Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Yuli pp. 8-13
  • Za Ka Iya Samun Ƙarfafa Daga Littafin Ishaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Samun Ƙarfafa Daga Littafin Ishaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • IDAN YANAYINMU YA CANJA BA ZATO BA TSAMMANI
  • IDAN MUNA YAWAN DAMUWA SABODA KUSKUREN DA MUKA YI A DĀ
  • IDAN MUNA BAƘIN CIKI DOMIN WANI NAMU YA RASU.
  • Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ba Za Mu Taɓa Zama Mu Kaɗai Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Ya Gafarta Maka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Yuli pp. 8-13

14-20 GA SATUMBA, 2026

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

Za Ka Iya Samun Ƙarfafa Daga Littafin Ishaya

“In ji Yahweh, . . . ‘Yadda mama take taꞌazantar da yaronta, haka zan taꞌazantar da ku.’”—ISHA. 66:​12, 13.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda karanta da kuma yin tunani a kan littafin Ishaya zai ƙarfafa mu.

1-2. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana saꞌad da muke baƙin ciki?

KA Yi tunanin wani yaro da yake kuka, mai yiwuwa domin shi da iyayensa za su ƙaura zuwa wani gida kuma zai rabu da abokansa. Ko kuma yana kuka ne domin wani kuskuren da ya yi. Idan mahaifiyarsa ta ga hakan, mene za ta yi? Babu shakka za ta rungumi ɗanta, ta saurare shi, kuma ta gaya masa cewa tana ƙaunar sa.

2 A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya ce yana kama da uwa da take ƙaunar ɗanta kuma take ƙarfafa shi. Ya ce: “Yadda mama take taꞌazantar da yaronta, haka zan taꞌazantar da ku.” (Isha. 66:13) Jehobah yana ƙaunar mu fiye da yadda iyaye suke ƙaunar yaransu. (Isha. 49:15) Ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki, Jehobah yana ƙarfafa da kuma taꞌazantar da mu saꞌad da muke baƙin ciki ko kuma muna cikin damuwa.—Rom. 15:4.

3. Mene ne za mu tattauna a talifin nan?

3 Littafin Ishaya yana ɗauke da abubuwa da yawa da Jehobah ya gaya mana da suke ƙarfafa mu. (Isha. 40:1) Jehobah ya sa annabi Ishaya ya rubuta littafin don ya ƙarfafa mutanensa da suke Yahuda saboda matsalolin da suke fuskanta a lokacin. Mu ma muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe” da ake shan “wahala sosai.” (2 Tim. 3:1) Bari mu tattauna wasu ayoyi daga littafin Ishaya da za su ƙarfafa mu idan (1) yanayinmu ya canja ba zato ba tsammani, (2) muna yawan damuwa saboda kuskuren da muka yi a dā, ko kuma (3) muna baƙin ciki domin wani namu ya rasu.

IDAN YANAYINMU YA CANJA BA ZATO BA TSAMMANI

4. Idan yanayinmu ya canja ba tsammani, ta yaya hakan zai iya shafan mu?

4 Yanayin rayuwarmu zai iya canjawa ba zato ba tsammani. (M. Wa. 9:11; 1 Kor. 7:31) Alal misali, za mu iya soma rashin lafiya ko rashin kuɗi, ko a soma tashin hankali a ƙasarmu, ko kuma a canja hidimar da muke yi a ƙungiyar Jehobah. Idan abubuwan nan suka faru, za su iya sa mu ji tsoro ko mu soma damuwa. Ƙari ga haka, za su iya sa mu yi tambayar nan cewa: ‘Me zan yi yanzu?’ Akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Joseph wanda ya yi shekara 17 yana hidima a Bethel. Sai aka ce ya koma gida ya yi hidimar majagaba. Ya ce: “Canjin bai yi mini sauƙi ba sam domin na daɗe ina hidima a Bethel. Ban san me zan yi ko kuma abin da zai faru da ni ba.” Wane ƙarfafa ne Jehobah ya tanada mana a littafin Ishaya da zai taimaka mana idan yanayinmu ya canja ba tsammani?

5. Wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu a Ishaya 42:16? (Ka kuma duba hoton.)

5 Karanta Ishaya 42:16. Jehobah ya yi alkawari cewa zai ja-goranci waɗanda suna nan kamar makafin da ba su san hanyoyin da suke bi ba, kuma zai mai da duhunsu haske. Kalmar nan “makafi” da furucin nan “a hanyoyin da ba su sani ba” da kuma “wuraren gargada” za su iya kwatanta yadda za mu ji idan yanayinmu ya canja babu tsammani. Za mu ji kamar muna tafiya a cikin daji ne kuma ba ma iya ganin gabanmu. Amma Jehobah yana tabbatar mana da cewa ko da wane irin yanayi ne muka sami kanmu a ciki, zai yi mana ja-goranci kuma ba zai taɓa barin mu ba. Jehobah zai riƙe mana hannu kuma ya ja-gorance mu saꞌad da muke cikin duhu, zai haskaka hanyar da muke bi, kuma zai cire duk wani gargada da ke hanyar. Ta yaya Jehobah yake yin hakan? Yana ba mu shawarwari masu kyau ta wurin Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa. (Zab. 119:105; Isha. 30:21) Yana kuma sa ꞌyanꞌuwanmu su taimaka mana. Ko da ba mu san abin da zai faru da mu ba, za mu iya dogara ga Jehobah ya taimaka mana domin yana ƙaunar mu kuma ya san yadda muke ji.—Isha. 41:10; 1 Bit. 5:​6, 7.

Hotuna: Wani ɗanꞌuwa da matarsa suna ganin cikar alkawarin da Allah ya yi a Ishaya 42:​16, da ta ce: ʻA hanyoyin da ba ku sani ba, zan bi da ku.’ Na 1. Maꞌauratan suna shirin ƙaura. Na 2. Wani iyali a sabuwar ikilisiyarsu suna marabtarsu.

Ko da yanayinka ya canja ba zato, Jehobah ba zai taɓa barin ka ba (Ka duba sakin layi na 5)b


6. Idan yanayinmu ya canja babu zato, wane abu ne muke da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana?

6 Ɗanꞌuwa Joseph da aka ambata ɗazu ya bayyana yadda Jehobah ya taimaka ma shi da matarsa bayan da suka bar Bethel. Ya ce: “Bayan mun bar Bethel, mun ga yadda Jehobah ya taimaka mana ta wurin ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Ya tanada mana abubuwan da muke bukata, ya ƙarfafa mu a daidai lokaci, kuma ya ci-gaba da yin hakan.” Idan yanayinka ya canja babu tsammani, kai ma za ka iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ƙarfafa ka, kuma ya yi maka ja-goranci ko da yanayin yana da wuya sosai. (Isha. 54:10; 58:11) Joseph ya sami ƙarfafa daga ɗaya daga cikin waƙoƙin JW namu da ta tabbatar mana da cewa komen yanayin da muka sami kanmu a ciki, Jehobah zai kasance tare da mu a kullum.a

IDAN MUNA YAWAN DAMUWA SABODA KUSKUREN DA MUKA YI A DĀ

7. Mene ne zai iya yi ma waɗanda suka yi zunubi a da wuya su yi?

7 Idan mun gaya wa dattawa zunubi mai tsanani da muka yi, za su taimaka mana domin suna ƙaunar mu. Bayan haka, za mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu sake yin kuskuren. (K. Mag. 28:13; Yak. 5:​14-16; 1 Yoh. 1:9) Duk da haka, bayan da dattawa sun taimaka mana, zuciyarmu za ta iya ci-gaba da damunmu. Za mu iya yin shakka ko Jehobah ya gafarta mana da gaske. (2 Kor. 2:7) Me ya sa? Domin yana da wuya mu mance da kurakuren da muka yi a dā. Sarki Dauda ya rubuta cewa: “Jikina ya yi ta ramewa saboda zunubaina. Na gaji kakaf, an kuma tattake ni ƙwarai.” (Zab. 38:​3, 8) Idan haka ne kake ji don kuskuren da yi a dā, littafin Ishaya zai iya ƙarfafa ka.

8-9. Mene ne Ishaya 1:18 ta nuna game da yadda Jehobah yake gafarta mana zunubanmu?

8 Karanta Ishaya 1:18. Jehobah ya yi amfani da wani kwatanci don ya nuna mana yadda yake gafarta mana zunubanmu. Ya ce ko da mun yi “ja wur” da zunubi, zai wanke mu mu zama “fari fat kamar auduga.” Jehobah yana ba mu tabbaci cewa idan ya gafarta mana, ba zai sake tunawa da zunubin da muka yi ba.

9 Bari mu yi laꞌakari da misalin Sarki Dauda, duk da cewa ya yi zina da kisan kai, Jehobah ya gafarta masa kuma ya kira shi mutum mai aminci. (2 Sam. 11:​3, 4, 14, 15; 12:13; 1 Sar. 9:​4, 5) Jehobah ya tuna da yadda Dauda ya riƙe amincinsa ba zunuban da ya yi ba. Hakazalika, idan muka tuba da gaske Jehobah zai gafarta mana kuma zai taimaka mana mu yi farin ciki. Wane tabbaci ne kuma za mu iya samu a littafin Ishaya idan muna yawan damuwa don kuskuren da muka yi a dā?

10. Wane abin ban ƙarfafa ne Jehobah ya ce zai yi mana a Ishaya 38:17?

10 Karanta Ishaya 38:17. Ayar ta ce: “Ka kawar da dukan zunubaina daga gabanka.” Hakan yana nufin cewa Jehobah yakan share zunuban wanda ya tuba da gaske. Ba zai sake tunawa da su ba. Wani kamus na littafi Mai Tsarki ya bayana ayar nan cewa: “Ka mai da zunubaina kamar ba su taɓa faruwa ba.” Wato idan Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, yana ganinmu kamar ba mu taɓa yin zunubin ba. Da zarar ya gafarta mana, ba zai sake hukunta mu don kurakuren da muka yi a dā ba, domin ba ya tunawa da su kuma. Ya yi alkawari cewa: “Ba zan taɓa tuna da laifofinku kuma ba.” (Isha. 43:25) Wannan yana sa mu farin ciki. Idan Jehobah ya manta da kuskurenmu, ba zai dace mu ci-gaba da tunawa da kuma damuwa saboda su ba.

Kada mu bar kurakuren da muka yi a dā su sa mu baƙin ciki

11. Ko da mene ne muka yi a dā, mene ne Jehobah yake mai da hankali a kai? (Ka kuma duba hoton.)

11 A duk lokacin da muka soma damuwa don kurakuren da muka a yi a dā, zai dace mu tuna da alkawuran da Jehobah ya yi mana. Idan ya gafarta mana, ba ya sake tunawa da kuskuren. Ba ma zama abin kunya a gabansa saboda kurakuren da muka yi a dā, kuma shi ba kamar ꞌyanꞌadam da suke tunawa da kurakuren da aka yi musu ba. (Isha. 57:16) Abin da ya fi muhimmanci a gun Jehobah shi ne abubuwan da muke yi yanzu, da kuma abubuwan da za mu yi a nan gaba, ba abubuwan da muka yi a dā ba. (Isha. 55:7) Babu shakka, Jehobah yana ƙaunar mu, kuma yana so ya gafarta mana idan muka yi kuskure. Don haka, bari mu ci-gaba da tuna cewa Jehobah yana ƙaunar mu, kuma kada mu bar kurakuren da muka yi a dā su sa mu baƙin ciki, ko kuma su sa mu daina bauta wa Jehobah har ya hana mu samun rai na har abada a nan gaba.

Hotuna: Wani ɗanꞌuwa yana amfana daga tabbacin da ke Ishaya 38:​17, da ta ce: “Ka kawar da dukan zunubaina daga gabanka.” Na 1. Wani ɗanꞌuwa yana baƙin ciki don kuskuren da ya yi a dā. Na 2. Daga baya yana farin ciki yayin da yake yin kalami a Makarantar Hidima ta Majagaba.

Jehobah ba ya mai da hankali ga kurakuren da muka yi a dā (Ka duba sakin layi na 11)c


IDAN MUNA BAƘIN CIKI DOMIN WANI NAMU YA RASU.

12. Yaya za mu iya ji idan wani namu ya rasu?

12 Idan wani namu ya rasu, hakan zai iya sa mu yi baƙin ciki sosai na dogon lokaci. A wasu lokuta, za mu iya soma tunanin dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wani namu ya mutu. Wani ɗanꞌuwa mai suna Michael da ya rasa iyayensa a gobarar wuta, ya ce: “Na yi baƙin ciki sosai ba kaɗan ba, kuma na yi fushi da Jehobah da ya ƙyale su su mutu. Ko da yake na san cewa ba shi ne ya kashe su ba, bai hana hakan faruwa ba.” Idan haka ne kake ji, wane taꞌaziyya da kuma bege ne Jehobah yake ba mu?

13. Wane alkawari ne Jehobah ya yi mana a Ishaya 25:8?

13 Karanta Ishaya 25:8. Jehobah ya yi alkawari cewa “zai halaka mutuwa har abada.” Ka yi tunani yadda rayuwa za ta kasance idan babu mutuwa! Ba za ka sake yin baƙin ciki ba don wani naka da ya mutu. (Isha. 35:10) Ba za ka sake ganin kabari inda aka binne wani naka da ya rasu ba. A maimako, za ka kasance tare da ƙaunatattunka cikin ƙoshin lafiya har abada. Alkawarin nan ba mafarki ne kawai ba, hakan zai faru domin Jehobah ne ya yi alkawarin, kuma shi kaɗai zai iya cikawa.—R. Yar. 21:​4, 5.

14. Yaya kake ji a duk lokacin da ka yi tunani game da lokacin da za a tā da matattu? (Ishaya 26:19) (Ka kuma duba hoton.)

14 Karanta Ishaya 26:19. Ba kawai Jehobah zai kawar da mutuwa ba, zai tā da ƙaunatattunmu da suka mutu. Wani juyin Littafi Mai Tsarki ya fassara ayar haka: “Gawayena za su tashi.” Wannan yana nufin cewa Jehobah yana ɗaukan su kamar nasa. Yana sane da su kuma ba zai manta da su ba. A daidai lokacin da ya shirya, Jehobah zai tā da su. Kamar yadda ruwa take sa shukin da ya bushe ya sake tsirowa, haka ma Jehobah zai tā da ƙaunatattunmu da suka mutu. Za mu yi farin cikin marabtar su a lokacin!—Ka duba Mar. 5:42.

Hotuna: Wata ꞌyarꞌuwa tana amfana daga alkawarin da Allah ya yi a Ishaya 26:​19, da ta ce: “Mutanenku da suka mutu za su rayu.” Na 1. Wata mahaifiya da take makoki ta zauna ita kaɗai a daƙin ꞌyarta da ta rasu, kuma ta riƙe hotonta. 2. Ta rungumi ꞌyar tana farin ciki bayan an tā da ꞌyar daga mutuwa.

Muna da tabbaci cewa za mu sake ganin ƙaunatattunmu da suka mutu (Ka duba sakin layi na 14)


15. Ta yaya begen tashin matattu yake taimaka mana idan wani namu ya rasu?

15 Ko da mun yi imani cewa Jehobah zai tā da matattu, za mu yi baƙin ciki sosai idan wani namu ya rasu. Amma mun san cewa Jehobah bai manta da su ba, kuma sanin hakan na ƙarfafa mu. Abin da ya taimaka wa Michael da aka ambata ɗazu ke nan, ya ce: “Littafin Ishaya 26:19 ya taimaka mini in fahimci cewa iyayena suna da muhimmanci a gaban Jehobah. Ba zai manta da su ba, kuma zai tā da su idan lokaci ya kai. Hakan na ƙarfafa ni sosai.” Mu ma, zai dace mu riƙa mai da hankali ga lokacin da za mu sake haɗuwa da ƙaunatattunmu da suka mutu.

16. Wane nassi ne yake ƙarfafa ka idan kana cikin wani yanayi mai wuya?

16 Mun tattauna wasu ayoyin littafin Ishaya da za su iya taꞌazantar da kuma ƙarfafa mu idan yanayinmu ya canja ba zato ba tsammani, idan muna yawan damuwa saboda kurakuren da muka yi a dā, da kuma idan muna baƙin ciki don wani namu ya rasu. Muna farin ciki sosai domin Jehobah yana amfani da Kalmarsa don ya ƙarfafa mu! (Zab. 94:19) Shin, kana da wani nassin da yake ƙarfafa ka idan kana cikin wani yanayi mai wuya? Idan zai yiwu ka haddace shi, ka rubuta shi a wani wuri, ko kuma ka manna shi a inda za ka riƙa ganin sa kullum. Fatanmu shi ne, Kalmar Allah da ka haddace ko kuma ka rubuta zai ci-gaba da ƙarfafa ka.

TA YAYA AYOYIN NAN SUKE ƘARFAFA KA . . .

  • Ishaya 42:16?

  • Ishaya 1:18; 38:17?

  • Ishaya 25:8; 26:19?

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

a Jigon waƙar JW ɗin shi ne “Ba Zan Ji Tsoro Ba.”

b BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ꞌyanꞌuwa suna marabtar wani ɗanꞌuwa da matarsa da suka bar Bethel da suka ƙaura zuwa ikilisiyarsu.

c BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa ya manta da kurakuren da ya yi a dā yana jin daɗin halartan Makarantar Hidima ta Majagaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba