa da kuma zubo da ruhu mai tsarki. Afolos ya yi amfani da abin da ya koya. Bayan haka a Akaya “ya yi taimako dayawa ga waɗanda suka bada gaskiya ta wurin alheri, gama da ƙarfi ya kayarda Yahudawa, a sarari kuwa, yana bayyanawa daga cikin littattafai Yesu Kristi ne.” (Ayukan Manzanni 18:24-28) Kalami da ’yan’uwa masu bi suka yi sau da yawa zai taimaka mana mu kyautata fahimtar Kalmar Allah da muka yi. Muna bukatar juna a wannan ma.
Ba da Gudummawa
7. Ta yaya Filibbiyawa suka amsa kira sa’ad da Kiristoci masu bi suka bukaci taimako?
7 Waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista a Filibbi suna ƙaunar Bulus sosai da suka aika masa kayayyaki sa’ad da yake zama a Tassalunika. (Filibbiyawa 4:15, 16) Sa’ad da ’yan’uwa a Urushalima suke bukatar taimako, Filibbiyawa sun nuna suna shirye su ba da gudummawa sosai. Bulus ya yi godiya sosai ga hali mai kyau na ’yan’uwa a Filibbi da ya ambace su misali ga wasu masu bi.—2 Korinthiyawa 8:1-6.
8. Wane ruhu ne Abafroditus ya nuna?
8 Sa’ad da aka jefa Bulus a kurkuku, Filibbiyawa sun aika masa kyauta har da wakilinsu Abafroditus. “Sabili da aikin Kristi [Abafroditus] ya kai kusa da mutuwa, yana kasaida ransa,” in ji Bulus, “domin shi cika abin da ya tauye wajen hidimarku gareni.” (Filibbiyawa 2:25-30; 4:18) Ba a gaya mana ba ko Abafroditus dattijo ne ko bawa mai hidima. Duk da haka, Kirista ne mai saɗaukar da kai mai ba da taimako, Bulus ya yi bukatarsa sosai. Akwai wani kamar Abafroditus a ikilisiyarku?
Sun ‘Sanyaya Zuciya’
9. Wane misali Aristarkus ya nuna?
9 Ana daraja ’yan’uwa da suke da ƙauna, kamarsu Akila, Biriska, da Abafroditus sosai a kowacce ikilisiya. Wasu cikin ’yan’uwanmu masu bi za su iya zama kamar Aristarkus Kirista na ƙarni na farko. Shi da wasu sun ‘sanyaya zuciya,’ wataƙila ta yin ta’aziyya ko taimako game da abubuwa na zahiri. (Kolossiyawa 4:10, 11) Ta taimakon Bulus, Aristarkus ya kasance aboki na gaske a lokacin wahala. Ya kasance irin mutumin da aka ambata a Misalai 17:17: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” Bai kamata dukanmu mu yi ƙoƙari mu zama masu ‘sanyaya zuciya’ ga ’yan’uwa Kiristoci ba? Ya kamata musamman ma mu taimaki waɗanda suke shan wahala.
10. Wane misali Bitrus ya kafa wa dattawa Kirista?
10 Dattawa Kirista musamman dole su sanyaya zuciyar ’yan’uwansu na ruhaniya. Kristi ya gaya wa manzo Bitrus: “Ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” (Luka 22:32) Bitrus ya yi hakan domin ya nuna ƙaƙƙarfan hali, musamman bayan tashin Yesu daga matattu. Dattawa, ku yi iyakacin ƙoƙarinku ku yi hakan da yardan rai kuma da hankali, domin ’yan’uwanku masu bi suna bukatarku.—Ayukan Manzanni 20:28-30; 1 Bitrus 5:2, 3.
11. Ta yaya za mu amfana daga bincika halin Timothawus?
11 Abokin tafiyar Bulus Timothawus dattijo ne da ya damu ƙwarai game da wasu Kiristoci. Ko da yana ciwo, Timothawus ya nuna bangaskiya marar jijjiga ‘ya yi bauta da Bulus zuwa yaɗuwar bishara.’ Saboda haka, manzon ya gaya wa Filibbiyawa: “Ba ni da kowa wanda hankalinsa ya yi daidai da nasa ba, wanda za ya yi tattalin zamanku da gaskiya.” (Filibbiyawa 2:20, 22; 1 Timothawus 5:23; 2 Timothawus 1:5) Za mu kasance da amfani ga ’yan’uwa masu bauta wa Jehovah ta nuna hali irin na Timothawus. Hakika, dole mu jimre da kasawarmu da gwaji dabam dabam, amma za mu iya kuma ya kamata mu nuna bangaskiya mai ƙarfi da damuwa da ’yan’uwanmu na ruhaniya. Ya kamata koyaushe muna tuna cewa suna bukatarmu.
Mata da Suka Damu da Wasu
12. Menene za mu koya daga misalin Dokas?
12 Dokas tana cikin mata masu ibada da suka damu da wasu. Sa’ad da ta mutu, almajirai suka kira Bitrus suka kai shi wani bene. A wajen “dukan gwauraye suka tsaya wurinsa suna kuka, suna nuna riguna da tufafi waɗanda Tabitha ta yi, tun tana tare da su.” An mai da Dokas zuwa rai kuma babu shakka ta ci gaba da ‘ayyukan nagarta da kyauta na alheri.’ A cikin ikilisiyar Kirista na zamani akwai mata kamar Dokas da ƙila suke ɗinki ko su yi wasu abubuwa masu kyau ga waɗanda suke da bukata. Hakika, ayyukansu na nagarta zai zama ɗaukaka abubuwa na Mulki da sa hannu cikin aikin almajirantarwa.—Ayukan Manzanni 9:36-42; Matta 6:33; 28:19, 20.
13. Ta yaya Lidiya ta nuna ta damu da ’yan’uwa Kiristoci?
13 Mace mai tsoron Allah da sunanta Lidiya ta damu da wasu. ’Yar Tiyatira ce, tana da zama a Fillibi sa’ad da Bulus ya yi wa’azi a wajen, misalin shekara ta 50 A.Z. Wataƙila Lidiya Bayahudiya shigaggiya ce, amma ƙila Yahudawa kalilan ne kuma babu majalisa a Fillibi. Ita da wasu mata masu ibada sun taru don bauta a kusa da kogi sa’ad da manzon ya yi musu bishara. Labarin ya ce: “Ubangiji kuwa ya buɗe zuciyar [Lidiya], da za ta lura da abin da Bulus yana faɗi. Sa’anda aka yi mata baftisma, duk da iyalinta, ta roƙe mu, ta ce, idan kun aza ni amintacciya ce ga Ubangiji, ku zo gidana, ku zauna. Har ta i mamu.” (Ayukan Manzanni 16:12-15) Domin Lidiya tana son ta yi abubuwa masu kyau wa wasu, ta ci nasara a rinjayar Bulus da wasu su zauna tare da ita. Muna farin ciki sa’ad da Kiristoci masu ƙauna da alheri yau suka yi mana maraba!—Romawa 12:13; 1 Bitrus 4:9.
Matasa Muna Bukatarku
14. Ta yaya Yesu Kristi ya bi da matasa?
14 Ɗan Allah, Yesu Kristi mai ƙauna da alheri ne ya soma ikilisiyar Kirista. Mutane sun sake a wurinsa domin yana ƙauna da juyayi. Sa’ad da wasu suka kawo yaransu wajen Yesu a wani lokaci, almajiransa sun yi ƙoƙari su kore iyayen da yaransu. Amma Yesu ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su: gama na irin waɗannan mulkin Allah ya ke. Hakika ina ce muku, dukan wanda ba ya karɓi mulkin Allah kamar yaro ƙanƙani ba, ba za ya shiga cikinsa ba daɗai.” (Markus 10:13-15) Don mu samu albarkar Mulki, dole mu kasance da tawali’u, waɗanda ake iya koya musu yadda ake wa yara ƙanana. Yesu ya nuna yana ƙaunar yara ƙanana ta rungumar su kuma ya yi musu albarka. (Markus 10:16) Matasa a yau kuma fa? Ku tabbata cewa ana ƙaunarku kuma ana bukatarku a cikin ikilisiya.
15. Waɗanne abubuwa game da rayuwar Yesu suke rubuce a Luka 2:40-52, wane misali ya kafa wa matasa?
15 Sa’ad da Yesu yake yaro, ya nuna yana ƙaunar Allah da kuma Nassosi. Sa’ad da yake ɗan shekara 12, shi da iyayensa, Yusufu da Maryamu suka yi tafiya daga garinsu Nazarat zuwa Urushalima su yi Idin Ƙetarewa. Sa’ad da suke komawa gida, iyayen Yesu suka gane cewa Yesu ba ya cikin rukunin da suke tafiya tare. Daga baya suka iske shi yana zaune a majami’ar haikalin, yana sauraran malaman Yahudawa yana yi musu tambayoyi. Da ya yi mamaki cewa Yusufu da Maryamu ba su san inda za su same shi ba, Yesu ya yi tambaya: “Ba ku sani ba wajib ne a gareni ina cikin sha’anin Ubana?” Ya koma gida da iyayensa, ya yi musu biyayya, ya ci gaba cikin hikima da girma. (Luka 2:40-52) Yesu ya kafa wa matasarmu misali mai kyau! Babu shakka ya kamata su yi wa iyayensu biyayya suna son su yi koyo game da abubuwa na ruhaniya.—Kubawar Shari’a 5:16; Afisawa 6:1-3.
16. (a) Menene wasu yara suka yi sowarsa sa’ad da Yesu yake wa’azi a haikali? (b) Wane zarafi matasa Kiristoci suke da shi yau?
16 Kai matashi, ƙila kana wa’azi game da Jehovah a makaranta da kuma gida gida da iyayenka. (Ishaya 43:10-12; Ayukan Manzanni 20:20, 21) Sa’ad da Yesu yake wa’azi kuma yake warkar da mutane a haikali ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa, wasu yara suka yi sowa: “Hosanna ga ɗan Dauda!” Da manyan malamai da marubuta suka yi fushi domin wannan suka ce: “Kana jin abin da waɗannan su ke faɗi?” Yesu ya ce: “I: ba ku taɓa karantawa ba, Daga cikin bakin jarirai da masu-shan mama ka cika yabo?” (Matta 21:15-17) Kamar waɗannan yara, matasa cikin ikilisiya kuna da zarafin yabon Allah da Ɗansa. Muna sonku muna bukatarku ku yi aiki na masu shelar Mulki tare da mu.
Sa’ad da Wahala ta Faɗo
17, 18. (a) Me ya sa Bulus ya shirya tattara kayan agaji wa Kiristoci a Yahudiya? (b) Yaya tara kuɗi da aka yi wa Yahudawa masu bi ya shafi Kiristoci Yahudawa da na Al’umma?
17 Ko yaya yanayinmu, ƙauna tana motsa mu mu taimaki ’yan’uwa Kiristoci da suke da bukata. (Yohanna 13:34, 35; Yaƙub 2:14-17) Ƙauna ce don ’yan’uwansa a Yahudiya ta motsa Bulus ya shirya a tara musu abubuwa a ikilisiyoyin da ke Akaya, Galatiya, Makidoniya, da Asiya. Tsanani, hargitsi, da yunwa da almajirai a Urushalima suka fuskanta sun kawo abin da Bulus ya kira “wahala,” “ƙunce-ƙunce,” da “wason dukiyar[su].” (Ibraniyawa 10:32-34; Ayukan Manzanni 11:27–12:1) Saboda haka, ya kula da tara abubuwa da aka yi wa Kiristoci matalauta a Yahudiya.—1 Korinthiyawa 16:1-3; 2 Korinthiyawa 8:1-4, 13-15; 9:1, 2, 7.
18 Kyauta da aka bayar da yardan rai don tsarkakku a Yahudiya ya nuna cewa da gamin ’yan’uwantaka tsakanin Yahudawa masu bauta wa Jehovah da na Al’umma. Ba da kyautar kuɗi ta taimaki Kiristoci na Al’umma su nuna wa ’yan’uwansu Yahudawa masu bi godiya don wayewa na ruhaniya da suka samu daga wajensu. Shi ya sa aka yi kyauta da na kayayyaki ne da na ruhaniya. (Romawa 15:26, 27) Ba da kyauta ga ’yan’uwa mabukata a yau da yardan rai ne kuma ƙauna ce ke motsa ta. (Markus 12:28-31) Muna bukatar juna a wannan ma don mu yi daidai da ‘wanda ya tara kaɗan, kada kuwa ya gaza masa.’—2 Korinthiyawa 8:15.
19, 20. Ka ba da misali da ya nuna yadda mutanen Jehovah suka ba da taimako sa’ad da bala’i ta auku.
19 Sanin cewa Kiristoci na bukatar juna, muna saurin taimakon ’yan’uwanmu cikin bangaskiya. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da girgizar ƙasa da rushewar manyan duwatsu da ƙasa suka auku a El Salvador a farkon shekara ta 2001. Wani rahoto da aka bayar ya ce: “ ’Yan’uwa a dukan ɓangarorin El Salvador suka shirya kayan agaji. ’Yan’uwa daga Guatemala, Amirka, da Canada suka zo su taimake mu. . . . Da sauri aka gina gidaje 500 da Majami’un Mulki 3 masu kyau. Aiki tuƙuru da haɗin kan waɗannan ’yan’uwa da suka saɗaukar da kansu wa’azi ne sosai.”
20 Rahoto daga Afirka ta Kudu ya ce: “Ambaliya mai tsanani da ya ragargaza ɓangare mai girma na Mozambique ya shafi ’yan’uwanmu Kiristoci da yawa. Reshen Mozambique ya shirya ya kula da yawancin bukatunsu. Amma ’yan’uwa da suke reshen sun ce mu aika wa ’yan’uwa mabukata tufafi masu kyau da ba ma amfani da su. Mun tara isashen tufafi, muka aika da kwandon aika kaya 40 [da ke daidai da faɗin ɗakuna uku] cike da tufafi wa ’yan’uwanmu a Mozambique.” Hakika, a waɗannan hanyoyi ma, muna bukatar juna.
21. Me za a bincika a talifi na gaba?
21 Yadda aka ambata da farko, dukan gaɓoɓin jikin mutum suna da muhimmanci. Hakan yake da gaske a ikilisiyar Kirista. Dukan waɗanda suke cikinta na bukatar juna. Ya kamata su ci gaba da bauta cikin haɗin kai. Talifi na gaba zai bincika wasu abubuwa da zai sa wannan ya yiwu.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane kamani ke tsakanin jikin mutum da ikilisiyar Kirista?
• Yaya Kiristoci na farko suke amsa kira sa’ad da ’yan’uwa masu bi suka bukaci taimako?
• Waɗanne misalai ne na Nassi suka nuna cewa Kiristoci suna bukatar juna kuma suna taimakon juna?
[Hoto a shafi na 10]
Akila da Biriska sun damu da wasu
[Hotuna a shafi na 12]
Mutanen Jehovah suna taimakon juna da kuma wasu sa’ad da wahala ta fāɗa musu