Ibrahim Misali Ne Na Bangaskiya
“[Ibrahim ne] uban masu-bada gaskiya duka.”—ROMAWA 4:11.
1, 2. (a) Da me ake tuna da Ibrahim tsakanin Kiristoci na gaskiya a yau? (b) Me ya sa aka kira Ibrahim “uban masu-bada gaskiya duka”?
KAKAN wata babbar al’umma ne, annabi ne, ɗan kasuwa ne, kuma shugaba ne. Saboda haka, a tsakanin Kiristoci a yau, ana tunawa da shi sosai domin halinsa da ya motsa Jehovah Allah ya yi abokantaka da shi—bangaskiyarsa mara girgiza. (Ishaya 41:8; Yaƙub 2:23) Sunansa Ibrahim, kuma Littafi Mai Tsarki ya kira shi “uban masu-bada gaskiya duka.”—Romawa 4:11.
2 Mutane da suka riga Ibrahim, kamar su Habila, Ahnuhu, da Nuhu ba sun nuna bangaskiya ba? E, amma da Ibrahim ne aka yi alkawarin za a albarkaci dukan al’ummai na duniya. (Farawa 22:18) Da haka, ya zama, ta alama uban dukan waɗanda za su ba da bangaskiya ga Zuriyar. (Galatiyawa 3:8, 9) A wata hanya, za a iya ɗaukan Ibrahim ubanmu, domin bangaskiyarsa ta zama misali da za mu yi koyi da ita. Za a iya ɗaukar dukan rayuwarsa nuni ce ta bangaskiya, domin ya ƙunshi gwaji da jarrabobi da yawa. Hakika, da daɗewa kafin Ibrahim ya fuskanci abin da za a ce gwajin bangaskiya mafi girma—watau umurnin ya yi hadaya da ɗansa Ishaƙu—Ibrahim ya tabbatar da bangaskiyarsa a ƙananan jarrabobi. (Farawa 22:1, 2) Yanzu bari mu bincika wasu cikin waɗannan gwajin bangaskiya na farko kuma mu ga darussa da za su koya mana a yau.
Umurnin Ya Bar Ur
3. Menene Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da inda Abram ya fito?
3 Littafi Mai Tsarki ya gabatar mana Abram (wanda daga baya aka kira shi Ibrahim) a Farawa 11:26, da ta ce: “Terah kuma ya yi shekara saba’in, kana ya haifi Abram da Nahor, da Haran.” Abram daga zuriyar Shem ne mai tsoron Allah. (Farawa 11:10-24) In ji Farawa 11:31, Abram yana tare da iyalinsa a “Ur na Chaldiyawa” mai ni’ima, birnin da a dā yake gabashin Kogin Euphrates.a Saboda wannan, bai yi girma yana zaman makiyayi ba a daji amma mazauni ne a birni, inda yake da abubuwan shaƙatawa da yawa. Ana samun kayayyakin ƙasashen waje a kasuwar Ur. Manyan gidaje masu famfuna, da suke kan titunansa.
4. (a) Waɗanne kalubale ne waɗanda suke bauta wa Allah na gaskiya suka fuskanta a ƙasar Ur? (b) Ta yaya Abram ya zo ga nuna bangaskiya ga Jehovah?
4 Ban da yawan abin duniya da yake da shi, Ur kalubale ne ƙwarai ga wanda yake son ya bauta wa Allah na gaskiya. Birni ne da ke cike da bautar gumaka da camfi. Hakika, babban ginin da ke birnin, hasumiya da aka gina don ɗaukaka allahn-wata ne Nanna. Babu shakka kuwa da Abram ya fuskanci matsi ya saka hannu cikin irin mummunar bautar nan, wataƙila ma matsi daga wasu cikin danginsa. Bisa ga wasu al’adu na Yahudawa, uban Abram, Terah shi kansa mai ƙera gumaka ne. (Joshua 24:2, 14, 15) Ko yaya yake dai, Abram ba mai bauta ta ƙarya, ƙasƙantacciya ba ne. Kakansa da ya tsufa Shem yana da rai kuma babu shakka ya gaya masa game da Allah na gaskiya. Domin haka, Abram ya nuna bangaskiya ga Jehovah, ba ga Nanna ba!—Galatiyawa 3:6.
Gwajin Bangaskiya
5. Wane umurni da kuma alkawari ne Allah ya yi wa Abram tun yana Ur?
5 Za a gwada bangaskiyar Abram. Allah ya bayyana gare shi kuma ya umurce shi: “Ka fita daga ƙasarka, daga danginka kuma, da gidan ubanka, zuwa ƙasa da zan nuna maka: daga wurinka zan yi al’umma mai-girma, zan albarkace ka kuma, in sa ka yi suna; ka zama albarka: waɗanda sun albarkace ka zan albarkace su, in la’antarda wanda ya la’antarda kai: a cikinka kuma dukan kabilan duniya za su yi albarka.”—Farawa 12:1-3; Ayukan Manzanni 7:2, 3.
6. Me ya sa ya bukaci bangaskiya ta ƙwarai daga Abram don ya bar ƙasar Ur?
6 Abram ya tsufa kuma ba shi da ɗa. Yaya zai zama “al’umma mai-girma”? Wai shin a ina ne wannan ƙasar da aka umurce shi ya je take? Allah bai gaya masa ba a lokacin. Saboda haka, ya bukaci bangaskiya ta ƙwarai daga Abram don ya bar ƙasar Ur mai ni’ima da dukan moriyarta. Littafin nan Family, Love and the Bible ya lura da lokatan dā: “Horo mafi tsanani da za a yi wa wani da ya yi laifi mai tsanani shi ne a kore shi daga tsakanin iyalinsa, a hana shi ci gaba da ‘zama ɗaya’ cikin iyalin. . . . Abin da ya sa ke nan ya zama biyayya mafi girma babu tuhuma kuma dogara ce ga Allah yayin da Ibrahim, ba kawai ya bar ƙasarsa ba, amma har da danginsa don ya amsa kiran da Allah ya yi masa.”
7. Ta yaya Kiristoci a yau za su iya fuskantar gwaji irin waɗanda Abram ya fuskanta?
7 A yau Kiristoci za su iya fukantar gwaji irin wannan. Kamar Abram, za mu matsu mu saka abin duniya a gaba da abubuwa na Allah. (1 Yohanna 2:16) Za mu iya fuskantar hamayya daga waɗanda suke cikin iyalinmu da ba masu bi ba ne, har da waɗanda aka yi musu yankan zumunci, waɗanda za su so su jawo mu cikin mummunar tarayya. (Matta 10:34-36; 1 Korinthiyawa 5:11-13; 15:33) Ta haka Abram ya kafa mana misali mai kyau. Ya sa abota da Jehovah gaba da kome—har da gami na iyali ma. Bai san ainihin yadda, ko yaushe ne, ko kuma inda alkawuran Allah za su cika ba. Duk da haka, a shirye yake ya ba da ransa ga alkawuran nan. Dubi yadda wannan ƙarfafa ce mai kyau mu saka Mulkin da farko a rayuwarmu a yau!—Matta 6:33.
8. Ta yaya bangaskiyar Abram ta taɓa waɗanda suke cikin iyalinsa, kuma me Kiristoci za su koya daga wannan?
8 Me za a ce game da waɗanda suke cikin iyalin Abram? Mai yiwuwa ne cewa bangaskiyar Abram da kuma tabbacinsa sun taɓa su, domin matarsa, Saraya, da ɗan wansa maraya da ake kira Lot sun motsa su amsa kiran Allah kuma sun bar Ur. Ɗan’uwan Abram, Nahor da wasu yaransa daga baya suka bar Ur kuma suka zauna a Haran, a wurin suka bauta wa Jehovah. (Farawa 24:1-4, 10, 31; 27:43; 29:4, 5) Hakika, har uban Abram, Terah ma ya yarda ya bi ɗansa! Saboda haka Littafi Mai Tsarki ya ce game da Terah ya ƙaura zuwa Kan’ana, tun da shi ne shugaban iyalin. (Farawa 11:31) Mu ma za mu iya samun ɗan nasara idan muka yi wa danginmu wa’azi cikin basira?
9. Waɗanne shirye-shirye Abram ya yi don tafiyarsa, kuma me ya sa lalle ya ƙunshi sadaukarwa?
9 Kafin ya fara tafiyarsa, Abram yana da abin yi da yawa. Zai sayar da gida da kayayyaki kuma ya sayi tanti, raƙumai, abinci, da kayayyakin da ake bukata. Wataƙila Abram ya ɗan yi hasarar kuɗi don shiri na gaggawa haka, amma yana murna ya yi wa Jehovah biyayya. Lalle zai zama rana ce ta musamman sa’ad da aka gama shiri kuma ayarin Abram yana tsaye a bayan garun Ur, a shirye domin su fara tafiya! Suka bi Kogin Euphrates da ya tanƙware, ayari ya bi arewa maso yamma. Bayan tafiya na makonni, tafiyar wajen mil 600, suka iso wani birni da ke arewacin Mesopotamiya da ake kira Haran, babban wajen hutun ayarori.
10, 11. (a) Menene wataƙila ya sa Abram ya zauna na ɗan lokaci a Haran? (b) Wace ƙarfafa za a yi wa Kiristoci da suke kula da iyaye tsofaffi?
10 Abram ya zauna a Haran, wataƙila ya yi hakan saboda ubansa da ya tsufa, Terah. (Leviticus 19:32) Kiristoci da yawa a yau ma suna da hakkin lura da iyaye da suka tsufa ko kuma marasa lafiya, wasu ma sun yi gyara don su yi haka. Sa’ad da hakan ya dace, za a iya tabbatar wa waɗannan cewa sadaukarwa da suke yi “abin karɓa ne a wurin Allah.”—1 Timothawus 5:4.
11 Aka kwana biyu. “Kwanakin Terah fa shekara ce metin da guda biyar: Terah kuwa ya mutu cikin Haran.” Hakika Abram ya yi baƙin cikin wannan rashi, amma bayan da lokacin baƙin cikin nan ya ƙare, nan da nan ya fice. “Abram yana shekara saba’in da biyar sa’anda ya fita Haran. Abram ya ɗauki matatasa Saraya, da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan dukiyarsu da suka tattara, da masu-rai waɗanda suka samu cikin Haran; suka fita fa domin su tafi cikin ƙasar Kan’ana.”—Farawa 11:32; 12:4, 5.
12. Menene Abram ya yi sa’ad da yake barin Haran?
12 Yana da kyau a lura da cewa sa’ad da suke Haran, Abram ya tara ‘kayayyaki da yawa.’ Ko da yake ya sadaukar da abin duniya don ya bar Ur, Abram ya bar Haran attajiri. Hakika, wannan albarkar Allah ce. (Mai-Wa’azi 5:19) Ko da yake Allah bai yi alkawarin zai ba da arziki ba ga dukan mutanensa a yau, mai aminci ne ga alkawarinsa na biyan bukatun waɗanda suka bar ‘gidaje, ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata’ saboda Mulkin. (Markus 10:29, 30) Abram ma ya ‘sami masu rai,’ watau, bayi da yawa. Wani Fassarar a Urushalima da kuma Ainihin Aramanci da aka Fassara sun ce Abram ya ‘almajirantar.’ (Farawa 18:19) Bangaskiyarka tana motsa ka ka yi wa maƙwabta, abokan aiki, ko kuma abokan makaranta magana? Maimakon ya zauna kuma ya manta da umurnin Allah, Abram ya yi amfani da lokacinsa a Haran da kyau. Amma yanzu lokacinsa a wajen ya ƙare. “Abram fa ya tafi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.”—Farawa 12:4.
A Ƙetaren Euphrates
13. Yaushe ne Abram ya ƙetare Kogin Euphrates, kuma menene muhimmancin hakan?
13 Abram zai sake yin tafiya kuma. Sun bar Haran a baya, ayarinsa ya nufi yamma, suka yi tafiyar mil 55. Wataƙila Abram ya ɗan tsaya a wani masauƙi a ƙetaren Euphrates daga cibiyar kasuwanci na Karchemish. Wannan babban masauƙi ne da raƙumai suke ƙetarewa.b A wace rana ce ayarin Abram suka ƙetare kogin? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya auku ne shekara 430 kafin Fitowar Yahudawa daga Masar a ranar 14 ga Nisan, 1513 K.Z. Fitowa 12:41 ta ce: “Ya zama kuwa a ƙarshen shekarun nan arbaminya da talatin, a waccan rana fa, sai ya zama dukan rundunan Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.” Wataƙila alkawari na Ibrahim ya soma ne a ranar 14 ga Nisan, 1943 K.Z., sa’ad da Abram cikin biyayya ya ƙetare Euphrates.
14. (a) Menene Abram ya gani da idanunsa na basira? (b) A wace hanya ce mutanen Allah a yau suke da albarka fiye da ta Abram?
14 Abram ya bar birni mai ni’ima. Duk da haka, yanzu yana iya hangar “birni da ke da tussa,” gwamnatin adalci bisa mutane. (Ibraniyawa 11:10) I, da wannan ɗan sani, Abram ya soma fahimtar ƙudurin Allah na fansar bil Adam masu mutuwa. A yau, mun sami albarka ta fahimtar ƙudurin Allah sosai fiye da Abram. (Misalai 4:18) “Birni,” ko kuma Sarautar gwamnatin, wanda Abram yake bege yanzu ya kasance da gaske—an kafa a sammai tun shekara ta 1914. Saboda haka, bai kamata mu motsa mu yi aikin bangaskiya ba kuma mu dogara ga Jehovah?
Tafiya a Ƙasar Alkawari ta Fara
15, 16. (a) Me ya sa ake bukatar ƙarfin zuciya kafin Abram ya gina bagadi ga Jehovah? (b) Ta yaya Kiristoci a yau za su yi ƙarfin zuciya irin na Abram?
15 Farawa 12:5, 6 sun gaya mana: “Cikin ƙasar Kan’ana kuma suka zo. Abram kuma ya ratsa ƙasar har zuwa wurin Shechem, zuwa itacen terebinth na Moreh.” Shechem mil 30 ne a arewacin Urushalima a cikin kwari mai ni’ima da aka kira ta “aljanna ta ƙasa mai tsarki.” Ko da yake, “Kan’aniyawa ke cikin ƙasar sa’annan.” Tun da yake Kan’aniyawa lalatarsu ta yi yawa, Abram zai yi tsayin daka don ya tsare iyalinsa daga mummunar rinjayarsu.—Fitowa 34:11-16.
16 Lokaci na biyu ke nan, “Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, Ga tsatsonka zan bada wannan ƙasa.” Abin farin ciki ne! Lalle ya bukaci bangaskiya wajen Abram ya yi farin ciki a wani abin da ’ya’yansa ne kaɗai nan gaba za su more. Duk da haka, a nuna yarda Abram ya “gina bagadi ga Ubangiji, wanda ya bayyana gareshi.” (Farawa 12:7) Wani manazarin Littafi Mai Tsarki ya ba da shawara cewa: “Gina bagadi a ƙasar tabbaci ne na mallakar ta bisa damar mallakar ta wurin bangaskiyarsa.” Gina bagadin nan aiki ne na ƙarfin zuciya. Babu shakka, wannan bagadin irinsa ne aka ambata cikin Dokar alkawari, ya ƙunshi duwatsu (da ba a ƙera) ba. (Fitowa 20:24, 25) Shi ya sa lalle zai bambanta daga bagadai da Kan’aniyawa suke amfani da su. Da haka Abram ya ɗauki mataki da gaba gaɗi a fili cewa shi mai bauta wa Allah ne na gaskiya, Jehovah, yana barin kansa ga wani mugunta ko rauni. Mu kuma fa a yau? Wasunmu—musamman ma matasa—muna ƙin gaya wa maƙwabtanmu ko abokan makaranta su sani muna bauta wa Jehovah? Bari misalin Abram na gaba gaɗi ya ƙarfafa dukanmu mu yi alfaharin mu bayin Jehovah ne!
17. Ta yaya Abram ya tabbatar da kansa mai wa’azin sunan Allah, kuma menene wannan ke tunasar da Kiristoci a yau?
17 Duk inda Abram ya je, bautar Jehovah ce ta farko. “Daga can kuma ya ƙaura zuwa dutsen da ke gabashin Bethel, ya kafa [tanti] nasa, da ya tura Bethel a yamma, Ai kuma a gabas: can fa ya gina bagadi ga Ubangiji, ya kira kuma bisa sunan Ubangiji.” (Farawa 12:8) Furcin nan na Ibrananci “kira kuma bisa sunan” yana iya nufin “sanar (yi wa’azin) sunan Ubangiji.” Babu shakka, Abram ya sanar da sunan Jehovah da ƙarfin zuciya tsakanin maƙwabtansa Kan’aniyawa. (Farawa 14:22-24) Wannan ya tunasar mana da aikinmu mu sa hannu sosai yadda ya yiwu a “shaida sunansa” a yau.—Ibraniyawa 13:15; Romawa 10:10.
18. Yaya dangantakar Abram take da mazauna Kan’ana?
18 Abram bai zauna ya daɗe ba a duk waɗannan wuraren. “Abram fa ya yi ta tafiya, kudu dai ya ke nufa”—wani wuri kusan hamada ta kudancin duwatsun Yahuda. (Farawa 12:9) Ta ci gaba da tafiya da kuma sanar da kansu masu bautar Jehovah a dukan sababbin wajejen da suka sauƙa, Abram da iyalinsa sun ‘shaida hakan su baƙi ne, bare ne cikin ƙasar.’ (Ibraniyawa 11:13) Koyaushe suna guje wa yin abokantaka da maƙwabtansu arna. Dole ne Kiristoci a yau su kasance “ba na duniya ba.” (Yohanna 17:16) Sa’ad da muke yin alheri da kuma hankali wajen maƙwabtanmu da abokan aiki, za mu mai da hankali kada mu dulmuya cikin halaye da ke nuna halin duniya da take ware daga Allah.—Afisawa 2:2, 3.
19. (a) Me ya sa rayuwa irin ta makiyaya lalle za ta kawo gwaji wa Abram da Saraya? (b) Waɗanne kalubale ne suke kan hanya wa Abram?
19 Kada mu manta cewa yin gyara don rayuwa irin ta makiyaya ba zai kasance da sauƙi ba ga Abram ko Saraya. Suna ci daga garkensu maimakon sayan abinci daga manyan kasuwa na Ur; suna zama cikin tanti maimakon manyan gidaje masu kyau. (Ibraniyawa 11:9) Rayuwar Abram ta cika da aiki; yana da aiki mai yawa na kula da garke da kuma bayinsa. Babu shakka Saraya ta yi ayyuka da mata suke yi a al’adarsu: curi, gasa gurasa, burga wulu, ɗinkin tufafi. (Farawa 18:6, 7; 2 Sarakuna 23:7; Misalai 31:19; Ezekiel 13:18) Har ila yau, sababbin gwaji suna gaba tukuna. Ba da daɗewa ba, Abram da iyalinsa za su fuskanci yanayin da zai sa rayukansu cikin haɗari! Bangaskiyar Abram za ta iya tsaya wa kalubalan kuwa?
[Hasiya]
a Ko da yake a yanzu kogin Euphrates yana gudu wajen mil goma ta gabashin Ur na dā, alama ta nuna cewa a dā kogin yana gudu ta yammacin birnin ne. Shi ya sa aka faɗi cewa Abram ya fito daga “ƙetaren Kogin [Euphrates].”—Joshua 24:3.
b Ƙarnuka daga baya, Sarki Ashurnasirpal na II na Assuriya ya ƙetare Euphrates a kan gadan katakai kusa da Karchemish. Ko haka ne Abram kansa ya yi ko dai shi da ayarinsa sun yi iyo su ƙetare, Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba.
Ka Lura?
• Me ya sa aka kira Abram “uban masu-bada gaskiya duka”?
• Me ya sa ya bukaci bangaskiya daga Abram ya bar Ur na Chaldiyawa?
• Yaya Abram ya nuna cewa ya saka bautar Jehovah a farko?
[Hoto a shafi na 5]
Ya bukaci bangaskiya daga Abram don ya bar moriyar Ur
[Taswira a shafi na 6]
TAFIYAR ABRAM
Ur
Haran
Karchemish
KAN’ANA
Babbar Teku
[Inda aka Dauko]
Daidai da taswira da Pictorial Archive (Near Eastern History) Est. and Survey of Israel suke da hakkin wallafarta
[Hoto a shafi na 8]
Ta wajen zama cikin tanti, Abram da iyalinsa sun “shaida hakanan su baƙi ne, bare”