Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ya kamata ne mu fahimci Ru’ya ta Yohanna 20:8 cewa adadin mutane da Shaiɗan zai ruɗe su a gwaji na ƙarshe ba su da iyaka?
Ru’ya ta Yohanna 20:8 ta kwatanta hari na ƙarshe da Shaiɗan zai kai wa mutanen Allah da suke raye a duniya a ƙarshen sarautar shekara dubu na Mulkin Almasihu. Da take magana game da Shaiɗan, ayar ta ce: “Za ya fito kuma garin ya ruɗe al’umman da ke cikin ƙusurwoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, shi tattara su zuwa yaƙin; yawansu fa yana kama da yashi na teku.”
Duk da ci gaba a hanyar ƙirge na kimiyya, ba wanda ya san yawan “yashi na teku.” Saboda haka, za a iya cewa wannan furcin yana nufin adadi da ba a san iyakansa ba. Amma yana nufi ne adadi da ba shi da iyaka, ko kuma dai kawai yana nufin adadi ne da yake da yawa amma ba a san iyakansa ba?
A cikin Littafi Mai Tsarki, furcin nan “kamar yashi na teku” an yi amfani da shi a hanyoyi da yawa. Alal misali, a Farawa 41:49, ya ce: “Yusufu ya ajiye hatsi kamar yashi na teku, da yawa ƙwarai, har ya bar lissafinsa; gama ya fi gaban lissafi.” A nan nanaci yana bisa yawansa ne da ya fi gaban lissafi. Hakazalika, Jehovah ya ce: “Kamar yadda rundunar sama ba ta ƙidayuwa, yashi a teku ba shi aunuwa: hakanan zan riɓanɓanya zuriyar Dauda bawana.” Yadda ba a iya ƙirga taurari na sama da yashi a teku, haka Jehovah zai cika alkawarinsa ga Dauda.—Irmiya 33:22.
Sau da yawa furcin nan “yashi na teku” yana nufin abu mai yawa ko kuma mai girma. Isra’ilawa a Gilgal sun damu ƙwarai domin yawan sojojin Filistiyawa a Michmash, waɗanda suke da yawa “kamar yashi wanda ke bakin teku don yawa.” (1 Samu’ila 13:5, 6; Alƙalawa 7:12) Kuma “Allah ya ba Sulemanu hikima da ganewa ƙwarai da gaske, da buɗaɗɗiyar zuciyar, kamar yashin da ke a bakin teku.” (1 Sarakuna 4:29) Ko da yake abin da aka faɗa gaskiya ne a dukan wannan batutuwa, amma suna da iyaka.
“Yashi na teku” zai iya nufin adadin da ba a san iyakansa ba, ba tare da nufin yana da yawa ƙwarai ba. Jehovah ya gaya wa Ibrahim: “Zan riɓanɓanya tsatsonka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku.” (Farawa 22:17) Sa’ad da yake maimaita wannan alkawarin ga jikan Ibrahim Yakubu, Jehovah ya yi amfani da furcin nan “turɓaya ta ƙasa” kuma Yakubu ya maimaita shi “yashi na teku.” (Farawa 28:14; 32:12) Kamar yadda abubuwa suka juya, “zuriyar” Ibrahim, ban da Yesu Kristi, sun kasance 144,000, wanda Yesu ya kira “ƙaramin garke.”—Luka 12:32; Galatiyawa 3:16, 29; Ru’ya ta Yohanna 7:4; 14:1, 3.
Menene muka koya daga waɗannan misalan? Furcin nan “kamar yashi na teku” ba ko yaushe ba ne yake nufin adadin da ba shi da iyaka; kuma ba ko yaushe ba ne ake amfani da shi a kwatanta abin da yake da yawa ƙwarai ko kuma mai girma sosai. Sau da yawa yana nufin adadi mai iyaka amma wanda ba a san yawansa ba. Saboda haka, daidai ne a gaskata cewa taron ’yan tawaye da za su tallafa wa Shaiɗan a harinsa na ƙarshe a kan mutanen Allah zai kasance, ba marar iyaka ba, amma adadi mai yawa da zai iya yin barazana. Amma adadin, har yanzu ba a san iyakacinsa ba.