Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Yuli pp. 20-25
  • Ku Taimaka wa Mutane Su San Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Taimaka wa Mutane Su San Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU SAN JEHOBAH SOSAI
  • KU KOYA MUSU HALAYEN JEHOBAH
  • KU TAIMAKA MUSU SU YI AMFANI DA ABIN DA SUKA KOYA
  • JEHOBAH ZAI ALBARKACE KA IDAN KA SAN SHI
  • Ka Taimaka wa Ɗalibanka Su Zaɓi Bauta wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Taimaka wa Dalibinka Ya Cancanci Yin Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma—Sashe na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Yuli pp. 20-25

28 GA SATUMBA–4 GA OKTOBA, 2026

WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

Ku Taimaka wa Mutane Su San Jehobah

“Abin da zai sa su sami rai na har abada shi ne su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya.”—YOH. 17:3.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda za mu taimaka wa ɗalibanmu su san Jehobah, su kuma san halayensa da abubuwan da yake so da kuma waɗanda ba ya so.

1. Yaya kake ji idan ka ga wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki yana samun ci-gaba?

YAYA ka ji saꞌad da wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya halarci taro a karo na farko, ya soma yin kalami da yin waꞌazi, kuma daga baya ya yi baftisma? Hakika ka yi farin ciki! Jehobah ne ya cancanci yabo saboda ci-gaban da ɗalibinmu yake samuwa, kuma muna yaba masa don hakan.—1 Kor. 3:​5-9; 3 Yoh. 3, 4.

2. Mene ne nufin Jehobah ga ɗaliban Littafi Mai Tsarki? (1 Timoti 2:​3, 4)

2 Nufin Allah shi ne “dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (Karanta 1 Timoti 2:​3, 4.) Jehobah yana so mutane su san shi sosai, su kuma san nufe-nufensa. (Irm. 9:24) Hakan yana nufin cewa za su san koyarwar gaskiya. Mene ne koyarwar gaskiya take nufi? Ba ta nufin sanin abubuwa game da Allah kawai. Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce, hakan na nufin “mutum ya san abubuwa da za su motsa shi ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kusaci Allah.” Idan ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya san Jehobah sosai, hakan zai shafi yadda yake yin rayuwa. Kuma idan ya yi hakan, zai kasance da begen samun “rai na har abada.”—Yoh. 17:3.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Jehobah ya ba mu aiki mai muhimmanci, wato mu taimaka wa mutane su san shi. A talifin nan, za mu tattauna tambayoyin nan: Me ya sa ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna bukatar su san Jehobah sosai? Ta yaya za mu koya musu halayen Jehobah? Kuma ta yaya za mu taimaka musu su yi amfani da abin da suka sani game da Jehobah a rayuwarsu?

KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU SAN JEHOBAH SOSAI

4. Bisa ga Markus 12:​30, mene ne ya kamata mu mai da hankali a kai yayin da muke nazari da ɗalibinmu?

4 Yesu ya ce doka mafi muhimmanci ita ce mu ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarmu, da dukan ranmu, da dukan tunaninmu, da kuma dukan ƙarfinmu. (Karanta Markus 12:30.) Kafin ɗalibi ya ƙaunaci Jehobah, dole ne ya san Jehobah tukuna. Muna son ɗalibinmu ya yi baftisma domin yana ƙaunar Jehobah, ba domin yana so ya zama abokinmu, ko ya zama abokin wasu Shaidun Jehobah, ko kuma domin yana son wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Don haka, abin da zai fi dace mu mai da hankali a kai shi ne taimaka ma ɗalibinmu ya san Jehobah kuma ya ƙaunace shi.

5. Mene ne ƙaunar Jehobah zai sa ɗalibinka ya yi?

5 Akwai alaƙa tsakanin ƙauna da biyayya. Muddin ɗalibinka ya san Jehobah kuma ya soma ƙaunar sa, hakan zai sa ya yi wa Jehobah biyayya. Yesu ya ce: “Domin duniya ta san cewa ina ƙaunar Uban, ina yin daidai abin da Uban ya umurce ni in yi.” (Yoh. 14:31) Kamar yadda Yesu ya yi, ɗalibin da ya san Jehobah kuma yana ƙaunar sa, zai yi masa biyayya kuma ya riƙe amincinsa gare shi.—1 Yoh. 5:3.

6. Ta yaya sanin Jehobah zai taimaka ma ɗalibinka ya riƙa yanke shawarwari masu kyau? Ka ba da misali.

6 Zai yi ma ɗalibi sauƙi ya yanke shawarwari masu kyau idan ya san Jehobah sosai. Alal misali, idan mutum yana so ya koyi yadda ake tuƙa keke, ba zai zauna kawai yana lura da yadda wasu suke tuƙin ba, ko kuma ya karanta takardar da ta ba da bayani a kan keken ba. A maimakon haka, zai hau keken kuma ya yi awoyi yana gwada tuƙawa. Idan ya ci-gaba da yin hakan, zai koyi yadda zai tuƙa keken da kyau. Haka ma, ba nazarin Littafi Mai Tsarki ne kawai zai taimaka ma ɗalibi ya san Jehobah sosai ba, yana kuma bukatar ya lura da yadda shawarwarin da ya yanke bisa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suke kyautata rayuwarsa. Yayin da yake ƙara sanin Jehobah da kuma ganin yadda Jehobah yake taimaka masa, zai iya yanke shawara mai kyau a kowane yanayi.

7. Me ya taimaka ma Yusufu ya yi abin da ya dace?

7 Yusufu ya san Jehobah sosai, kuma hakan ya taimaka masa saꞌad da matar Fotifar ta so ya yi jimaꞌi da ita. Tun lokacin da Yusufu yake yaro, babu shakka ya ji labarin Adamu da Hauwaꞌu, da kuma Ibrahim da Saratu. (Far. 2:24; 20:​3, 6) Labaran nan sun taimaka masa ya san raꞌayin Jehobah game da aure da kuma jimaꞌi. Yusufu ya san Jehobah sosai shi ya sa ya ƙi yin abin da mata Fotifar ta ce ya yi, kuma ya gaya mata cewa “Don me zan yi wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?” (Far. 39:​7-9) Ya san abin da Jehobah yake so da abin da ba ya so. Ya kuma san abin da zai ɓata wa Allahnsa rai. Saboda haka, Yusufu ya yi abin da ya dace. Idan muka taimaka ma ɗalibanmu su san Jehobah da kuma halayensa sosai, hakan zai taimaka musu su yi abin zai sa shi farin ciki.

KU KOYA MUSU HALAYEN JEHOBAH

8. Ta yaya za ka yi amfani da littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! ka taimaka ma ɗalibinka ya san Jehobah?

8 Ta yaya za mu koya wa ɗalibanmu halayen Jehobah? Jehobah ya taimaka ma Ayuba ya san shi sosai ta wurin yi masa tambayoyi fiye da 50! (Ayu. 38:1–41:34) Mu ma za mu iya yin hakan. Littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! yana ɗauke da tambayoyi da za su taimaka ma ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya san halayen Jehobah a hankali a hankali. (Ka duba akwatin nan “Tambayoyin da Muke Koyarwa da Su.”) Don haka, ka yi amfani da tambayoyin wajen taimaka ma ɗalibinka ya san Jehobah.

Wata ꞌyarꞌuwa tana saurara yayin da ɗalibarta take amsa tambaya daga darasi na 17 na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!

Tambayoyin da Muke Koyarwa da Su

A littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, akwai tambayoyi da suke taimaka ma ɗalibi ya koyi game da Jehobah a hankali a hankali. Ga wasu daga cikinsu:

  • “Yaya Jehobah yake ganin masu yin waꞌazi?” (darasi na 21)

  • “Ta yaya abin da ka koya game da Jehobah da Yesu suka tabbatar maka cewa matakin da za su ɗauka [a Armageddon] zai amfane mu?” (darasi na 33)

  • “Yaya Jehobah zai ji saꞌad da ka zama mai hikima kuma ka yi masa biyayya? Me ya sa?” (darasi na 34)

  • “Yaya kake ganin Jehobah zai ji idan mutum ya yanke shawarar auran mutumin da ba ya ƙaunar Jehobah?” (darasi na 42)

  • “Ta yaya yadda Jehobah yake bi da waɗanda suka yi zunubi yake nuna cewa shi mai ƙauna ne, mai jinƙai, kuma ya san abin da ya dace da mu?” (darasi na 57)

9-10. (a) Mene ne zai taimaka ma ɗalibai su ƙara sanin Jehobah yayin da suke karatun Littafi Mai Tsarki? (Yakub 5:11) (b) Ka ba da misalin yadda wani labari a Littafi Mai Tsarki zai iya nuna abin da Jehobah yake so da wanda ba ya so.

9 Saꞌad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, mukan ƙarfafa su su riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana.a Ta yaya za mu taimaka musu su san Jehobah sosai yayin da suke karatun? Za mu iya gaya musu cewa a duk lokacin da suke karanta wani labari a cikin Littafi Mai Tsarki, su yi tunanin dalilin da ya sa Jehobah ya sa aka rubuta labarin a cikin Kalmarsa, da kuma halayen Jehobah da labarin ya nuna. Alal misali, ka ga abin da mabiyin Yesu mai suna Yaƙub ya rubuta game da Ayuba. Yaƙub bai mai da hankali a kan yadda Ayuba ya jimre kawai ba, amma ya kuma mai da hankali a kan halayen Jehobah, wato yadda yake da jinƙai da kuma tausayi.—Karanta Yakub 5:11.

10 Muna so ɗalibanmu su san yadda kowane labari ya nuna abin da Jehobah yake so da wanda ba ya so. A ce ɗalibinmu ya bincika akwatin nan “Ka Soma Karanta Littafi Mai Tsarki” a littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, kuma ya gaya mana cewa yana so ya karanta labarin yadda aka jefa Daniyel a ramin zakuna. Za mu iya gaya masa cewa yayin da yake karatun, ya yi tunani a kan tambayoyin nan: ‘Me ya sa Jehobah ya ceci Daniyel? Mene ne hakan ya koya mini game da abin da ke sa Jehobah farin ciki?’ (Dan. 6:​10, 22) Zai kuma iya yi ma kansa tambayoyin nan: ‘Mene ne ya faru da mutanen da suka zargi Daniyel? Mene ne hakan ya koya mini game da abin da ke ɓata ma Jehobah rai?’ (Dan. 6:​4, 5, 24) A ƙarshe, zai kuma iya yin tunani a kan wasu halayen Jehobah da labarin ya nuna.—Dan. 6:​26, 27.

11. Ta yaya za mu taimaka ma ɗalibinmu ya ga cewa Jehobah ne yake koyar da shi?

11 Muna farin ciki idan ɗalibinmu yana amfana daga abubuwan da yake koya daga Littafi Mai Tsarki. Amma zai dace mu taimaka masa ya gane cewa abin da yake koya daga wurin Jehobah ne. (Isha. 30:​20, 21) Ɗalibinmu zai iya gode mana don abubuwan da yake koya. Zai ma iya yaba mana don yadda muke koyarwa. Ba laifi ba ne idan ɗalibinmu ya yi hakan, amma zai dace mu miƙa godiyar da kuma yabon ga Jehobah.

KU TAIMAKA MUSU SU YI AMFANI DA ABIN DA SUKA KOYA

12-13. Ta yaya sanin Jehobah sosai zai taimaka ma ɗalibi idan ya yi masa wuya ya fahimci wani labari da ya karanta a Littafi Mai Tsarki? (Ka kuma duba hoton.)

12 Don mutum ya amfana sosai daga abubuwan da yake koya, dole ne ya bi abin da ya koya a rayuwarsa da su a rayuwarsa. To, ta yaya za ka taimaka ma ɗalibinka ya yi hakan? Za ka iya somawa da koya masa ya tuna da abin da ya koya game da Jehobah idan ya karanta wani labari da ya yi masa wuyar fahimta. Alal misali, idan yana karanta wani labari game da yadda Jehobah ya yi hukunci, zai iya yin tunani a kan dalilin da ya sa Jehobah ya hallaka wasu kuma ya bar wasu. Ta yaya za ka taimaka masa ya yi tunani a kan batun?

13 Za ka iya ƙarfafa shi ya yi tunani a kan abin da ya riga ya koya game da Jehobah. Alal misali, ka gaya masa ya tambayi kansa cewa: Yaya darajar rai yake a gun Jehobah? (2 Bit. 3:9) Wane abu mai muhimmanci ne Jehobah ya yi don ya cece mu, duk da cewa mu masu zunubi ne? (Afis. 2:​4, 5) Shin Jehobah yana hukunta marasa laifi ne? Idan mutum ya yi laifi, Jehobah zai ƙi ya hukunta shi ne? (Fit. 34:​6, 7) A wasu labaran Littafi Mai Tsarki, ba a ba da bayanai dalla-dalla yadda za mu fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya yanke wasu shawarwari ba. Ba ma bukatar mu san dalilin. Mun san Allahnmu kuma muna da tabbaci cewa zai yi abin da ya dace a ko yaushe.

Hotuna: ꞌYarꞌuwar tana taƙaita darasin da suka koya tare da ɗalibar. Na 1. Jehobah yana zauna a kujerar mulkinsa a sama. 2. Adamu da Hauwaꞌu suna tunanin ko su ci ꞌyaꞌyan itacen da aka ce kada su ci. Na 3. Wani tafin ƙafa yana murƙushe kan maciji. Na 4. Jirgin da Nuhu ya gyara a kan ruwa saꞌad da ake ambaliya. Na 5. Musa ya raba jar teku. Na 6. Gidan Rahab a tsaye, amma katangar Jeriko ya rushe. Na 7. Ebedmelek ya fitar d Irmiya daga rijiya. Na 8. Yesu a kan gungume.

Ka taimaka ma ɗalibinka ya tuna da abin da ya koya game da Jehobah idan ya karanta wani labari a Littafi Mai Tsarki da ya yi masa wuyar fahimta (Ka duba sakin layi na 12-13)


14. Ta yaya za mu taimaka ma ɗalibinmu idan wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta ɓata masa rai?

14 Ga hanya ta biyu da ɗalibi zai iya yin amfani da abin da ya koya game da Jehobah. A ce ɗalibinka ya soma halartar taro, sai wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi abin da ya ɓata masa rai. Ka gaya ma ɗalibinka ya yi bincike a kan yadda Jehobah yake ɗaukan ꞌyanꞌuwanmu, kuma ya yi tunani a kan tambayoyin nan: Wace sadaukarwa ce Jehobah ya yi don ya nuna cewa yana ƙaunar su? (Yoh. 3:16) Yaya Jehobah yake ji idan Kristoci suna da haɗin kai? (Zab. 133:1) Yaya Jehobah yake ji idan muna yin iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da zama da haɗin kai? (2 Kor. 13:11) Ka taimaka ma ɗalibinka ya san cewa Jehobah yana farin ciki idan mun mai da hankali a kan halaye masu na ꞌyanꞌuwanmu, maimakon kurakuransu.

15-16. (a) Ta yaya ɗalibi zai iya yin koyi da Yesu saꞌad da yake so ya yanke shawara mai muhimmanci? (Yohanna 8:29) (b) Ta yaya Marianne ta taimaka ma ɗalibarta ta yanke shawara mai kyau? (Ka kuma duba hoton.)

15 A ƙarshe, za ka iya taimaka ma ɗalibinka ya yi amfani da abin da ya koya daga Littafi Mai Tsarki ya yanke shawarwari masu kyau. Za ka iya soma da nuna masa abin da ke darasi na 35 na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, mai jigo “Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau.” Amma, a ce ɗalibinka ya yi bincike kuma ya yi adduꞌa, amma duk da haka bai san shawarar da zai yanke ba fa? Wataƙila yana ganin akwai ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da yawa a kan batun kuma bai san wanda zai bi ba. Za ka iya gaya masa ya yi tunani a kan misalin Yesu. Ta yaya Yesu ya yanke shawarwari? Ya ce: “Kullum ina yin abin da [Babana] yake so.” (Karanta Yohanna 8:29.) Ka ƙarfafa ɗalibin ya yi ma kansa tambayar nan, ‘Bisa ga binciken da na yi da kuma abubuwan da na riga na koya game da Jehobah, wace shawara ce ya kamata in yanke da zai sa shi farin ciki?’ Duk wata shawara da za ta sa Jehobah farin ciki, shawara ce mai kyau.

16 Wata mata a ƙasar Chile wadda take nazarin Littafi Mai Tsarki, ta bukaci ta yanke shawara mai muhimmanci. Iyalinta sun matsa mata ta karɓi wani aiki da ake biyan albashi mai yawa, amma aikin zai sa ta riƙa fasa taro. ꞌYarꞌuwa da ke nazari da ita mai suna Marianne ta ce: “Na ƙarfafa ta ta yi tunani a kan yadda Jehobah zai ji don shawarar da ta yanke. Shin zai yi farin ciki ne, ko kuma zai yi baƙin ciki? Na kuma ƙarfafa ta ta yi adduꞌa ga Jehobah a kan batun, kuma ta lura da yadda Jehobah zai taimaka mata. Ta ƙi ta karɓi aikin, kuma daga baya ta sami wani aikin da ya ba ta damar halartan taro babu fashi.” Ka lura cewa Marianne ba ta gaya wa ɗalibarta shawarar da za ta yanke ba, amma ta gaya mata ta yi tunani a kan abubuwan da ta riga ta sani game da Jehobah. Hakan ya sa ɗalibar ta ƙara yin kusa da Marianne, kuma ta ƙara yin kusa da Jehobah. Ga abin da Marianne ta faɗa game da ɗalibarta: “Ta koya cewa Jehobah zai kula da mu idan muka sa ayyukan ibada farko a rayuwarmu.”

Wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki ta ƙi ta karɓa wani aikin da aka ba ta, shugaban aikin na riƙe da takardar kwangilar da yake so ya ba ta.

Ka koya wa ɗalibinka yadda zai riƙa yanke shawarwari da za su sa Jehobah farin ciki (Ka duba sakin layi na 15-16)b


JEHOBAH ZAI ALBARKACE KA IDAN KA SAN SHI

17. Wane abu mafi muhimmanci ne ɗalibi yake bukatar ya koya?

17 Ɗalibanmu suna koyan abubuwa da yawa masu muhimmanci yayin da muke nazari da su. Alal misali, suna koyan abin da ke faruwa da mutum bayan ya mutu, da dalilin da ya sa Yesu ya mutu a madadinmu, da kuma abin da Mulkin Allah zai yi. Suna kuma koyan yadda aka tsara ƙungiyarmu, wato yadda muke taro, da aikin da dattawa suke yi da kuma aikin da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu take yi. Amma kamar yadda muka tattauna, muna so ɗalibanmu su koya fiye da waɗannan abubuwa. Muna so su san Jehobah sosai.

18. Waɗanne albarku ne waɗanda suka san Jehobah za su samu?

18 Koya ma wasu su san Jehobah babban gata ne a garemu! Waɗanda suka riga suka san Jehobah kuma suna bauta masa, suna farin ciki a yanzu. (Za 25:​12-15) A nan gaba, waɗanda suka “san shi wanda yake na gaskiya” za su samu rai na har abada. (1Yo 5:20) Amma ba shi ke nan ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “Allah ya san da” duk waɗanda suke yin iya ƙoƙarinsu don su san shi kuma su ƙaunace shi. (1 Kor. 8:3) Hakika, Allah Maɗaukaki yana ganin mu kuma yana ɗaukan mu a matsayin abokansa. Babu shakka wannan albarka ce mai kyau ga waɗanda suka san Allah na gaskiya!

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa dole ne ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya san game da Jehobah sosai?

  • Ta yaya za mu koya ma ɗalibin Littafi Mai Tsarki halayen Jehobah?

  • Ta yaya za mu taimaka ma ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da abubuwan da ya koya game da Jehobah?

WAƘA TA 84 Yin Hidima a Inda Akwai Bukata

a Maƙasudin da aka ambata a darasi na 05 na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! shi ne: “Ka soma karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana ta wurin amfani da sashen nan ‘Ka Soma Karanta Littafi Mai Tsarki.’”

b BAYANI A KAN HOTO: Hoton ya kwatanta yadda ɗalibar Marianne ta ƙi karɓan aikin da aka ba ta.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba