TALIFIN NAZARI NA 34
WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Ya Gafarta Maka
“Ka kuwa gafarta mini laifofina.”—ZAB. 32:5.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa idan muka tuba da gaske, Jehobah zai gafarta mana, da kuma dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu gaskata da hakan.
1-2. Idan mun san cewa Jehobah ya riga ya gafarta mana, yaya hakan zai sa mu ji? (Ka kuma duba hoton.)
ZUNUBAN da Sarki Dauda ya yi, sun sa shi baƙin ciki ba kaɗan ba. (Zab. 40:12; 51:3; rubutu na sama) Amma ya tuba kuma Jehobah ya gafarta masa. (2 Sam. 12:13) Hakan ya sa shi farin ciki sosai, da yake ya san cewa Jehobah ya gafarta masa.—Zab. 32:1.
2 Kamar Dauda mu ma za mu yi farin ciki idan muka san cewa Jehobah ya nuna mana jinƙai kuma ya gafarta mana zunubanmu. Ko da mun yi zunubi mai tsanani, abin farin ciki ne sanin cewa Jehobah zai gafarta mana idan muka tuba da gaske, muka roƙe shi gafara, muka gaya wa dattawa, kuma muka yi iya ƙoƙarinmu kada mu sake yin zunubin! (K. Mag. 28:13; A. M. 26:20; 1 Yoh. 1:9) Ƙari ga haka, muna farin ciki cewa idan Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, ba zai sake kama mu da laifi ko ya huƙunta mu a kan su ba!—Ezek. 33:16.
Sarki Dauda ya rera waƙoƙi da yawa da suka bayyana yadda Jehobah yake gafartawa (Ka duba sakin layi na 1-2)
3-4. Mene ne ya dame wata ꞌyarꞌuwa bayan ta yi baftisma, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?
3 A wasu lokuta, za mu iya gani kamar Jehobah bai gafarta mana ba. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jennifer ke nan. Iyayenta Shaidu ne kuma sun koya mata yadda za ta ƙaunaci Jehobah. Amma da ta yi girma, ta soma yin abubuwa marasa kyau a ɓoye. Bayan wasu shekaru, ta daina abin da take yi, ta yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ta yi baftisma. Ta ce: “A dā ina yawan yin lalata, ina buguwa da giya, ina saurin fushi, kuma neman kuɗi ne ya fi muhimmanci a gare ni. Na san cewa Littafi Mai Tsarki ya ce fansar Yesu zai sa Jehobah ya gafarta mana. Amma duk da cewa na tuba kuma na roƙi Jehobah ya gafarta mini, ban gaskata cewa ya yi hakan ba.”
4 Shin, kai ma a wasu lokuta kana ganin Jehobah bai gafarta maka ba, don wasu zunuban da ka yi a dā? Idan haka ne, ka tuna abin da Dauda ya faɗa game da Jehobah cewa shi mai jinƙai ne. Dauda ya kasance da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta masa, kuma Jehobah yana so kai ma ka yi hakan. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta mana da kuma abin da zai taimaka mana mu yi hakan.
ME YA SA MUKE BUKATAR MU KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH YA GAFARTA MANA?
5. Mene ne Shaiɗan yake so mu gaskata da shi? Ka ba da misali.
5 Idan muka gaskata cewa Jehobah ya gafarta mana, hakan zai sa ba za mu faɗa a cikin tarkon Shaiɗan ba. Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa don ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Don ya cim ma hakan, zai sa mu ga kamar ba za a taɓa gafarta mana zunubanmu ba. Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da mutumin da ke ikilisiyar Korinti wanda aka cire shi daga ikilisiya domin ya yi lalata. (1 Kor. 5:1, 5, 13) Bayan ya tuba, Shaiɗan ya so ꞌyan ikilisiyar su ƙi gafarta masa, kuma kada su marabce shi hannu bibbiyu. Idan ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ba su gafarta masa ba, mutumin zai ga kamar Jehobah ba zai taɓa gafarta masa ba. Zai iya yin “baƙin ciki” sosai har ya daina bauta wa Jehobah. Abin da Shaiɗan yake so ke nan. Haka ma a yau, Shaiɗan zai so mu ga kamar Jehobah ba zai taɓa gafarta mana ba har mu daina bauta wa Jehobah. Amma ba za mu faɗa a tarkonsa ba don “mun san dabarunsa sarai.”—2 Kor. 2:5-11.
6. Me za mu iya yi idan muna gani kamar Jehobah bai gafarta mana ba?
6 Idan muka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta mana, zuciyarmu za ta daina damunmu. Idan muka yi zunubi muna baƙin ciki sosai. (Zab. 38:4) Hakan yana da kyau. Domin idan zuciyarmu ta dame mu, hakan zai sa mu yi ƙoƙarin gyara kuskurenmu, kuma mu yi abin da ya dace. (2 Kor. 7:10, 11) Amma idan zuciyarmu ta ci-gaba da damunmu bayan mun tuba, hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa sosai har mu daina bauta wa Jehobah. Shi ya sa zai dace mu gaskata cewa Jehobah ya gafarta mana gabaki ɗaya, hakan zai sa mu daina baƙin ciki. Za mu sake yin farin ciki, kuma mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da tabbaci cewa zai karɓi bautarmu. Abin da Jehobah yake so mu yi ke nan. (Kol. 1:10, 11; 2 Tim. 1:3) Amma ta yaya za mu tabbatar wa kanmu cewa Jehobah ya gafarta mana?
MENE NE ZAI TAIMAKA MANA MU KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH YA GAFARTA MANA?
7-8. Mene ne Jehobah ya faɗa game da kansa, kuma wane tabbaci ne hakan ya ba mu? (Fitowa 34:6, 7)
7 Ka yi tunani a kan abin da Jehobah ya faɗa game da kansa. Alal misali, ka yi laꞌakari da abin da Jehobah ya gaya wa Musa a Babban Tudun Sinai.a (Karanta Fitowa 34:6, 7.) Ko da yake Jehobah yana da halaye da yawa masu kyau. Ya gaya wa Musa cewa shi “Allah mai jinƙai ne, mai alheri.” Shin, mai irin wannan halin zai ƙi gafarta wa bawansa da ya tuba da gaske? Sam-sam! Jehobah ba zai taɓa yin hakan ba. Hakan zai nuna cewa Jehobah ba mai jinƙai da alheri ba ne.
8 Muna da tabbaci cewa abin da Jehobah ya faɗa game da kansa, gaskiya ne. Domin ba ya ƙarya. (Zab. 31:5) Saboda haka, za mu iya gaskatawa da abin da ya faɗa. Idan yana yi maka wuya ka gaskata cewa Jehobah ya gafarta maka, ka tambayi kanka: ‘Shin na gaskata cewa Jehobah mai jinƙai da alheri ne kuma zai gafarta wa duk wanda ya tuba da gaske?’ Idan ka gaskata da hakan, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta maka.
9. Me ake nufi da cewa an gafarta mana zunubanmu? (Zabura 32:5)
9 Ka yi tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yadda Jehobah yake gafarta mana. Ka yi laꞌakari da abin da Dauda ya faɗa game da yadda Jehobah yake gafartawa. (Karanta Zabura 32:5.) Ya ce: “Ka kuwa gafarta mini laifofina.” A Ibrananci, kalmar nan gafartawa tana nufin “ɗaga” ko kuma “ɗauke.” Saboda haka, saꞌad da Jehobah ya gafarta wa Dauda zunubansa, ya ji kamar Jehobah ya ɗaga masa wani kaya mai nauyi ne kuma ya ɗauka ya tafi da shi. Hankalin Dauda ya kwanta da yake ya san cewa Jehobah ya gafarta masa gabaki ɗaya. (Zab. 32:2-4) Mu ma za mu iya ji kamar yadda Dauda ya ji. Idan muka tuba daga zunubanmu, bai kamata mu bar zuciyarmu ta ci-gaba da damun mu ba domin Jehobah ya riga ya gafarta mana gabaki ɗaya.
10-11. Mene ne ake nufi da cewa Jehobah yana shirye ya gafarta mana? (Zabura 86:5)
10 Karanta Zabura 86:5. Dauda ya ce Jehobah yana “yin gafara” wato, yana shirye ya gafarta mana. Hakan yana nufin cewa Jehobah ba ya saurin fushi idan muka yi kuskure. Kuma yana marmari ya gafarta mana idan muka tuba. Me ya sa Jehobah yake nan haka? Dauda ya ƙara da cewa, kai “mai yawan ƙauna marar canjawa ga dukan masu kira gare ka.” Kamar yadda muka gani a talifin da ya shige, Jehobah ya yi alkawari zai nuna ƙauna marar canjawa ga masu ƙaunar sa kuma ba zai taɓa barin su ba. Saboda haka, idan mun yi zunubi kuma muka tuba, Jehobah zai ci-gaba da nuna mana ƙauna marar canja, kuma ya gafarta mana gabaki ɗaya. (Isha. 55:7) Idan yana maka wuya ka amince cewa Jehobah ya gafarta maka. Ka tambayi kanka: ‘Na gaskata cewa Jehobah na marmarin gafarta wa duk wanda ya tuba da gaske, kuma ya nemi taimakonsa? Idan ka gaskata da hakan, zai dace ka kasance da tabbaci cewa ya gafarta maka kai ma a lokacin da ka roƙe shi gafara.’
11 Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah ya san mu ciki da waje, kuma ya san mu ajizai ne. Sanin hakan yana ƙarfafa mu. (Zab. 139:1, 2) Bari mu ga wani abu kuma da Dauda ya faɗa a littafin Zabura da zai taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa, Jehobah yana so ya gafarta mana.
KADA KA MANTA DA ABIN DA JEHOBAH YAKE TUNAWA
12-13. Bisa ga Zabura 103:14, mene ne Jehobah yake tunawa game da mu, kuma yaya hakan yake sa ya bi da mu?
12 Karanta Zabura 103:14. Dauda ya ce Jehobah yana “tuna cewa mu ƙurar ƙasa ne.” Hakan yana nufin cewa ya san za mu yi kuskure, bari mu ƙara tunani a kan abin da Dauda ya faɗa.
13 Dauda ya ce Jehobah ya san abin da aka yi mu da shi. Shi ne ya halicci Adamu da “ƙurar ƙasa.” Saboda haka, ya san kome da kome game da ꞌyanꞌadam da abubuwan da suke bukata. Alal misali, ya san suna bukatar su ci abinci, su yi barci kuma su yi numfashi. Waɗanda ba ajizai ba ma suna bukatar abubuwan nan. (Far. 2:7) Amma bayan da Adamu da Hauwaꞌu suka yi zunubi, sun zama ajizai. Da yake mu ꞌyaꞌyansu ne mun gāji zunubi, kuma hakan yana sa muna yin abubuwan da ba su dace ba. Jehobah ya san cewa mu ajizai ne. Amma saꞌad da Dauda ya ce yana “tuna” da hakan, abin da yake nufi shi ne, Jehobah ya san za mu yi kuskure kuma yana tausaya mana. A taƙaice, abin da Dauda yake nufi shi ne, Jehobah ya san za mu yi kuskure a wasu lokuta. Idan hakan ya faru, Jehobah zai ji tausayin mu ya gafarta mana idan muka tuba da gaske.—Zab. 78:38, 39.
14. (a) Mene ne kuma Dauda ya faɗa game da yadda Jehobah yake gafarta mana? (Zabura 103:12) (b) Mene ne za mu iya koya daga yadda Jehobah ya gafarta wa Dauda? (Ka duba akwatin nan, “Yadda Jehobah Yake Gafarta da Kuma Manta da Zunubanmu.”)
14 Mene ne kuma zai daɗa tabbatar mana cewa Jehobah ya gafarta mana? (Karanta Zabura 103:12.) Dauda ya ce idan Jehobah ya gafarta mana, Yana sa zunubanmu su yi nisa “kamar yadda gabas take nesa da yamma.” Gabas ce ta fi nisa daga yamma. Idan wani mutum ya nufi gabas, wani kuma ya nufi yamma, ba za su taɓa haɗuwa ba. Hakan yana nufin cewa idan Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, kamar ya ɗauki zunuban ya kai su wuri mai nisa sosai daga inda muke ne. Saboda haka, idan Jehobah ya gafarta mana, babu abin da zai sa ya sake tunawa, ko kuma ya hukunta mu don zunubin.—Ezek. 18:21, 22; A. M. 3:19.
15. Me muke bukata mu yi idan muna ganin kamar Jehobah bai gafarta mana zunuban da muka yi a dā ba?
15 Ta yaya abin da Dauda ya faɗa a Zabura 103 zai taimaka maka idan yana yi maka wuya ka gaskata cewa Jehobah ya gafarta maka? Ka yi tunani a kan abin da Jehobah yake tunawa. Yana tuna cewa kai ajizi ne, kuma Jehobah yana gafarta wa waɗanda suka tuba kamar yadda kai ma ka tuba. Ka kuma tuna cewa Jehobah ba zai sake tuna wa kansa ko ya tuna maka zunuban da ya riga ya gafarta maka ba. Don haka, ba zai taɓa hukunta ka domin su ba. Jehobah ba ya mai da hankali a kan zunuban da muka yi a dā. Ba zai dace mu mu yi hakan ba. (Zab. 130:3) Idan mun gaskata cewa Jehobah ya gafarta mana, za mu daina baƙin ciki kuma mu ci-gaba da bauta masa da farin ciki.
16. Ka ba da misali da ya nuna cewa bai da kyau mu ci-gaba da yin tunani a kan zunuban da Jehobah ya gafarta mana. (Ka kuma duba hoton.)
16 Ga wani misali. Idan mutum yana tuƙa mota, yana ɗan kallon madubi don ya ga abin da ke zuwa a bayansa. Ba zai dace ya kafa ido a madubin yana ta kallon baya ba. Idan ya yi hakan, zai yi hatsari. Amma idan yana so ya yi tuƙi lafiya, dole ne ya riƙa kallon gabansa. Haka ma, ba laifi ba ne mu ɗan yi tunani a kan kurakuren da muka yi a dā ba. Hakan zai iya sa ba za mu sake yin irin kuskuren ba. Amma idan muka ci-gaba da yin tunani a kan zunubin da Jehobah ya riga ya gafarta mana, hakan zai iya sa mu daina farin ciki. Kuma ba za mu iya bauta wa Jehobah yadda yake so ba. A maimakon haka, bari mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da kuma yin tunani game da alkawarin sabuwar duniya da ya yi mana. A lokacin, “ba za a sāke tunawa da abubuwan dā ba.”—Isha. 65:17; K. Mag. 4:25.
Kamar yadda mai tuƙa mota yake bukatar ya riƙa kallon gabansa, maimakon madubin da ke nuna bayansa. Haka mu ma muke bukatar mu mai da hankali ga albarkun da za mu samu a nan gaba, maimakon kurakuren da muka yi a dā (Ka duba sakin layi na 16)
KA CI-GABA DA TABBATAR WA KANKA CEWA JEHOBAH YA GAFARTA MAKA
17. Me ya sa muke bukatar mu ci-gaba da tabbatar wa kanmu cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma ya gafarta mana?
17 Muna bukatar mu ci-gaba da tabbatar wa kanmu cewa Jehobah yana ƙaunar mu, kuma yana shirye ya gafarta mana. (1 Yoh. 3:19) Me ya sa? Domin Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa ya sa mu ga kamar Jehobah ba zai taɓa ƙaunar mu, ko ya gafarta mana zunubanmu ba. Burinsa shi ne ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Kuma da yake ya ga cewa lokacinsa ya rage kaɗan, yana iya ƙoƙarinsa don ya sa mu yi hakan. (R. Yar. 12:12) Dole ne mu yaƙi Shaiɗan, kuma mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci!
18. Me muke bukatar mu yi don mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana gafarta mana?
18 A talifin da ya wuce, mun ga abin da muke bukatar mu yi don mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu. A wannan talifin kuma, mun koyi abin da muke bukatar mu yi don mu tabbatar wa kanmu cewa Jehobah ya gafarta mana. Alal misali, mun ga cewa muna bukatar mu riƙa tuna da abin da Jehobah ya faɗa game da kansa. Kuma mun ga cewa zai dace mu riƙa tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yadda Jehobah yake gafartawa. Mu tuna cewa ya san mu ajizai ne, kuma zai nuna mana jinƙai. Ƙari ga haka, idan ya gafarta mana yakan yi hakan gabaki ɗaya. Saboda haka, za mu iya yin farin ciki domin mun tabbata cewa Jehobah yana nuna mana jinƙai. Kuma kamar Dauda za mu iya cewa, mun gode Jehobah don kana ‘gafarta mana laifofinmu’!—Zab. 32:5.
WAƘA TA 1 Babu Wani Kamar Jehobah
a Ka duba talifin nan, “Ka Kusaci Allah—Saꞌad da Jehobah Ya Kwatanta Kansa” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2009.