Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 9/1 pp. 15-19
  • Kada Ka Yi Kasala A Aikin Nagarta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Yi Kasala A Aikin Nagarta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Faɗāwa Kai Tsaye
  • Ɗawainiya ta Yau da Kullum
  • Gwaji da Muke Ɗora wa Kanmu
  • Bangaskiya Cikin Abubuwan da Ba a Gani Ba
  • Yadda Za Mu Sami Farin Ciki Duk da Tangarɗa
  • Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Kana Jiran “Birnin Nan Wanda Yake da Tushe”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • An Gwada Bangaskiyarsa
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 9/1 pp. 15-19

Kada Ka Yi Kasala A Aikin Nagarta

“Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi za mu girbe, in ba mu yi suwu ba.”—GALATIYAWA 6:9.

1, 2. (a) Me ya sa ake bukatar haƙuri don a bauta wa Allah? (b) Ta yaya Ibrahim ya nuna haƙuri, kuma me ya taimake shi ya yi haka?

MU Shaidun Jehovah, muna farin ciki wajen yin nufin Allah. Muna kuma samun wartsakewa da muka ɗauki “karkiya” ta almajiranci. (Matta 11:29) Duk da haka, bauta wa Jehovah tare da Kristi ba kullum yake da sauƙi ba. Manzo Bulus ya bayyana wannan yayin da ya aririci ’yan’uwa Kirista: “Kuna da bukatar haƙuri, domin, bayanda kun aika nufin Allah, ku karɓi alkawarin.” (Ibraniyawa 10:36) Ana bukatar haƙuri domin bauta wa Allah tana da kalubale.

2 Rayuwar Ibrahim lalle ta tabbatar da wannan. A lokatai da yawa ya fuskanci zaɓe masu wuya da kuma yanayi mai wahala. Da aka umurce shi ya bar rayuwar morewa a Ur, mafari ne kawai. Ba da daɗewa ba, ya fuskanci yunwa, ƙiyayya daga maƙwabtansa, kusan ya yi hasarar matarsa, da ƙiyayya daga wasu dangi, da kuma mugunta ta yaƙi. Har ila, manyan gwaji na gaba. Amma Ibrahim bai kasala ba a aikin nagarta. Wannan abin mamaki ne musamman idan ka lura cewa ba shi da cikakkiyar Kalmar Allah yadda muke da ita a yau. Babu shakka, yana da sani game da annabci na farko, wanda ciki Allah ya ce: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma.” (Farawa 3:15) Tun da yake ta wurinsa ne Ɗan zai fito, lalle Ibrahim zai fuskanci magabtaka daga Shaiɗan. Babu shakka fahimtar wannan ya taimake Ibrahim ya jimre wa gwajinsa cikin farin ciki.

3. (a) Me ya sa mutanen Jehovah a yau za su zaci wahala? (b) Wace ƙarfafa Galatiyawa 6:9 ta ba mu?

3 Mutanen Jehovah a yau ma ya kamata su yi tsammanin wahala. (1 Bitrus 1:6, 7) Ballantana ma, Ru’ya ta Yohanna 12:17 ta faɗakar da mu cewa Shaiɗan yana ‘yaƙi’ da raguwar shafaffu. Saboda haka, tarayyarsu na kurkusa da shafaffu, “waɗansu tumaki” ma sun zama abin hasala na Shaiɗan. (Yohanna 10:16) Ban da hamayya da Kiristoci suke fuskanta a hidimarsu ta fage, suna kuma samun wasu matsi na gwaji a rayuwarsu. Bulus ya gargaɗe mu: “Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi za mu girbe, in ba mu yi suwu ba.” (Galatiyawa 6:9) Amma, ko da Shaiɗan ya nufa ya halaka bangaskiyarmu, dole ne mu tsaya gāba da shi, da ƙarfi a bangaskiya. (1 Bitrus 5:8, 9) Me zai iya zama sakamakon bin tafarkinmu na aminci? Yaƙub 1:2, 3 ya bayyana haka: “ ’Yan’uwana, kadan jarabobi masu-yawa sun same ku, ku maishe shi abin farinciki sarai; kun sani gwadawar bangaskiyarku tana jawo haƙuri.”

Faɗāwa Kai Tsaye

4. Ta yaya Shaiɗan ya yi amfani da farmaki kai tsaye a ƙoƙarin karya amincin mutanen Allah?

4 Rayuwar Ibrahim lalle ta nuna “jarrabobi masu-yawa” da Kirista zai fuskanta a yau. Alal misali, dole ne ya mai da martani ga farmakin runduna daga Shinar. (Farawa 14:11-16) Ba abin mamaki ba ne, Shaiɗan ya ci gaba da yin amfani da farmaki kai tsaye kamar su tsanantawa. Tun ƙarshen Yaƙin Duniya na II, gwamnonin ƙasashe da yawa sun kafa taƙunƙumi a kan aikin Kirista na ilimantarwa na Shaidun Jehovah. Littafin nan 2001 Yearbook of Jehovah’s Witnesses ya faɗi game da nuna ƙarfi da Kiristoci suka jimre a Angola a hannun magabta. Ta wajen dogara ga Jehovah, ’yan’uwanmu a ƙasashen nan cikin aminci sun ƙi su daina! Sun amsa ba ta wurin ramako da nuna ƙarfi ba ko kuma ta tawaye, amma ta naciya cikin aikin wa’azi da hikima.—Matta 24:14.

5. Ta yaya ake tsananta wa matasa Kirista a makaranta?

5 Amma kuma, tsanani ba lalle sai ya haɗa da nuna ƙarfi ba. A ƙarshe an albarkaci Ibrahim da ’ya’ya maza biyu—Isma’ila da Ishaƙu. Farawa 21:8-12 sun gaya mana cewa a wani lokaci Isma’ila yana wa Ishaƙu “ba’a.” A cikin wasiƙarsa zuwa ga Galatiyawa, Bulus ya nuna cewa wannan ba wasan yara ba ne kawai, domin ya kwatanta Isma’ila cewa yana tsananta wa Ishaƙu! (Galatiyawa 4:29) Ba’a daga abokan makaranta da baƙar magana daga wajen ’yan hamayya za a iya kiran su tsanantawa. Wani matashi Kirista mai suna Ryan ya tuna yadda ya wahala a hannun ’yan ajinsa: “Minti 15 na tafiya da dawowa daga makaranta kama yake da awoyi domin yadda ake yi mini baƙar magana. Su ƙone ni da ƙarfe mai zafi da suka saka a wutar sigari.” Menene dalilin wannan mugun hali? “Reno na ne na tsarin Allah ya sa na bambanta da sauran matasa na makarantar.” Duk da haka, tare da taimakon iyayensa, Ryan ya jimre da aminci. Matasa, zolayar tsaranku tana sa ku ku yi sanyin gwiwa ne? To, kada ku yi kasala! Ta jimrewa da aminci, za ku ɗanɗana cikar kalmomin Yesu: “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zaginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowace irin mugunta, sabili da ni.”—Matta 5:11.

Ɗawainiya ta Yau da Kullum

6. Waɗanne abubuwa za su iya lalata dangantaka mai kyau tsakanin ’yan’uwa Kirista a yau?

6 Yawancin jarraba da muke fuskanta a yau sun haɗa da ɗawainiya ta yau da kullum. Ibrahim kansa ma ya jimre da jayayya da ta taso tsakanin makiyayarsa da na ɗan wansa Lot. (Farawa 13:5-7) A makamancin hanyar nan a yau, jayayya ko ƙananan kishi suna hana dangantaka mai kyau har ma razanar da salamar ikilisiyar. “Wurinda kishi da tsaguwa su ke, nan akwai yamutsai da kowane irin mugun al’amari.” (Yaƙub 3:16) Lalle yana da muhimmanci a gare mu kada mu yi kasala amma mu sa salama a gāba da fahariya, yadda Ibrahim ya yi, kuma mu biɗa wa wasu!—1 Korinthiyawa 13:5; Yaƙub 3:17.

7. (a) Me ya kamata mutum ya yi idan ɗan’uwa Kirista ya ɓata masa rai? (b) Ta yaya Ibrahim ya bar misali mai kyau na riƙe dangantaka mai kyau da wasu?

7 Kasancewa masu neman salama zai zama da wuya musamman idan muna jin wani ɗan’uwa mai bi ya ɓata mana rai. Misalai 12:18 ta ce: “Akwai wanda ya kan yi magana da garaje kamar sussukan takobi.” Magana da garaje, idan aka yi ta ko da rashin sani ne, takan yi ciwo sosai. Ciwon zai fi tsanani ma idan muna jin cewa an yi mana tsegumi ko an yi gulmanmu. (Zabura 6:6, 7) Amma Kirista ba zai yarda irin wannan ya sa shi ya yi kasala ba! Idan kana cikin irin yanayin nan, ka ɗauki matakin warware matsalar ta wurin yin magana da wanda ya yi maka laifin cikin alheri. (Matta 5:23, 24; Afisawa 4:26) Ka yi niyyar gafarta wa mutumin. (Kolossiyawa 3:13) Ta mancewa da laifin, muna warkar da namu tsotsuwar zuciya da kuma dangantakarmu da ɗan’uwanmu. Ibrahim bai ci gaba da ganin laifin Lot ba da ƙila ya yi. Hakika, Ibrahim ya ruga ya tsare Lot da iyalinsa!—Farawa 14:12-16.

Gwaji da Muke Ɗora wa Kanmu

8. (a) Ta yaya Kiristoci za su iya huda kansu da baƙin ciki da yawa? (b) Me ya sa Ibrahim ya iya kasancewa da daidaicaccen ra’ayi na abin duniya?

8 Hakika, wasu gwaji mu muke jawo wa kanmu. Alal misali, Yesu ya umurci mabiyansa: “Kada ku ajiye wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke cinyewa, inda ɓarayi kuma ke hudawa suna sata.” (Matta 6:19) Duk da haka, wasu ’yan’uwa suna “huda kansu da baƙinciki mai-yawa” ta sa abin duniya a gaba da abubuwan Mulki. (1 Timothawus 6:9, 10) Ibrahim ya kasance a shirye ya sadaukar da abin duniya don ya faranta wa Allah rai. “Ta wurin bangaskiya ya baƙunta cikin ƙasar alkawari, sai ka ce ba tasa ba ce, yana zaune cikin [tanti], tare da Ishaƙu da Yakubu, magāda tare da shi na alkawarin: gama yana tsumayen birnin da ke da tussa, wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.” (Ibraniyawa 11:9, 10) Bangaskiyar Ibrahim cikin “birni” na nan gaba, ko cikin gwamnati ta Allah ta taimake shi bai dogara ga arziki ba. Mu ma ba za mu yi hikimar yin haka ba?

9, 10. (a) Ta yaya burin son yin suna zai jawo gwaji? (b) Ta yaya a yau ɗan’uwa zai mai da kansa ‘ƙarami’?

9 Lura da wani gefe kuma. Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan ja-gora mai ƙarfi: “Idan mutum ya zaci kansa wani abu ne, shi kuwa ba kome ba ne, ruɗin kansa ya ke yi.” (Galatiyawa 6:3) Ban da haka ma, an aririce mu “kada [mu] yi kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u.” (Filibbiyawa 2:3) Wasu suna ƙoƙarin jawo wa kansu gwaji ta ƙin yin amfani da wannan gargaɗin. Domin burin yin suna da suke da shi maimakon burin yin “nagarin aiki,” sukan yi sanyin gwiwa kuma su nuna rashin gamsuwa yayin da ba su samu wasu gata cikin ikilisiya ba.—1 Timothawus 3:1.

10 Ibrahim ya bar misali mai kyau na ‘ƙin aza kansa gaba da inda ya kamata.’ (Romawa 12:3) Yayin da ya sadu da Melchizedek, Ibrahim bai nuna cewa albarkarsa gaban Allah ya fifita shi ba. Maimako ma, ya fahimci babban matsayin Melchizedek wanda firist ne ta biyansa ushira. (Ibraniyawa 7:4-7) Ya kamata Kiristoci a yau ma su kasance a shirye su mai da kansu ‘ƙanana’ don kar su so matsayin da za a san da su. (Luka 9:48) Idan waɗanda suke jagabanci cikin ikilisiya kamar suna hana ka gata, ka bincika kanka sosai kuma ka yi gyara da za ka iya a mutumtakarka ko a yadda ka ke yin abubuwa. Maimakon ka yi fushi game da gatar da ba ka da ita, ka yi amfani sosai da wadda ka ke da ita—gatar taimakon wasu su san Jehovah. I, “ku ƙasƙantarda kanku . . . ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, domin shi ɗaukaka ku loton da ya zama daidai.”—1 Bitrus 5:6.

Bangaskiya Cikin Abubuwan da Ba a Gani Ba

11, 12. (a) Me ya sa wataƙila wasu cikin ikilisiyar sun yi rashin azancinsu na gaggawa? (b) Ta yaya Ibrahim ya bar misali mai kyau na yin rayuwarsa ta kasancewa da bangaskiya cikin alkawuran Allah?

11 Wani gwaji zai iya zama na ganin kamar ƙarshen wannan mugun tsarin abubuwan ya makara. In ji 2 Bitrus 3:12, Kiristoci za su yi “sauraron ranar Allah, [suna] kuwa marmarin zuwanta ƙwarai.” Amma kuwa, mutane da yawa sun jira wannan “ranar” na shekaru da yawa. Domin haka, wasu sun yi sanyin gwiwa kuma sun yi rashin azanci na gaggawarta.

12 Har ila kuma, ka yi la’akari da misalin Ibrahim. Ya yi rayuwarsa gabaki ɗaya a kan bangaskiya cikin alkawuran Allah, ko da ma bai yiwu su cika a lokacin rayuwarsa ba. Hakika, ya rayu na dogon lokaci da ya ga ɗansa Ishaƙu ya yi girma. Amma zai kai ƙarnuka kafin ’ya’yan Ibrahim su kai “kamar taurarin sama” ko kuma “kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku.” (Farawa 22:17) Wannan bai sa Ibrahim ya yi fushi ba ko sanyin gwiwa. Manzo Bulus ya gaya mana game da Ibrahim da wasu ubanni: “Dukan waɗannan suka mutu cikin bangaskiya, ba su rigaya sun amshi alkawura ba, amma daga nesa suka tsinkaye su, suka yi musu maraba, suka shaida hakanan su baƙi ne, bare ne cikin duniya.”—Ibraniyawa 11:13.

13. (a) Ta yaya ne Kiristoci a yau suke kamar “baƙi”? (b) Me ya sa Jehovah zai kawo ƙarshe ga wannan tsarin abubuwa?

13 Idan Ibrahim ya sa rayuwarsa a kan alkawuran da cikarsu “daga nesa” ne, muna bukatar mu fi shi mu da a yau muke kusa haka da cikar waɗannan abubuwa! Kamar Ibrahim, dole ne mu ɗauki kanmu kamar “baƙi ne” cikin tsari na Shaiɗan, mu ƙi zama mazauna a zancen bin yayin rayuwa na almubazzaranci. Son samu, za mu so “matuƙar dukan abu” ta zo nan da nan, ba kawai ta yi kusa ba. (1 Bitrus 4:7) Wataƙila muna wahala don ciwo mai tsanani. Ko kuwa muna shan wahala domin matsi na tattalin arziki. Amma dole mu tuna cewa Jehovah zai kawo ƙarshe, ba don kawai ya cece mu daga yanayi na wahala ba, amma domin ya tsarkake sunansa. (Ezekiel 36:23; Matta 6:9, 10) Ƙarshen zai zo, ba kawai a lokacin da ya fi mana kyau ba, amma lokacin da zai cika ƙudurin Jehovah.

14. Ta yaya ne haƙurin Allah ya amfane Kiristoci a yau?

14 Ka kuma tuna cewa, “Ubangiji ba mai-jinkiri ba ne ga zancen alkawarinsa, yadda waɗansu mutane su ke aza jinkiri; amma mai-haƙuri ne zuwa gareku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:9) Ka lura, Allah yana “haƙuri ne zuwa gareku”—waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista. Babu shakka, wasunmu na bukatar ƙarin lokaci don yin canje-canje sabili da a “tararda ku cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gabansa.” (2 Bitrus 3:14) Bai kamata mu yi godiya ba cewa Allah ya yi irin wannan haƙuri haka?

Yadda Za Mu Sami Farin Ciki Duk da Tangarɗa

15. Ta yaya Yesu ya riƙe farin cikinsa a lokacin gwaji, kuma ta yaya yin koyi da shi zai amfane Kiristoci a yau?

15 Rayuwar Ibrahim ta koya wa Kiristoci darussa a yau. Ba kawai ya nuna bangaskiya ba amma haƙuri, hikima, ƙarfin zuciya, da kuma ƙauna mara son kai. Ya sa bautar Jehovah muhimmi cikin rayuwarsa. Dole a tuna cewa misali mafi girma dominmu mu koya shi ne wanda Yesu Kristi ya kafa. Shi kansa ya fuskanci gwaji da jarraba da yawa, amma cikin duka, bai taɓa rashin farin cikinsa ba. Me ya sa? Domin ya sa zuciyarsa kan begen da ke a nan gaba. (Ibraniyawa 12:2, 3) Domin haka Bulus ya yi addu’a: “Yanzu dai Allah na haƙuri da na ta’aziyya shi yarda muku ku zama da hankali ɗaya da junanku bisa ga Kristi Yesu.” (Romawa 15:5) Tare da hali mai kyau, za mu sami farin ciki duk da tangarɗa da Shaiɗan zai sa a gabanmu.

16. Me za mu iya yi yayin da matsalolinmu kamar za su sha kanmu?

16 Yayin da kamar matsaloli za su sha kanka, ka tunasar da kanka cewa yadda ya ƙaunaci Ibrahim, Jehovah yana ƙaunarka. Yana son ka yi nasara. (Filibbiyawa 1:6) Ka sa dogararka cikin Jehovah, da gaba gaɗin cewa “ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Korinthiyawa 10:13) Ka koyi halin karanta Kalmar Allah kowacce rana. (Zabura 1:2) Ka nace cikin addu’a, kana roƙon Jehovah ya taimake ka ka jimre. (Filibbiyawa 4:6) Zai “bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa.” (Luka 11:13) Ka yi amfani da tanadin da Jehovah ya yi don kiyaye ka a ruhaniya, kamar su littattafai masu tushe na Littafi Mai Tsarki. Ka kuma nemi tallafawar ’yan’uwanci. (1 Bitrus 2:17) Ka halarci taron Kiristoci kullum, domin daga wurin za ka sami ƙarfafa da ka ke bukata don ka jimre. (Ibraniyawa 10:24, 25) Ka yi murna cewa jimrewarka ya kai samun tagomashi a gaban Allah kuma cewa amincinka ya faranta masa rai!—Misalai 27:11; Romawa 5:3-5.

17. Me ya sa Kiristoci ba za su fid da rai ba?

17 Allah ya ƙaunaci Ibrahim ya zama ‘abokinsa.’ (Yaƙub 2:23) Duk da haka, rayuwar Ibrahim ta cika da wahalar gwaji da ƙunci. Saboda haka, Kiristoci za su zaci irin haka a waɗannan miyagun “kwanaki na ƙarshe.” Hakika, Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa “miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba.” (2 Timothawus 3:1, 13) Maimakon fid da rai, mu fahimci cewa matsin da muke fuskanta tana ba da tabbaci ne cewa ƙarshen mugun tsarin Shaiɗan ya kusa. Amma Yesu ya tuna mana cewa “wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.” (Matta 24:13) Saboda haka, ‘kada ka kasala a aikin nagarta!’ Ka yi koyi da Ibrahim, domin ka kasance tsakanin waɗanda “ke gāda alkawura ta wurin bangaskiya da haƙuri.”—Ibraniyawa 6:12.

Ka Lura?

• Me ya sa mutanen Jehovah a yau za su yi tsammanin gwaji da kuma ƙunci?

• A waɗanne hanyoyi Shaiɗan zai iya amfani da farmaki?

• Ta yaya za a iya warware jayayya tsakanin Kiristoci?

• Ta yaya fahariya da girman kai za su iya jawo gwaji?

• A wace hanya ce Ibrahim ya bar misali mai kyau na jirar cikar alkawuran Allah?

[Hoto a shafi na 16]

Kiristoci matasa da yawa suna shan tsanani, tsaransu suna zolayarsu

[Hoto a shafi na 19]

A zamanin Ibrahim cikar alkawuran Allah “daga nesa” suke, duk da haka ya kewaye rayuwarsa da su

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba