Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Yuli pp. 14-19
  • Ka Ci-gaba da Koya don Ka Ƙara Sanin Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci-gaba da Koya don Ka Ƙara Sanin Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENE NE SANIN JEHOBAH YAKE NUFI?
  • DALILIN DA YA SA ZAI DACE MU CI-GABA DA ƘARA SANIN JEHOBAH
  • TA YAYA ZA MU ƘARA SANIN JEHOBAH?
  • BA ZA MU DAINA KOYA GAME DA JEHOBAH BA
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • “Ku Zaɓi Wanda Za Ku Bauta Masa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Yuli pp. 14-19

21-27 GA SATUMBA, 2026

WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko

Ka Ci-gaba da Koya don Ka Ƙara Sanin Jehobah

“Ka san Allahn kakanka, . . . Ka yi masa hidima da dukan zuciyarka.”—1 TAR. 28:9.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da sanin Jehobah yake nufi, da dalilin da ya sa zai dace mu yi niyyar ƙara sanin sa, da kuma yadda za mu yi hakan.

1. Yaya muke ji saꞌad da muka yi tunani game da ilimin Jehobah, da hikimarsa da kuma abubuwa masu ban alꞌajibi da yawa da ya yi?

JEHOBAH ya san kome da kome, ya fi kowa hikima, kuma ya yi abubuwa da yawa masu ban alꞌajibi. Hakika, yin tunani a kan Mahaliccinmu yana sa mu yi mamaki sosai. Muna ji kamar yadda manzo Bulus ya ji saꞌad da ya rubuta cewa: “Albarkun Allah, da hikimarsa, da kuma iliminsa ba su da iyaka. Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike, hanyoyinsa sun wuce gaban ganewa.”—Rom. 11:​33, 34.

2. Mene ne ya nuna cewa za mu iya sanin Jehobah?

2 Gaskiyar ita ce, ba za mu iya sanin kome da kome game da Jehobah ba, amma za mu iya sanin wane irin Allah ne shi. Sarki Dauda ya gaya wa ɗansa Sulemanu cewa: “Ka san Allahn kakanka. Dole ne ka yi masa hidima da dukan zuciyarka . . . Idan ka neme shi, zai sa ka same shi.” (1 Tar. 28:9) Kuma shekaru da yawa bayan haka, manzo Yohanna ya gaya wa ꞌyanꞌuwa maza da mata cewa za su iya ‘sanin Allah wanda yake na gaskiya.’ (1 Yoh. 5:20) Yesu ya ce zai taimaka wa mutane su “san Uban sosai.”—Mat. 11:27.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Dukanmu da muke bauta wa Jehobah mun riga mun koya abubuwan da yawa game da shi. Har ila, akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya game da Jehobah. (Yoh. 17:3) Alal misali, za mu iya koya game da abubuwan da suke sa shi farin ciki, da kuma yadda za mu ƙara dogara gare shi. Za mu tattauna tambayoyi gudu uku da za su taimaka mana mu ƙara sanin Jehobah ko da mun daɗe muna bauta masa: Na ɗaya: Mene ne sanin Jehobah yake nufi? Na biyu: Me ya sa muke bukata mu ci-gaba da ƙara sanin sa. Na uku: Ta yaya za mu ƙara sanin sa?

MENE NE SANIN JEHOBAH YAKE NUFI?

4. Mene ne sanin Jehobah ya ƙunsa?

4 Za mu iya gane abin da sanin Jehobah ya ƙunsa ta wajen yin laꞌakari da abin da Jehobah ya gaya wa Yahudawan da za su dawo daga zaman bauta a Babila. Jehobah ya yi musu alkawari cewa: “Zan ba su zuciyar da za ta san ni, su sani ni ne Yahweh.” (Irm. 24:7) Babu shakka, Yahudawan da suka dawo daga Babila sun riga sun san abubuwa da yawa game da Jehobah, amma suna bukatar su yi iya ƙoƙarinsu don su kusaci Jehobah. Wani masani ya ce: “Akwai bambanci tsakanin sanin Allah da kuma sanin Allah sosai har mutum ya zama amininsa. Za mu iya kwatanta shi da bambancin da ke tsakanin karanta game da soyayya da kuma yin soyayya.” Sanin cewa Jehobah yana da suna kuma cewa shi Allah ne kawai bai isa ba, wajibi ne mu san halayensa masu kyau.

5. Mene ne muka koya daga Sarkin Yosiya game da abin da ake nufi da sanin Jehobah?

5 Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, hakan zai sa mu san abin da yake so da abin da ba ya so. Ala misali, bari mu yi laꞌakari da Sarki Yosiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘A shekara takwas na mulkinsa, a lokacin da yana yaro, Yosiya ya fara neman Allahn kakansa Dawuda.’ (2 Tar. 34:3) Yosiya ya yi fiye da karanta Kalmar Allah. Ya yi amfani da abin da ya koya. Shi ya sa Jehobah ya gaya wa annabi Irmiya cewa, Yosiya ya “yi gaskiya, ya aikata adalci,” wato ya taimaka wa matalauta da kuma waɗanda ba mai taimakon su. Sai Jehobah ya ƙara da cewa: “Ba wannan shi ne abin da ake nufi da sanina ba?”—Irm. 22:​15, 16.

6. Idan muka ƙara sanin Jehobah, mene ne hakan zai sa mu yi? (Zabura 9:10)

6 Karanta Zabura 9:10. Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, hakan zai sa mu ƙara dogara gare shi. Abin da ya faru da manzo Bulus ke nan. A karo na ƙarshe da aka ƙulle shi a kurkuku, kuma kafin a kashe shi, ya rubuta cewa: “Ba na jin kunya domin na san ga wane ne na ba da gaskiya.” (2 Tim. 1:12) Abubuwan da Bulus ya koya game da Jehobah, da kuma yadda Jehobah ya yi ta taimaka masa a rayuwa ne suka sa ya ƙara dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa. Bulus yana da tabbaci cewa Jehobah ba zai manta da shi da kuma ayyukan da ya yi a hidimarsa ba, kuma Jehobah zai tā da shi.

DALILIN DA YA SA ZAI DACE MU CI-GABA DA ƘARA SANIN JEHOBAH

7. Mene ne zai iya faruwa bayan mun daɗe muna bauta wa Jehobah?

7 Bayan mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, zai iya yi mana wuya mu yi ƙoƙarin sanin sa kamar yadda muka yi a lokacin da muka soma koya game da shi. Me ya sa? Yawancin lokuta idan muna karanta Littafi Mai Tsarki a gida ko a taro, mukan mai da hankali a kan yadda abin da muka karanta zai amfane mu, da kuma yadda za mu taimaka ma wasu da abin da muka koya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu yi hakan. (2 Tim. 3:​16, 17) Amma ban da haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abubuwa da yawa game da Jehobah. (Zab. 25:​8-10) Don haka, ba zai dace mu mai da hankali a kan yadda saƙon Littafi Mai Tsarki zai amfane mu da kuma wasu kawai ba, har mu manta mu tambayi kanmu cewa, ‘Mene ne abin da na karanta ya koya mini game da Jehobah?’a

8. Idan muka ƙara sanin Jehobah, mene ne zai faru da dangantakarmu da shi? (Zabura 73:​24-28)

8 Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, dangantakar mu da shi za ta ƙara yin ƙarfi. Alal misali, yaya kake ji game da Jehobah bayan ka karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, ko bayan ka kalli shirin tashar JW, ko kuma bayan ka halarci wani taron daꞌira ko na yanki? Babu shakka hakan yana sa mu ƙara kusantar Ubanmu na sama. Me ya sa? Domin mun ƙara koyan wani abu game da shi, kuma abubuwan da muka koya suna sa mu yabe shi kuma mu gode masa. Za mu ji kamar wani marubucin zabura da ya yi tunani a kan yadda Jehobah yake kula da shi, sai ya ce: “Allah shi ne ƙarfin zuciyata, abin da nake da shi har abada.” (Karanta Zabura 73:​24-28.) A duk lokacin da muka yi ƙoƙarin ƙara sanin Jehobah, hakan zai sa mu ƙara gode masa don shi aboki ne na ƙwarai.

9. Idan muna “tuna da” Jehobah, mene ne hakan zai taimaka mana mu yi? Ka ba da misali.

9 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu riƙa “tuna da” Jehobah. (K. Mag. 3:​5, 6, Mai Makamantu Ayoyi.) Hakan yana nufin cewa za mu yi tunani a kan abin da muka koya game da shi, da yadda yake ji don abubuwan da muke yi. Yin hakan zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Alal misali, ꞌyanꞌuwa da yawa suna sa hoton matansu ko mazajensu a wayarsu. Hakan yana sa su riƙa tuna da matansu ko mazansu, kuma su riƙa yin abin da zai faranta musu rai, maimakon su yi abin da zai ɓata musu rai. Haka mu ma, idan muna yawan tunani game da Jehobah, zai yi mana sauƙi mu yi abubuwan da za su faranta masa rai.—Zab. 19:​13, 14.

10. Yayin da muke ƙara sanin Jehobah, mene ne hakan zai taimaka mana mu iya yi?

10 Jehobah ya halicce mu a kamaninsa, shi ya sa muna iya yin koyi da halayensa. (Far. 1:26) Yayin da muke ƙara sanin halayen Jehobah, za mu ƙara sanin hanyoyi da za mu yi koyi da shi. Abin da Farisiyawa suka kasa koya ke nan. Ko da yake sun san Dokar sosai, amma Yesu ya ce sun yi “watsi da abubuwan da suka fi muhimmanci a cikin Doka, wato adalci da jinƙai da kuma aminci.” (Mat. 23:23) Ba ma so mu zama kamar shugabannin addinan nan. A maimakon haka, muna so mu yi tunani sosai a kan abin da doka da kuma ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suke koya mana game da Jehobah. Yin hakan zai sa mu iya yin koyi da shi.—1 Yoh. 4:​8, 11.

TA YAYA ZA MU ƘARA SANIN JEHOBAH?

11. Ta yaya ka soma koya game da Jehobah?

11 Wane ne ya soma koya maka game da Jehobah? Wataƙila iyayenka ne. Babu shakka sun gaya maka labaran Littafi Mai Tsarki, ko kuma sun koya maka game da abubuwan da Jehobah ya yi da suka nuna halayensa. Ko kuma wani Mashaidin Jehobah ne ya koya maka gaskiya. Wataƙila wanda ya yi nazari da kai ya yi amfani da littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! wajen taimaka maka ka yi tunani mai zurfi a kan labaran Littafi Mai Tsarki, da kuma abubuwan da Jehobah ya yi da suka koya maka game da halayensa masu kyau.b (Neh. 8:8; A. M. 14:17) Yanzu, bari mu tattauna yadda za mu ci-gaba da koya game da Jehobah.

12-13. Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki, mene ne za mu iya koya game da Jehobah? Ka ba da misali. (Irmiya 39:​15-18) (Ka kuma duba shafin farko.)

12 Da farko, za mu iya koya game da Jehobah ta wurin karanta da kuma yin nazarin Kalmarsa. Akwai wurare a cikin Littafi Mai Tsarki da aka ambata halayen Jehobah kai tsaye. (Fit. 34:​6, 7) Amma a yawanci wurare, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da mutane da kuma shawarwarin da suka yanke. Idan ka karanta labaran mutanen nan, ka yi tunani a kan abin da labarin zai iya koya maka game da Jehobah.

13 Ga wani misali. A ce ka karanta Irmiya 38:​6-13, a wurin ka karanta cewa wani mutumin Itiyofiya mai suna Ebedmelek ya ceci annabi Irmiya. Babu shakka zai yi maka sauƙi ka ga cewa kana bukatar ka zama mai taimaka wa mutane, mai nuna ƙauna da ƙarfin zuciya kamar yadda Ebedmelek ya yi. Shin, ka kuma lura da halayen Jehobah da labarin nan ya nuna? (Karanta Irmiya 39:​15-18.) Alal misali, mene ne a labarin nan ya nuna cewa Jehobah mai yin godiya ne, da yin adalci, kuma ba ya nuna bambanci? Mene ne kuma za ka iya koya game da Jehobah a labarin nan? A duk lokacin da kake karanta Kalmar Allah, ka nemi abin da za ka iya koya game da halayen Jehobah, sai ka gode da kuma yaba masa don halayensa.

Ebedmelek da wasu mazaje sun yi amfani da igiya suna cire Irmiya daga rijiya. A bayansu, akwai wasu mutane da suke riƙe da makamai suna gadi.

Ebedmelek ya nuna ƙarfin zuciya wajen ceci Irmiya daga rijiya mai taɓo (Ka duba sakin layi na 12-13)


14. Me ya sa zai dace mu yi tunani mai zurfi a kan abubuwan da Jehobah ya halitta?

14 Na biyu, za mu iya koya game da Jehobah ta wurin yin tunani mai zurfi a kan halittunsa. (Zab. 145:​9, 10) Gaskiyar ita ce, kallon halittun Jehobah kawai bai isa ba. Me ya sa? Wasu suna yin shekaru da yawa wajen yin bincike a kan wata dabba ko kuma wani tsiro. Duk da haka, ba su san cewa akwai wanda ya halicci waɗannan abubuwan ba, balle ma su san halayensa masu kyau. Manzo Bulus ya rubuta game da Allah cewa “ana iya sanin halayensa da ba a gani, domin ana iya gane halayen ta wurin abubuwan da ya yi.” (Rom. 1:20) A wani juyi, an fassara ayar nan cewa za mu iya gane halayen Allah domin “abubuwa ne da ido yake gani.” Saboda haka, wajibi ne mu riƙa yin tunani mai zurfi a kan halittun Jehobah, da kuma abubuwan da suke koya mana game da shi.

15. Mene ne Patrick ya yi don ya ƙara sanin Jehobah da kyau, kuma ta yaya kai ma za ka yi hakan? (Ka kuma duba hoton.)

15 Da yawa daga cikinmu muna rayuwa ne a birane inda babu shuke-shuke da dabbobi da yawa. Idan kana rayuwa a irin wannan wurin, zai yiwu ka koya game da Jehobah daga abubuwan da ya halitta? Ka yi laꞌakari da misalin ɗanꞌuwa Patrick wanda yake zama a birnin Brazzaville na Jamhuriyar Kwango. Ya ce: “A kowace rana, ina yin iya ƙoƙarina don in lura da wani abu da Jehobah ya halitta. Nakan lura da yadda kwari da ƙananan tsuntsaye suke neman abinci ko kuma wurin da za su zauna. Na taɓa lura da yadda wasu tsuntsaye suke gyara gidansu. Sun nemi ciyayi masu laushi sun yi gidan domin yaransu.” Amma Patrick bai tsaya a nan ba, ya yi tunani mai zurfi game da Mahaliccinsu. Ya ce: “Na koyi cewa Jehobah yana lura da halittunsa, har ma da waɗanda suka fi ƙanƙanta. Wannan ya tabbatar mini da cewa yana lura da ni kuma ba zai fasa tanada mini abubuwan da nake bukata ba.”

Wata ꞌyarꞌuwa a gidanta da ke wani birni, tana zuba wa furanni da ta shuka a baranda ruwa, kuma tana murmushi yayin da take kallon wani tsuntsu da ke cin wani abu a furannin.

Ka ƙara sanin Jehobah ta wurin yin tunani mai zurfi a kan halittunsa (Ka duba sakin layi na 15)


16. Mene ne ya taimaka wa Maryamu, mamar Yesu ta ƙara sanin Jehobah, kuma ta yaya za mu yi koyi da ita? (Ka kuma duba hoton.)

16 Hanya ta uku da za mu iya ƙara sanin Jehobah shi ne yin tunani a kan abubuwan da ya yi mana. Abin da Maryamu mahaifiyar Yesu ta yi ke nan. Ta riga ta san Jehobah sosai kuma ta ‘sami alheri a gabansa.’ (Luk. 1:30) Amma sai Jehobah ya ba ta wani aiki mai muhimmanci, wato za ta haifi Ɗansa. Jehobah ya yi amfani da malaꞌika Jibraꞌilu da danginta Alisabatu don ya tabbatar mata da cewa ya yarda da ita kuma zai taimaka mata. Ta yi tunani mai zurfi a kan abubuwan da suka gaya mata. Hakan ya sa ta gane cewa Jehobah mai iko ne, yana yi wa dukan mutane alheri, kuma ya damu da mutanen da ba a ɗaukan su da muhimmanci. (Luk. 1:​46-55) Maryamu ta gode ma Jehobah don yadda ya taimaka mata, mu ma muna godiya saꞌad da Jehobah ya taimaka mana “a lokacin bukata.” (Ibran. 4:16) Idan Jehobah ya taimaka maka ta wannan hanyar, ka tambayi kanka cewa: ‘Mene ne hakan ya koya mini game da Jehobah? Waɗanne halayen Jehobah ne na koya daga taimakon da ya yi mini?’

Hotuna: Wani ɗanꞌuwa yana yin tunani a lokacin da Jehobah ya taimaka masa. Na 1. Yana roƙon Jehobah ya taimaka masa don wani aikin da aka ba shi a ikilisiya. Na 2. Ya yi aikin da kyau daga kan dakalin magana.

Ka ƙara sanin Jehobah ta wurin yin tunani mai zurfi a kan abubuwan da ya yi maka (Ka duba sakin layi na 16)c


BA ZA MU DAINA KOYA GAME DA JEHOBAH BA

17-18. Me ya sa za mu iya cewa ba za mu taɓa daina koya game da Jehobah ba?

17 A sabuwar duniya, za mu samu zarafin koyan abubuwa da yawa game da Jehobah fiye da yadda muke yi yanzu. Za a ba mu sababbin littattafai da za su nuna mana abubuwan da Jehobah yake so mu yi. (R. Yar. 20:12) Zai yi mana sauƙi mu lura da abubuwan da Jehobah ya yi. (Isha. 11:​6-9) Za mu kuma ga sabbin abubuwa da za su ƙara koya mana game da Jehobah, kamar yadda za a ta da matattu, da kuma yadda zai taimaka mana mu zama cikakku.

18 Ba za mu taɓa daina koya game da Jehobah ba. Ya san abubuwa da yawa sosai fiye da mu. Littafi Mai Tsarki ya ce “ganewarsa ta wuce gaban misali.” (Zab. 90:2; 147:5) Ba za mu iya “sanin cikakken abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe ba.” (M. Wa. 3:11) Saboda haka, ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, bari mu ci-gaba da yin amfani da hanyoyi da dama wajen ƙara koya game da Ubanmu mai ƙauna.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne sanin Jehobah yake nufi?

  • Me ya sa zai dace mu ci-gaba da ƙara sanin Jehobah?

  • Ta yaya za mu ƙara sanin Jehobah?

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

a Ka duba tambaya ta 20 na ƙasidar nan Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah.

b Ka duba darasi na 07 batu na 5-7 a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!

c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗanꞌuwa da yake fama da damuwa yana yin tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka masa ya yi aikin da aka ba shi a taron tsakiyar mako.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba