Ka Kasance Da Bangaskiya Irin Ta Ibrahim!
“Waɗanda ke daga wajen bangaskiya, su ne ’ya’yan Ibrahim.”—GALATIYAWA 3:7.
1. Ta yaya Abram ya bi da sabon gwaji a Kan’ana?
ABRAM ya bar rayuwar morewa a Ur a yin biyayya da umurnin Jehovah. Matsalolin da ya fuskanta a shekarun da suka biyo baya somi ne kawai a zancen gwajin bangaskiya da ya fuskanta a Masar. Labarin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai yunwa ta faru a ƙasan.” Da zai zama da sauƙi Abram ya yi baƙin cikin yanayinsa! Maimako, ya ɗauki mataki don ya yi wa iyalinsa tanadi. “Abram kuwa ya gangara zuwa Masar domin ya yi zaman baƙonci a can; gama yunwa ta tsananta ƙwarai cikin ƙasan.” Yadda iyalin Abram ke da girma da kyar a kasa ganinsu a Masar. Jehovah zai yi aminci ga alkawuransa ya kāre Abram daga lahani kuwa?—Farawa 12:10; Fitowa 16:2, 3.
2, 3. (a) Me ya sa Abram ya ɓoye cewa Saraya matarsa ce? (b) Domin yanayin, yaya Abram ya bi da matarsa?
2 Mu Karanta a Farawa 12:11-13: “Ya zama kuma, sa’anda ya kusa shiga cikin Masar, ya ce ma Saraya matatasa, Ki duba dai, na sani ke mace mai-kyan gani ce: za ya zama fa, lokacinda Masarawa sun gan ki, za su ce, Matatasa ce waccan nan: za su kashe ni kuma, amma su a bar ki da rai. Ina roƙonki, ki ce ’yar’uwata ce ke: domin in zauna lafiya sabili da ke, raina kuma shi rayu sabili da ke.” Ko da yake Saraya tana sama da shekara 65, kyakkyawa ce ƙwarai. Wannan ya sa ran Abram cikin haɗari.a (Farawa 12:4, 5; 17:17) Mafi muhimmanci ma, ya shafi nufin Jehovah, domin ya ce ta wurin tsatson Abram dukan al’umman duniya za su sami albarka. (Farawa 12:2, 3, 7) Tun da yake har ila Abram ba shi da ɗa, yana da muhimmanci ya kasance da rai.
3 Abram ya gaya wa matarsa su yi amfani da wata dabara da suka shirya da farko, watau, ta ce ita ’yar’uwarsa ce. Ka lura cewa ko da yana da ikon shugabanci, bai nuna ikon ba, amma ya nemi haɗin kanta da kuma goyon bayanta. (Farawa 12:11-13; 20:13) Ta haka, Abram ya bar misali mai kyau ga maza su nuna shugabanci mai kyau, kuma Saraya, ta wurin miƙa kanta, misali ce ga mata a yau.—Afisawa 5:23-28; Kolossiyawa 4:6.
4. Yaya ya kamata bayin Allah masu aminci a yau su bi da kansu yayin da zance ya shafi rayukan ’yan’uwansu?
4 Saraya ta faɗi cewa ita ’yar’uwar Abram ce domin da gaske ita ’yar ubansa ce. (Farawa 20:12) Bugu da ƙari, ba dole ba ne ya gaya wa mutane abin da ba su dace a gaya musu ba. (Matta 7:6) Bayin Allah masu aminci a lokatan zamani sun bi umurnin Littafi Mai Tsarki na kasancewa da gaskiya. (Ibraniyawa 13:18) Alal misali, ba za su taɓa yin ƙarya ba har da rantsuwa a wani kotu. Idan ya shafi rayukan ’yan’uwansu a zahiri ko a ruhaniya, a lokatai na tsanantawa ko na hargitsi, suna bin gargaɗin Yesu su zama “masu-azanci fa kamar macizai, marasa-ɓarna kamar kurciyoyi.”—Matta 10:16; Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 1996, shafi na 30, izifil na 19.
5. Me ya sa Saraya ta kasance a shirye ta yi biyayya ga roƙon Abram?
5 Yaya Saraya ta yi na’am da roƙon Abram? Manzo Bitrus ya kwatanta mata kamar ta, da cewa “suna kafa bege ga Allah.” Saboda haka, Saraya ta fahimci mahawwara ta ruhaniya da ta ƙunsa. Ballantana ma, tana ƙaunar mijinta kuma tana daraja shi. Domin haka, Saraya ta zaɓa ta ‘miƙa kanta ga mijinta’ kuma ta ƙi faɗar cewa ita matar aure ce. (1 Bitrus 3:5) Babu shakka yin haka zai sa ta cikin haɗari. “Sa’anda Abram ya je cikin Masar, Masarawa suka ga mata kyakkyawa ce ƙwarai. Sarakunan Fir’auna kuma suka gan ta, suka yi ta koɗa ta a gaban Fir’auna: har aka ɗauki matan aka kai ta gidan Fir’auna.”—Farawa 12:14, 15.
Ceton da Jehovah Ya Yi
6, 7. A cikin wane yanayi ne mai wahala Abram da Saraya suka iske kansu, kuma ta yaya Jehovah ya ceci Saraya?
6 Lalle zai zama da wahala ƙwarai ga Abram da Saraya! Ya bayyana kamar dai za a yi lalata da Saraya. Ban da haka ma, Fir’auna bai san Saraya matar aure ba ce, ya yi wa Abram kyauta mai yawa, har ya “sami tumaki, da shanu, da jakai, da ma’aikata maza da mata, da jakai mata, da raƙuma.”b (Farawa 12:16) Waɗannan kyauta lalle sun zama da ƙyama ƙwarai ga Abram! Ko da abubuwa kamar sun gama lalacewa, Jehovah bai yasar da Abram ba.
7 “Amma Ubangiji ya wahalda Fir’auna duk da gidansa da masihu masu-girma sabili da Saraya matar Abram.” (Farawa 12:17) A wata hanyar da ba a faɗe ta ba, an bayyana wa Fir’auna dalilin ‘masihun.’ Nan da nan: “Fir’auna kuma ya kirayi Abram, ya ce, Menene wannan da ka yi mini? don menene ba ka faɗa mini ita matarka ce? Donme ka ce, Ita ƙan’uwata ce? har da na ɗauke ta ta zama matata: yanzu fa, ga matarka, ka karɓe ta, ka yi tafiyarka. Fir’auna kuma ya yi ma waɗansu mazaje umurni a kansa: su kuwa suka yi masa rakiya, da matatasa, da abin da yake da shi duka.”—Farawa 12:18-20; Zabura 105:14, 15.
8. Wane irin kāriya Jehovah ya yi alkawarinta ga Kiristoci a yau?
8 A yau, Jehovah bai ce zai kāre mu daga mutuwa, aikata laifi, yunwa, ko kuma wani bala’i ba. Ya yi mana alkawarin cewa zai kāre mu daga abubuwan da za su lalata ruhaniyarmu. (Zabura 91:1-4) Yana yin haka musamman ta ba mu gargaɗi a kan kari ta wurin Kalmarsa da kuma “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45) Me kuma za a ce game da mutuwa domin tsanani? Ko da zai ƙyale mutane su mutu, Allah ba zai taɓa yarda a kawar da mutanensa gabaki ɗaya ba. (Zabura 116:15) Kuma idan mutuwa ta ci wasu masu aminci, muna da gaba gaɗi a tashinsu daga matattu.—Yohanna 5:28, 29.
Sadaukar da Kai don Samun Salama
9. Menene ya nuna cewa Abram ya ci gaba da tafiyarsa yayin da yake a Kan’ana?
9 Hakika da ƙarewar yunwa a Kan’ana, “Abram fa ya tashi daga Masar, shi, da matatasa, da abin da ya ke da shi duka, da Lot kuma tare da shi, suka nufi Kudu [wajejen kudu na duwatsun Yahuda da ba a yawan ruwan sama]. Abram kuwa yana da arziki dayawa na bisashe, da azurfa, da zinariya.” (Farawa 13:1, 2) Mazaunan za su ga mutum ne da yake da iko da rinjaya, babban hakimi. (Farawa 23:6) Abram ba shi da burin ya zauna wajen kuma ya shiga siyasar Kan’aniyawa. Maimako, “ya kama yin tafiyarsa kuma daga Kudu har zuwa ga Bethel, zuwa wurin [tanti] nasa ya ke da fāri, tsakanin Bethel da Ai.” Kullum dai, Abram yana sa bautar Jehovah farko a duk inda ya je.—Farawa 13:3, 4.
10. Wace matsala ce ta faru tsakanin makiyayan Abram da na Lot, kuma me ya sa ya kamata su warware ta da sauri?
10 “Lot kuma, wanda ya tafi tare da Abram, yana da garkunan tumaki da na shanu, da [su tanti]. Amma ƙasan nan ta kāsa musu, da za su zauna wuri ɗaya: gama abin mulkinsu dayawa ne, har da ba su iya zauna tare ba. Sai husuma kuma ta faru tsakanin makiyaya na bisashen Abram da makiyaya na bisashen Lot: a kwanakin nan Kan’aniyawa da Perizziyawa kuma su ke zaune a ƙasan.” (Farawa 13:5-7) Ƙasar ba ta da isashen ruwa da ciyayi da za su ciyar da garkunan Abram da na Lot. Domin haka husuma ta taso tsakanin makiyayan. Irin hasalar nan bai dace da masu bauta wa Allah na gaskiya ba. Idan irin fushin nan ya ci gaba, rata ta dindindin za ta shiga tsakaninsu. Saboda haka, yaya Abram zai warware wannan yanayin? Ya ɗauki Lot bayan mutuwar ubansa, wataƙila ya yi renonsa a kan ɗansa. Tun da yake shi ne babba cikinsu, ba daidai ne Abram ya zaɓa wa kansa wuri mafi kyau ba?
11, 12. Wace kyauta hannu sake Abram ya yi wa Lot, kuma me ya sa zaɓen Lot ba na hikima ba ce?
11 Amma, “sai Abram ya ce ma Lot, Ina roƙonka, kada husuma ta kasance tsakanina da kai, tsakanin makiyayana da makiyayanka kuma; gama mu ’yan’uwa ne. Dukan ƙasan nan ba shimfiɗe ta ke a gareka ba? ka ware dabam da ni, ina roƙonka: in ta hannun hagu ka ke ɗauka, ni in tafi zuwa na dama: in kuwa za ka wajen na dama, ni in nufa wajen na hagu.” Kusa da Bethel da akwai abin da ake kira “babbar hasumiya ta Palasɗinu.” Wataƙila daga wurin “Lot ya tada idanunsa, ya dubi dukan Filin Urdun, ga shi wuri mai-dausayi ne ko’ina tun Ubangiji ba ya halaka Sodom da Gomorrah ba tukuna, kamar gonar Ubangiji ce, kamar ƙasar Masar, sa’anda za ka wajen Zoar.”—Farawa 13:8-10.
12 Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Lot, “mai adalci,” domin wasu dalilai bai ɓata lokaci ba wajen Abram a wannan batun, kuma babu alamar cewa ya biɗi shawarar tsohon mutumin. (2 Bitrus 2:7) “Lot fa ya zaɓa ma kansa dukan Filin Urdun; Lot kuma ya kama tafiya gabashi: suka rabu da junansu fa. Abram ya zauna cikin ƙasar Kan’ana, Lot kuma ya zauna cikin biranin Filin, ya zakuɗa da [tanti] nasa har wajen Sodom.” (Farawa 13:11, 12) Sodom yana da ni’ima sosai kuma akwai amfani na kayayyaki. (Ezekiel 16:49, 50) Ko da zaɓe da Lot ya yi kamar da hikima bisa batun arziki, amma ba hikima ba ce a batun ruhaniya. Me ya sa? Domin “mutanen Sodom miyagu ne, masu-zunubi ne kuma ƙwarai a gaban Ubangiji,” in ji Farawa 13:13. Shawarar Lot ya ƙaura zuwa wajen daga baya zai jawo wa iyalinsa baƙin ciki.
13. Ta yaya misalin Abram yake da taimako ga Kiristoci da ƙila suke shiga jayayyar kuɗi?
13 Amma ko da Abram ya nuna bangaskiya cikin alkawarin Jehovah cewa tsatsonsa daga baya za su mallaki ƙasar; bai yi jayayya ba domin wani ɓangaren ƙasar. Hannu sake, ya aikata daidai da ƙa’idar da daga baya aka ambata a 1 Korinthiyawa 10:24: “Kada kowa shi biɗa ma kansa, amma abin da za ya amfana maƙwabcinsa.” Wannan tunasarwa ce mai kyau ga waɗanda suka shiga jayayyar kuɗi da ’yan’uwansu masu bi. Maimakon bin gargaɗi da ke a Matta 18:15-17, wasu sun kai ’yan’uwansu kotu. (1 Korinthiyawa 6:1, 7) Misalin Abram ya nuna cewa ya fi amfani mutum ya yi hasarar kuɗi da ya jawo kunya bisa sunan Jehovah ko kuma ya lalata salamar ikilisiyar Kirista.—Yaƙub 3:18.
14. Yaya za a albarkaci Abram saboda kasancewa da hannu sake?
14 Za a albarkaci Abram saboda kasancewa mai hannu sake. Allah ya sanar da cewa: “In maida tsatsonka kamar turɓayar ƙasa ga yawa: har za ya zama idan mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, tsatsonka ya ƙidayu.” Abin ƙarfafa ne bayanin nan ga Abram da ba shi da ɗa! Sai Allah ya umurta: “Tashi, ka yi tafiya cikin ƙasan, iyakar tsawonta da faɗinta; gama zan ba ka ita.” (Farawa 13:16, 17) A’a, ba za a ƙyale Abram ya more rayuwar birni ba. Zai kasance da bambanci daga Kan’aniyawan. Haka ma dole Kiristoci a yau su kasance a ware daga duniya. Ba sa ɗaukan kansu sun fi wasu, amma ba sa tarayya kurkusa da duk wanda zai yaudare su ga yin halaye da ba na Nassi ba.—1 Bitrus 4:3, 4.
15. (a) Ƙila menene muhimmancin tafiyar da Abram ya yi? (b) Wane misali Abram ya bar wa iyalan Kiristoci a yau?
15 A lokatan Littafi Mai Tsarki, kafin mutum ya sayi fili, ana bukatar ya zagaya shi. Saboda haka yin tafiya ciki zai zama tunasarwa ne cewa wata rana wannan ƙasar za ta zama na ’ya’yan Abram. Cikin biyayya, “sa’annan Abram ya cira [tanti] nasa, ya je ya zauna wajen itatuwa na Mamre, waɗanda ke cikin Hebron, can kuma ya gina bagadi ga Ubangiji.” (Farawa 13:18) Abram ya sake nuna muhimmanci da ya ba wa bauta. Nazari na iyali, addu’a ta iyali, da kuma halartan taron suna da wuri na musamman cikin iyalinka?
Farmakin Magabci
16. (a) Me ya sa kalmomin farko na Farawa 14:1 suke da nahisa? (b) Menene dalilin farmaki da sarakuna huɗu na gabas suka yi?
16 “Ananan cikin zamanin Amraphel sarkin Shinar, da Arioch sarkin Ellasar, da Chedorlaomer sarkin Elam,c da Tidal sarkin Goiim, ya zama suka yi gāba.” A asalin Ibrananci, kalmomin nan na farko (“Ananan cikin kwanakin . . . ”) suna da nahisa a yadda ake furta su, suna nuna “lokacin gwaji da ƙarshensa albarka ce.” (Farawa 14:1, 2, hasiya ta NW ) Gwajin ya soma sa’ad da waɗannan sarakuna huɗu da rundunarsu suka fāɗa wa Kan’ana. Menene manufarsu? Don su mukushe tawayen biranen nan biyar Sodom, Gomorrah, Admah, Zeboiim, da kuma Bela. Wajen nasara bisa kowacce tsayayya, sarakuna biyar ɗin suka gama kai a cikin kwari na Siddim (watau Bahar Mai-gishiri ke nan).” Lot da iyalinsa suna da zama kusa da wurin.—Farawa 14:3-7.
17. Me ya sa ɗaukan Lot zuwa bauta gwajin bangaskiya ne ga Abram?
17 Sarakunan Kan’aniyawan sun tsayayya wa wannan abokan gāba, amma an yi musu cin wulakanci. Sai masu nasarar “suka kwashe dukan dukiya ta Sodom da Gomorrah, har da dukan guzurinsu, suka yi tafiyarsu. Kuma suka ɗauki Lot, ɗan ƙanen Abram, da ya ke zaune cikin Sodom, da dukiyarsa kuma, suka tashi.” Nan da nan labarin wannan ya kai kunnen Abram: “Sai wani wanda ya tsira ya je, ya fāɗa ma Abram Ba’ibrane: yana zaune wajen itatuwa na Mamre, Ba’amoriyi, ɗan’uwan Eshcol, ɗan’uwan Aner; su kuma suna amana da Abram. Abram kuwa . . . ya ji an kama ɗan’uwansa.” (Farawa 14:8-14) Gwajin bangaskiya ne kuwa! Abram zai yi baƙin rai ne da ɗan wansa don ya zaɓi wuri mafi kyau? Ka kuma tuna cewa waɗannan abokan gāba sun fito ne daga ƙasarsa, Shinar. Yin yaƙi da su zai kau da wani zarafi na komawa garinsu ke nan. Ballantana ma, me Abram zai iya yi wa rundunar da rundunar Kan’aniyawa gabaki ɗaya ba su iya cinsu ba?
18, 19. (a) Ta yaya ne Abram ya ceci Lot? (b) Wa za a yaba wa don nasararsa?
18 Abram ya sake dogararsa gabaki ɗaya ga Jehovah. “Sai ya fita da nasa mazaje, horarun mutane, haifaffun gidansa, mutum ɗari uku da goma sha takwas, ya bi su kuma har ya kai Dan. Da dare fa ya rarraba mutanensa, shi da bayinsa, domin yaƙi da su, ya ɗibge su, ya bi su har Hobah, wadda ta ke arewa da Dimashƙa. Ya fa komo da dukiya duka, ya kuma komo da Lot, ɗan’uwansa, da dukiyarsa, da mata kuma, da mutane.” (Farawa 14:14-16) A nuna bangaskiya mai ƙarfi ga Jehovah, Abram ya ja-goranci rundunarsa waɗanda aka ɗara su zuwa cin nasara, ya ceci Lot da iyalinsa. Sai Abram ya sadu da Melchizedek, sarki kuma firist na Salem. “Melchizedek kuma sarkin Salem ya fito da gurasa da ruwan anab: shi kuwa [firist] ne na Allah Maɗaukaki. Ya albarkace shi, ya ce, Mai-albarka ne Abram na Allah Maɗaukaki, Mai-sama da ƙasa: Mai-albarka kuma Allah Maɗaukaki, wanda ya bada maƙiyanka cikin hannunka. Sai ya ba shi ushira ta kowane abu.”—Farawa 14:18-20.
19 Hakika, nasara ta Jehovah ce. Domin bangaskiyarsa, Abram ya sake samun ceto daga Jehovah. Mutanen Allah a yau ba sa sa hannu cikin yaƙi, amma suna fuskantar gwaji da kuma kalubale da yawa. Talifinmu na gaba zai nuna mana yadda misalin Abram zai taimake mu mu bi da irin waɗannan da kyau.
[Hasiya]
a In ji Insight on the Scriptures (wanda Shaidun Jehovah suka buga), “wani rubutu da aka yi ya faɗi game da Fir’auna cewa yana aika mutane da makamai don su ƙwace kyakkyawar mace kuma su kashe mijinta.” Saboda haka, dole ne Abram ya tsorata.
b Wataƙila Hajaratu, wadda ta zama kuyangar Abram, tana cikin bayin da aka ba Abram a lokacin.—Farawa 16:1.
c ’Yan sūka sun taɓa yin da’awa cewa Elam ba ta da irin ikon nan a Shinar kuma sun ce labarin farmakin Chedorlaomer ƙage ne. Don fahimtar tabbaci na ’yan tonan ƙasa da ke goyon bayan na Littafi Mai Tsarki, duba Hasumiyar Tsaro, na 1 ga Yuli, 1989 (Turanci), shafuffuka 4-7.
Ka Lura?
• Ta yaya yunwa da ke ƙasan Kan’ana ta zama gwajin bangaskiya wa Abram?
• Ta yaya Abram da Saraya suka bar misali mai kyau wa maza da mata a yau?
• Waɗanne darussa ne muka koya daga yadda Abram ya warware matsala tsakanin bayinsa da bayin Lot?
[Hoto a shafi na 12]
Abram bai nuna ikonsa ba amma ya sa na Lot a gaban nasa
[Hoto a shafi na 14]
Abram ya nuna dogara ga Jehovah wajen ceton ɗan wansa Lot